Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Birthday

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah, Iyayen ɗaliban makarantarmu suna aiko mana da wasu abubuwan da za a raba wa sauran ɗalibai, wani lokacin ma da malaman, a kan a yi wa ɗalibi ko ɗaliba addu’a na birthday. Don Allaah, menene hukuncin wannan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Bikin tunawa da ranar haihuwa (birthday) da wasu musulmi a yau suke yi wa kansu da ’ya’yansu ba shi daga cikin koyarwar sahihin addininmu na musulunci. Abu ne da aka koyo shi daga waɗanda ba musulmi ba.

Shi musulunci abin da ya koyar da mu shi ne: Ranakun biki guda biyu ne kawai: Babbar Sallah da Ƙaramar Sallah. Ba ruwansa da sauran bukukuwan da mutane suka ƙirƙira, kamar bikin tunawa da ranar haihuwa, bikin tunawa da ranar yancin-kan ƙasa, bikin tunawa da ranar haihuwar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), da bikin cikar shekara da sauransu. (Tamaamul Minnah: 2/49).

Don haka kuma, bayar da taimako ko gudunmawa ga mai yin bikin da ya saɓa wa Musulunci, ta hanyar bayar da kyauta ko aikawa da saƙon gaisuwa ko taya-murna ta waya ko dai makamancin haka, wannan ma bai dace da koyarwar musulunci ba. Haka ma taya su murna ta hanyar yi musu addua duk ba daidai ba ne, domin dokar da Allaah Subhaanahu Wa Taaala ya faɗa kenan cewa:

...وَتَعَاوَنُوا عَلَى الْبِرِّ وَالتَّقْوَىٰ ۖ وَلَا تَعَاوَنُوا عَلَى الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ ۖ إِنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ ٢۝

Kuma ku taimaki juna  kan ayyukan alheri da ƙarin taqawa, kuma kar ku taimaki juna a kan zunubi da ƙetare haddi, kuma ku ji tsoron Allaah; haƙiƙa Allaah Mai Tsananin Uƙuba ne. (Surah Al-Maaidah: 2)

Sannan kuma a hankalce ma, duk mai hankali ya san cewa: Babu dalilin yin murna da farin ciki don kewayowar ranar haihuwa:

Shin wai bawan Allaah da bai tabbatar da cewa dukkan ayyukansa na-gari na shekarar da ta wuce sun samu karɓuwa ne a wurin Allaah Subhaanahu Wa Ta’aala ba …!

Kuma mutumin da bai samu tabbacin cewa dukkan zunuban da ya aikata a cikin shekarar da ta gabata an yafe masa su, an gafarta masa ba …! 

Kuma mutumin da bai ga mala’iku masu fararen fuska ne suka sauko don karɓar ransa ba …!

Wanda bai gama amsa tambayoyin Munkar da Nakeer a cikin Ƙabarinsa ba !

Wanda bai riga ya karɓi takardarsa ta hannun dama a ranar Ƙiyama ba !

Wanda bai ga cewa sikelinsa a ranar Lahira ya yi nauyi da kyawawan ayyuka ba …!

Wanda bai gama haye gadar Siraɗi siriri mai santsi ba …!

Ina yake da lokacin yin murna da farin ciki?!!

Alhali kuma murnar da yake yi Allaah bai sanya masa hakan daga cikin ayyukan da yake so ba!!!

Allaah ya datar da mu ga abin da yake so kuma yake yarda.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments