Ticker

6/recent/ticker-posts

Addu'oin Shiga Sabon Gida

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum mallam Allah ya saka da alkhairi Allah yaji kan mahaifa, mallam tambaya nake da shi ran jumu'a mai zuwan nan idan Allah ya kaimu inshallahu zanyi aure, to gidan da zan zauna sai wasu su daga cikin yan'uwa na suke ta kiraye kirayen naje na Karɓo taimako wai na binne a gidan, Ni kuma naki , shine nakeson mallam ya taimaka abani shawara maiya kamata nayi dangane da shiga sabon gida a tafarkin sunna.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Yadda kayi ɗin nan shine mataki mafi dacewa domin ta irin waɗannan hanyoyin ne sai ajefaka cikin shirka ba tare da ka sani ba.

Ga wasu matakai sahihai ingantattu da  zaka iya bi domin tsarkake gidanka daga Shaiɗanun aljanu da kuma samun tsaro daga kowanne sharri :

1. Ka rika karanta suratul Baqarah duk bayan kwanaki biyu agidanka. Idan baka samu damar karantawa ba, koda a na'urar MP3 PLAYER ka sanya, muryar karatun ta kewaya ko ina acikin gidan.

Yazo acikin hadisi Manzon Allah ya ce "SHAIƊANU BASU ZAMA ADUK GIDAN DA AKE KARANTA SURATUL BAQARAH".

2. Ka nemi ganyen magarya guda bakwai ka dakasu atsakanin duwatsu guda biyu (ma'ana kayi amfani da duwatsu biyu ɗaya bisa ɗaya) sannan ka zuba acikin ruwa mai tsarki, ka tsoma babban yatsanka na hannun dama acikin ruwan, ka kisanto da bokitin dap da bakinka sannan ka karanta Ayatur Ruqyah gaba ɗayansu,  sai kuma Suratul isra'i da suratu Yaseen, Sannan  ka yayyafa ruwan ko ina cikin gidan nan. Har jikin bangon.

To in Shã Allahu komai yawan Aljanun dake gidan zasu fita da izinin Allah. Koda suna bayyana afili ana ganinsu, to in Shã Allahu daga rannan ba za a  sake ganinsu ba.

3. Lubban Zakar  da Mustakha, idan aka samesu ahaɗasu waje guda arika turarawa acikin gidan, in Shã Allahu Shaiɗanu basu zama a inda zasu ji Qamshin waɗannan turaren.

4. Kullum kafin ka kwanta barci ka rika karanta fatiha, ayoyi huɗu na farkon baqara, ayatul kursiyyi da ayoyi biyu na gabanta, sai kuma ayoyi uku na karshen Suratul baqarah. In shã Allahu, Allah zai kiyayeka dakai da gidanka da iyalanka har makobtanka ma daga sharrin ɓarayi ko 'yan fashi ko matsafa da duk wani mai mugun nufi.

5. Duk cikin dare kafin ka kwanta ka rika yin wannan addu'ar  Qafa ɗaya :

أَعُوذُ بكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لَا يُجَاوِزُهُنَّ بَرٌّ ولَا فَاجِرٌ مِنْ شّرِّ مَا خَلقَ، وبَرَأَ وَذَرَأَ، ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ، وَمِنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فِيهَا، وَمِنْ شَرِّ مَا ذَرَأَ فِي الأَرْضِ، وَمِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا، وَمِنْ شَرِّ فِتَنِ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ، وَمِنْ شَرِّ كُلِّ طَارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بْخَيْرٍ يَا رَحْمَنُ

Imamu Ahmad da Ibnus Sunniy ne suka ruwaito  hadisin addu'ar.

In Shã Allahu babu wani mummunan abin da zai sameka daga sharrin ɓarayii ko 'yan fashi ko 'yan daba ko matsafa ko mahassada. Addu'a takobin mumini ce.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/K7RkQRMf2b57l3UENoJ1Or

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments