𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Matafiyi ne ya isa gida daf da Maghriba alhali bai yi la’asar ba, kuma bai tuna ba sai a bayan ya yi Maghriba. To wai La’asar ɗin ce kaɗai zai yi, ko duk da Maghriba?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa
Barakaatuh.
Malamai sun saɓa wa juna game da waɗannan:
(i) Wanda ya manta da wata sallah sai a bayan ya
yi wacce ta ke a a bayanta sannan ya tuna.
(ii) Wanda lokacin sallar yanzu ya yi masa ƙunci,
ta yadda idan ya ce zai yi wacce ta kuɓce masa lokacin ta yanzun ɗin zai fita.
(iii) Wanda ya shiga masallaci kuma ya tarar an
tayar da iqamar sallah alhali shi bai yi wacce ta ke kafin wannan da aka tayar ɗin ba.
Waɗansu
malamai sun zaɓi
cewa, lallai ya gabatar da wacce ta kuɓce masa da farko kafin ya yi ta yanzu, ko da kuwa
lokacin ta yanzun ɗin zai
fita. Idan kuma ya manta ne, to bayan ya yi wacce ta kuɓce masa sai ya sake maimaita ta yanzun ɗin. Suka ce, domin wajibi ne a jeranta
adadin sallolin yini guda.
Waɗansu
malaman kuma sun zaɓi ya
fara yin sallar yanzu ɗin,
sannan daga baya ya kawo wacce ta kuɓce masa. Suka ce, ai asali Allaah bai wajabta wa
musulmi ya maimaita wata sallah a rana guda sau biyu ba.
Wannan maganar ta ƙarshe ce muka fi natsuwa
da ita, domin ba mu ga wani dalili sahihi mai wajabta jerantawar ba. (Tamaamul Minnah:
1/175).
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
Post your comment or ask a question.