Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Rance Kudin Gwamnati Da Ruwa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. A ƙarƙashin shirin Gwamnatin Tarayya na samar da sanaoi ga marasa ƙarfi, bayan ta horar da masu koyon sanaoin, ta buɗe musu wuraren yin sana’o’in, sai kuma ta ba su rancen kuɗi wanda za su biya daga baya, amma tare da ƙarin kashi bakwai a cikin ɗari (7%) na kuɗin. To, mene ne hukuncin wannan ƙarin?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Haramcin bayarwa ko karɓar bashi-da-ruwa abu ne sananne a wurin dukkan masu addini, saboda Ayoyi da Hadisai Sahihai da suka zo a kan haka. Sannan kuma ga maganganun manyan malamai masana a kan batun, tun daga zamanin Sahabbai (Radiyal Laahu Anhum) har zuwa yau.

Amma a lokacin da gwamnatin ƙasa ta fito da wata hanya na bayar da rance da manufar rage wa talakawa raɗaɗin talauci da ƙuncin rayuwar da su ke ciki, ba zai yi kyau musulmi su janye jikinsu ko hannuwansu daga wannan shirin ba, saboda kawai an lulluɓe shi da irin waɗannan sharuɗɗa da ƙaidojin da suka saɓa wa dokokin musulunci. Musamman idan muka fahimci cewa da ma an saka waɗannan ƙaidojin ne kawai domin musulmi su janye jikinsu, su bar wa kafirai da fasiƙai fagen, su ci karensu ba babbaka!

Domin a fili ya ke cewa: Idan musulmi suka ƙi karɓar wannan rancen, to kamar sun ƙara ƙarfafa wa kafirai da fasiƙai ƙarfin tattalin arziƙi ne a kansu. Hakan kuwa bai kamata ba.

Ƙarin ƙarfin tattalin arziƙin fasiƙai da kafirai yana nufin ƙarin yaɗuwar hanyoyin ɓarna da ma sha’a kenan a cikin al’umma, wanda kuma zai shafi kowannenmu a duk inda ya ke. Wannan ma bai dace ba.

Idan musulmi suka ƙi karɓar wannan irin rancen alhali suna cikin tsananin buƙata ga kuma ƙuncin rayuwa, wannan shi zai ƙara tabbatar da su ko sashensu a matsayin maroƙa, mabarata a wurin waɗannan kafirai da fasiƙan. Wannan ma mummunan abin ƙyama ne.

Idan kuwa har wani musulmi zai koma ga roƙo ko bara a wurin wani fasiƙi ko kafiri a bayan hakan, to me kenan aka yi? An ƙi cin biri, an ci dila kenan! Ya ƙi karɓar rancen gwamnati a cikin girma da mutunci, ya koma neman irinsa a wurin kafiri a cikin wulaƙanci da ƙasƙanci!

Ko ba daga cikin riban irin waɗannan kuɗaɗen ne ba a kwanan baya aka nuna yadda ake raba wa wasu mata musulmi ba! Waɗanda wasunsu muka ga har kusa da yin ‘ruku’un sallah’ suke yi don girmama mai miƙa musu ƙazamar kyautar!

Ba riban irin waɗannan kuɗaɗen ne ake amfani da su wurin yaudarar wasu matasan musulmi har su bar addininsu ba! Kamar yadda ya faru a wani ƙauye a Jihar Katsina a kwanan baya, wanda suka ba shi shanun noma da takin zamani da kuma maƙudan kuɗaɗe!

Kuma ba daga irin waɗannan kuɗaɗen da musulmi suke ƙyamar karɓar su ba ne ake amfani da su har a fita ƙasashen waje a jikin jiragen sama, don a sayo makaman da ake ta tayar da rikici a yankunanmu, kuma ake ta karkashe mu da su a nan da can, ana raba mu da garuruwanmu da sanaoinmu ba?!

Sannan kuma ba da irin waɗannan kuɗaɗen ne aka yi ta yaudarar matasanmu ana shigar da su ƙungiyoyin taaddanci da sunan jihadi ba?! Jihadin da a kullum hallaka musulmi ya ke a yankunansu, yana ƙyale kafirai da yankunansu!!

Don haka, lallai musulmin da ke buƙata su yi amfani da wannan damar, su karɓi wannan rancen kuma su yi amfani da shi yadda ya dace, kuma su mayar da shi a sadda da yadda aka yi alƙawari. Sannan su sake karɓa in suna so domin amfaninsu da iyalinsu da addininsu.

Allaah ya datar da mu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DIcJIQrWyLP0oBOMSnDi5P

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments