Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Cin Bashin Katin Waya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Wanda ya karɓi rancen kuɗi a cikin layin wayarsa (MTN, GLO, AIRTEL, da sauransu) kamar na 100, sai su kuma su ba shi na 90, wato sun cire ruwan 10 kenan. Menene hukuncin wannan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Idan masu bayar da ‘service’ ɗin suka ce ‘customer’ yana iya rance katin, daga baya kuma a cire daidai kuɗin da ya yi amfani da shi idan ya sanya kuɗi a cikin layinsa, babu komai a kan hakan. Amma idan akwai wata yarjejeniya ko ƙaidar da ta ci-karo da koyarwar Addini kamar ta ƙarin ruwa a cikin tsarin, kamar idan ya yi amfani da katin naira ɗari (100) a lokacin biya kuma sai a cire masa naira ɗari da goma (110), to wannan ne bai dace ba.

Wato dai shiga wannan tsarin bai dace da koyarwar shari’a ba wacce ta hana duk yarjejeniyar da ta ƙunshi bayarwa da karɓan bashi da ruwa:

يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اتَّقُوا اللَّهَ وَذَرُوا مَا بَقِيَ مِنَ الرِّبَا إِنْ كُنْتُمْ مُؤْمِنِينَ ٨٧٢۝

Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku ji tsoron Allaah, kuma ku bar abin da ya saura na riba, in dai kun kasance muminai. (Surah Al-Baqarah: 278).

 فَإِنْ لَمْ تَفْعَلُوا فَأْذَنُوا بِحَرْبٍ مِنَ اللَّهِ وَرَسُولِهِ وَإِنْ تُبْتُمْ فَلَكُمْ رُءُوسُ أَمْوَالِكُمْ لَا تَظْلِمُونَ وَلَا تُظْلَمُون ٩٧٢۝

Idan kuma ba ku aikata hakan ba, to ku yi shirin yaƙi da Allaah da Manzonsa. Idan kuma kuka tuba, to asalin dukiyarku ta ku ce, ba za ku yi cutar ba, kuma ba za a cuce ku ba. (Surah Al-Baqarah: 279).

Kuma Hadisi Ya Tabbata Manzon Allah () Yana Cewa:

ﻋَﻦْ ﺍﺑْﻦِ ﻣَﺴْﻌُﻮﺩٍ ﺃَﻥَّ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲَّ قَالَ: ”ﻟَﻌَﻦَ ﺁﻛِﻞَ ﺍﻟﺮِّﺑَﺎ ﻭَﻣُﺆْﻛِﻠَﻪُ ﻭَﺷَﺎﻫِﺪَﻳْﻪِ ﻭَﻛَﺎﺗِﺒَﻪُ

`{رواه الترمذي}

An Karɓo daga Ibn Mas'ud, Daga Annabi() ya ce: “Allah Ya Tsinewa Mai Cin Riba, Da Wanda Ya Bayar da Ita, da Wanda Yayi Shaida da Kuma Wanda Ya Rubutata”.

 {Tirmizi}

A Wani Hadisin Kuma Cewa Yayi

ﻋَﻦْ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠَّﻪِ ﺑْﻦِ ﺣَﻨْﻈَﻠَﺔَ (ﻏِﺴِّﻴﻞِ ﺍﻟْﻤَﻠَﺎﺋِﻜَﺔِ) ﻗَﺎﻝَ : ﻗَﺎﻝَ ﺭَﺳُﻮﻝُ ﺍﻟﻠَّﻪِ : ﺩِﺭْﻫَﻢُ ﺭِﺑًﺎ ﻳَﺄْﻛُﻠُﻪُ ﺍﻟﺮَّﺟُﻞُ ﻭَﻫُﻮَ ﻳَﻌْﻠَﻢُ ﺃَﺷَﺪُّ ﻣِﻦْ ﺳِﺖٍّ ﻭَﺛَﻠَﺎﺛِﻴﻦَ ﺯَﻧْﻴَﺔً

{ﺭَﻭَﺍﻩُ ﺃَﺣْﻤَﺪُ}

An Karɓo daga Abdullahi bn Hanzalata (Wanda Mala'iku Sukayi Masa Wanka) ya ce: Manzon Allah () ya ce: “Dirhami Ɗaya Na Riba da Mutum Zaici Alhalin Yana Sane, Yafi tsanani Akan Yayi Zina Sau Talatin Da Shida

{Ahmad Ya Ruwaitoshi}

Kuma a cikin hadisin Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

 «الشِّرْكُ بِاللَّهِ، وَالسِّحْرُ، وَقَتْلُ النَّفْسِ الَّتِي حَرَّمَ اللَّهُ إِلَّا بِالحَقِّ، وَأَكْلُ الرِّبَا، وَأَكْلُ مَالِ اليَتِيمِ، وَالتَّوَلِّي يَوْمَ الزَّحْفِ، وَقَذْفُ المُحْصَنَاتِ المُؤْمِنَاتِ الغَافِلاَتِ»

Tarayya da Allaah, da Tsafi, da Kashe ran da Allaah ya haramta sai da haƙƙi, da cin Riba, da cin dukiyar maraya, da juyawa a ranar haɗuwa da maƙiya, da yin ƙazafi wa mata tsararru muminai rafkanannu a kan ɓarna. (Sahih Al-Bukhaariy: 6857; Sahih Muslim: 145).

A taƙaice dai ya kamata mai shiga irin waɗannan tsare-tsaren ya zama ga wanda yake cikin wata matsalar da ta takura masa ga cin bashin ne kawai.

Duk wanda kuma yayi taurin-kai, yaci gaba da karɓa ko bayar da kuɗin ruwa ta hanyar huldarsa da banki ko kampanonin waya, ko Gwamnati, To Ya kamata ya tanadi kayan yaki, Domin kuwa sai Allah ya yakeshi tun daga duniya har lahira.

Allaah ya kare mu daga dukkan hanyoyin hallaka.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments