𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin ko ya halatta mace ta shayar da Ɗanta
nono a gaban Muharramanta? Sannan ina ne ya ke iya zama tsiraicin mace a wajen
muharramanta?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Dangane da hukuncin mace ta fito da nononta waje a
gaban muharramanta don ta shayar da Ɗanta, an samu maganganu kamar guda uku na
Malamai a game da saɓanin
da suka yi dangane da cewa ina ne iyakar tsiraicin 'ya mace a gaban
muharramanta kamar
Ɗanta
Babanta
Ɗan-Mijinta
Ɗan'uwanta
Ɗan kaninta
Ɗan yayanta
1. Ƙauli na farko shi ne, abinda Mazhabin Malikiyya da
kuma Hanabila suka tafi a kansa cewa tsiraicin mace a gaban muharramanta ya
game dukkan jikinta ne amma banda fuskarta, hannayenta, kafafuwanta, da kuma
gashin kanta. Amma ba ya halatta a gareta ta bayyanar da kirjinta ko nonuwanta
a gabansu. Danhaka haramun ne muharraminta ya ga kirjinta ko nonuwanta, ko da
kuwa mahaifinta ne shi, sannan kuma ko da ba da nufin sha'awa ko jin daɗi ya kallaba.
2. Ƙauli na biyu kuma shi ne, Mazhabin Hanafiyya sun
tafi a kan cewa tsiraicin mace a gaban muharramanta shi ne tsakanin cibiyarta
zuwa guiwowinta da cikinta da kuma bayanta. Danhaka ya halatta ya ga dukkan
sauran jikinta in banda waɗancan
wuraren, amma sukace da sharaɗin ya
kasance an aminta da cewa babu wata fitina da a ke zaton kallon zai iya
haifarwa, sannan kuma ya zama ba kallo ba ne ze yi mata irin na sha'awa, idan
kuwa kallon sha'awa ne ze yi mata ko kuma ita za ta ji sha'awa ko daɗi a dalilin hakan, to haramun ne ya ga ni.
3. Ƙauli na uku shi ne abin da Mazhabin Shafi'iyya
suka tafi a kan cewa tsiraicin Mace a gaban muharramanta shi ne tsakanin
cibiyarta zuwa guiwowinta kaɗai,
sukace ya halatta Muharraminta ya iya ganin fuskarta, hannayenta, kafafuwanta,
gashin kanta, kirjinta, nonuwanta, cikinta, da kuma bayanta. Shin muharramin
nan Ɗan'uwanta ne shaƙiƙi na jini ko kuma Ɗan'uwanta ne da suka sha
nono tare, duk hukuncinsu ɗaya
ne.
To amma sai dai maganar da mafi yawan Malamai sukafi
rinjayar da ita ita ce, Ƙaulin
da Mazhabin MALIKIYYA suka tafi a kansa na cewa dukkan jikin mace tsiraici ne,
sai dai ya halatta muharramanta su iya ganinta a yanayin da a bisa al'ada a ke
iya ganin wasu wurare sukan bayyana a jikin mace idan tana yin wasu aikace-aikace
irin na cikin gida.
Wato kamar zira'in hannayenta, wuyanta, gashin
kanta, da kuma Ƙafafuwanta zuwa guiwarta.
Amma dangane da hukuncin tsiraicin Mace a gaban
'yan'uwanta Mata ko da kuwa waɗannan
matan 'yan'uwanta ne na jini, wasu daga cikin Malamai sukace tsiraicin mace a
gaban 'yan'uwanta mata dai-dai yake da hukuncin tsiraicinta a gaban
muharramanta, danhaka sukace ba ya halatta mace ta bayyana tsiraicinta kamar
cinyoyinta da nonuwanta da cikinta zuwa cibiya a gaban wasu Matan, sai dai in
da wata larura mai ƙarfi, amma sai dai wasu Malaman sun tafi ne a kan
cewa hukuncin tsiraicin Mace a gaban 'yan'uwanta mata dai-dai yake da hukuncin
tsiraicin namiji a gaban ɗan'uwansa
namiji, wato daga cibiya zuwa guiwa, to haka suma Mata a tsakaninsu daga cibiya
zuwa guiwa,
Daga ƙarshe idan mukayi duba a kan maganganun da Malamai
suka yi za muga cewa magana mafi inganci ita ce haramun ne Mace ta fito da
nonuwanta fili a gaban muharramanta dan ta shayar da jariri. danhaka ya zama
wajibi a kanta ta san duk yadda za ta yi ta suturce nonuwanta a lokacin da ta
ke shayar da Ɗanta.
шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ
Mυѕтαρнα Uѕмαи
08032531505
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.