Shin Imam Muslim Dalibin Imam Bukhari Ne?

    TAMBAYA (22)

    Sai tambaya ta tabiyu ancemana Muslim yakarbi karatu wajen bukhari kamar ana nufin almajirinsane amma km a wasu Hadith wa anda suka ban banta kowa d fahintarsa shin hakane km sunyi zamani d sahabbai Ina nufin sudin tabi'aine

    AMSA:

    Muhammad Ibn Ismail Abu Abdullah wanda aka fi sani da Imamul Bukhari an haifeshine a garin Bukhara (Tsakiyar Asia) a shekarar 810AC ya rasu 870AC

    Ya fara karatun hadisi yana dan shekaru 11, yayi aikin hajji yana shekara 16, wanda hakan ya bashi damar karatu a wajen manyan malaman Makka da Madina

    Ya tafi Misra inda yayi shekaru 16 ya wuce Asia yana neman karatun hadisai

    Bayan dawowarsa garinsu na Bukhara sai ya tattara hadisan da ya samo a kalla guda 600,000 inda ya fitarda sahihai guda 7,257 wadanda suka inganta daga bakin Ma'aiki SAW

    Duniyar musulunci bazata taba mantawa da gudunmawar ilimin hadisin da ya bayar ba

    Akwai ranar da Imam al-Bukhari yaje Baghdad, malaman can sukaji anata rawawul Bukhari kwatsam wataran sukace zasu gwada qarfin qwaqwalwarsa: Malamai 10 suka tattara dalibansu su 10 sau adadinsu (10) dukkansu dalibai 100 kenan, suka bawa kowanne dalibi hadisi guda daya suka cakuda Matn, Isnad da Rawin hadisai guda 100 sukace Imam al-Bukhari ya gyara wadannan hadisai ya maida kowanne gurbinsa. Abin da kowa a wancan lokacin yasan bazai yiwuba amman cikin ikon Allah sai gashi ba ma iya gyara hadisan yayi ba har saida ya tabbatar musu da cewar wanda ya rawaito hadisin dalibi wane ga isnadinsa can a wajen dalibi wane, matn din wancan shine aka cakuda da na wancan dalibin

    Allahu Akbar ! Dubunnan al'ummar Baghdad sunga abin mamaki a wannan ranar, tun daganan malaman hadisai na duniya suka sallama masa. Ya rasu ne yana dan shekaru 60 inda aka binneshi a Samarkand (Tsakiyar Asia)

    Shi kuma Imam Muslim (Abul Husnain) an haifeshine a shekara ta 202 bayan hijira a garin Naisaburi dake Persia

    Yayi tafiye-tafiyen neman ilimin hadisai, inda yaje Saudiyya, Misra, Syria da Iraq wanda acan ne yayi karatu a hannun Imam Ahmad Ibn Hanbal (Ba a wajen Imam al-Bukhari ba kamar yanda wasu suke fada)

    Ya tattaro hadisai a kalla 300,000 yayinda ya fitarda Sahihai guda 9,200 da ake kiransuda Sahih Muslim

    Ya rasu a shekara ta 261AH kuma an binneshi a inda aka haifeshi (Naisaburi)

    Dukkansu wadannan malamai marubuta Kutubus Sittah (Imam Bukhari wanda yayi rayuwa tsakanin 194AH zuwa 256AH, Muslim 202AH - 261AH, Abu Dawud 202AH - 275AH, Tirmidhi 209AH - 279AH, Ibn Majah 209AH - 273AH da kuma Imam an-Nasa'i 214AH - 303AH) sunyi zamani ne a cikin wadancan karnin guda uku wanda Annabi SAW ya ce "Daga karni na a daraja sai masu biye musu (Tabi'ai) sai masu biye musu (Tabi'utta bi'in)" (Bukhari 2652) sune abin koyi da ake kirada Salaf mai kokarin koyi dasu kuma ana kiransa da As-salafy ko As-salafiya ga mace

    Misalan mabiya Salaf (Wadanda ake kiransu da A'immatul Huda) na kwana kwanannan sune irinsu: Ibn Taimiyya, malamin Ibn al-Qayyim al-Jauziyya shikuma malamin kuma mahaifin Ibn Khathir dukkansu salafiyyun ne, ga irinsu Imamul Qurtubi, Ibn Hajar, Shaikh Nasiriddin Albany, Shaikh Abdulaziz Bin Baaz, Shaikh al-Uthaymeen da dai sauransu (Allah ya jikansu ya karbi ayyukansu)

    Don haka Imam Bukhari ba shine Malamin Imam Muslim ba dukda sun rayu a zamanin Tabi'ai, abin da ya tabbata shine Abu Dawud dalibi ne na Ahmad Ibn Hanbal sannan kuma daga baya ya zamo malamin Imam an-Nasa'i

    Allah ya tabbatar damu akan musulunci bisa fahimtar magabata (Salafus Salih)

    Amsawa:

    Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

    https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURQQ

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.