Ticker

6/recent/ticker-posts

Alamomin Balaga

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Game da yarinyar da ba ta fara haila ba amma ta fara kirgan-dangi, kuma da yaron da bai yi mafarki ba amma ya fara warin hammata, shin za su rama azumin Ramadan da suka sha ko ba za su rama ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Masana sun ce: Alamun balaga a wurin yaro su ne:

1. Fitar maniyyi daga gare shi a cikin barci ko a farke.

2. Tsirar gashi mai ƙarfi mai duhu a mararsa da hammatarsa.

3. Fitowar gashin gemu da saje da gashin baki a fuskarsa.

4. Buɗewar muryarsa.

5. Bayyanar waɗansu ƙurajen pimples a fuskarsa.

6. Samun warin jikinsa (warin balaga).

A wurin yarinya kuwa alamun su ne:

1. Samuwar jinin haila daga gare ta.

2. Bayyanar nono a ƙirjinta, wanda kuma yake cigaba da girma kaɗan-kaɗan.

3. Tsirowar gashi mai ƙarfi mai duhu a hammatarta da mararta.

4. Bayyanar waɗansu ƙurajen Pimples a fuskarta.

5. Sauyi a cikin gashin kanta, ta yadda yakan ƙara zama maniimci mai santsi da laushi.

6. Samuwar warin jiki (watau: Warin Balaga).

7. Ƙarin faɗin ƙugunta.

8. Fitar maniyyi a cikin barci ko a farke.

Don haka, duk wanda ya ga ɗaya daga cikin waɗannan alamomin sai ya kara kulawa da addininsa sosai.

Kodayake wasu Malamai sun nuna cewa babbar alamar balaga a wurin namiji ita ce fitar maniyyi, a wurin mace kuma fitar haila ce, amma dai abu mafi-kyau shi ne su rama duk azumin Ramadan da suka sha kawai, domin fita daga matsala a Lahira. 

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy

 

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RQbbrzgW

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments