Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukunce-Hukuncen Mai Takaba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum wa rahmatullaah. Allah gafarta Malam pls ayi mana bayani koda a takaice ne dangane da hukunce - hukuncen takaba... Na shiga wajen mahaifiya dazu, take cewa in tambaya mata Malamai tanadin shari'a akan wannan al'amari. Nagode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikum assalam To ɗan'uwa ina rokon Allah ya jikan mahafinku, akwai hukunce-hukunce da suka shafi takaba, ga muhimmai daga ciki:

1. Mai takaba za ta zauna a gidan mijinta ba za ta fita ba, har sai ta gama iddarta, wacce take wata huɗu da kwana goma, kamar yadda aya ta: 234 a suratul Bakara take nuni zuwa hakan.

وَالَّذِينَ يُتَوَفَّوْنَ مِنْكُمْ وَيَذَرُونَ أَزْوَاجًا يَتَرَبَّصْنَ بِأَنْفُسِهِنَّ أَرْبَعَةَ أَشْهُرٍ وَعَشْرًا ۖ فَإِذَا بَلَغْنَ أَجَلَهُنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ فِيمَا فَعَلْنَ فِي أَنْفُسِهِنَّ بِالْمَعْرُوفِ ۗ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ

Kuma waɗanda suke mutuwa daga gare ku suna barin mãtan aure, mãtan suna jinkiri da kansu wata huɗu da kwãna goma. To, idan sun isa ga ajalinsu, to, bãbu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu ga al´ãda. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne.

2. Ba za ta saka kaya masu kyau ba, don haka za ta guji ado, kamar yadda hadisin Abu-dawud mai lamba ta: 2304, ya yi bayanin hakan.

3. Shari'a ta hana mai takaba ta sanya turare, kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba ta: 5343, ya tabbatar da hakan,

4. Malamai suna cewa mai takaba ba za ta sanya tozali ba, kamar yadda hadisin Nasa'i mai lamba ta: 3565 ya bayyana hakan.

5. An hana mai takaba yin lalle, kamar yadda hanin ya zo a hadisin Abu-dawud mai lamba ta: 2304.

6. Idan wata bukata ta kama za ta iya fita daga gida, ko da rana ne ko da dare.

7. Za ta iya yin Magana da mazan da ba muharramanta ba, idan bukatar hakan ta kama, saidai ta guji, sanyaya murya, kamar yadda aya ta 32 a suratul-ahzab ta hana sanyaya murya ga wadanda ba muharramai ba.

يَا نِسَاءَ النَّبِيِّ لَسْتُنَّ كَأَحَدٍ مِنَ النِّسَاءِ ۚ إِنِ اتَّقَيْتُنَّ فَلَا تَخْضَعْنَ بِالْقَوْلِ فَيَطْمَعَ الَّذِي فِي قَلْبِهِ مَرَضٌ وَقُلْنَ قَوْلًا مَعْرُوفًا

Yã mãtan Annabĩ! Ba ku zama kamar kõwa ba daga mãtã, idan kun yi taƙawa, sabõda haka, kada ku sassautar da magana, har wanda ke da cũta a cikin zuciyarsa ya yi ɗammani, kuma ku faɗi magana ta alheri.

8. Babu wani launi na kaya na musamman da aka shar'anta mata ta sanya, don haka, duk kayan da ba kwalliya a jikinsu ya halatta ta sanya su .

9. Za ta iya yin wanka da sabulun da yake ba mai kanshi ba.

10. Za ta iya zama ta yi hira da makusantanta, har ma za ta iya buɗe gashin kanta, idan su duka muharramanta ne.

11. Bai halatta wani ya nemi auranta ba, har sai ta gama idda, saidai za'a iya yin jirwaye mai kama da wanka, kamar yadda aya ta 235 a Suratul Bakara ta yi nuni zuwa hakan.

وَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ فِيمَا عَرَّضْتُمْ بِهِ مِنْ خِطْبَةِ النِّسَاءِ أَوْ أَكْنَنْتُمْ فِي أَنْفُسِكُمْ ۚ عَلِمَ اللَّهُ أَنَّكُمْ سَتَذْكُرُونَهُنَّ وَلَٰكِنْ لَا تُوَاعِدُوهُنَّ سِرًّا إِلَّا أَنْ تَقُولُوا قَوْلًا مَعْرُوفًا ۚ وَلَا تَعْزِمُوا عُقْدَةَ النِّكَاحِ حَتَّىٰ يَبْلُغَ الْكِتَابُ أَجَلَهُ ۚ وَاعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ يَعْلَمُ مَا فِي أَنْفُسِكُمْ فَاحْذَرُوهُ ۚ وَاعْلَمُوا أَنَّ اللَّهَ غَفُورٌ حَلِيمٌ

Kuma bãbu laifi a kanku a cikin abin da kuka gitta da shi daga neman auren mãtã ko kuwa kuka ɓõye a cikin zukatanku. Allah Ya san cewa lalle ne ku za ku ambata musu (shi). Kuma amma kada ku yi wa jũna alkawari da shi a ɓõye, fãce dai ku faɗi magana sananniya. Kuma kada ku ƙulla niyyar daurin auren sai littãfin (idda) ya kai ga ajalinsa. Kuma ku sani cewa lalle ne Allah Yana sanin abin da yake cikin zukatanku, sabõda haka ku ji tsõronsa. Kuma ku sani cewa Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri.

12. Idan mai takaba tana da ciki, to iddarta ita ce: haife abin da take ɗauke da shi.

Allah shi ne mafi sani.

Dr. Jamilu Zarewa

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments