Takardar da Aka Gabatar a Taron Ranar Hausa Wanda Ƙungiyar Hausa ta Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato ta Shirya a Harabar Babban Ɗakin Taro na Jami’ar da Ke Mazauninta na Dindindin Ranar Asabar 07 ga Janairu, 2023 da Misalin 11:30 na Safe.
Hausa A Matsayin Harshen Uwa A Farfajiyar Karatun Boko
Daga
Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Nazarin Harsunan Nijerya,
Tsangayar Fasaha da Nazarin Addinin Musulunci,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato
Waya: 0803 431 6508
Ƙibɗau: mabunza @yahoo.com
TSAKURE
Hausa a Matsayin Harshen Uwa a Farfajiyar
Karatun Boko. Za a yi yunƙuri ne da karɓa kiran Gwamnatin Tarayyar Nijeriya kan a zaburar da
harsunanmu na gado su kasance da su ake ba wa ‘ya’yanmu karatu. Na yi ɗan yunƙurin tuntuɓar tsofaffin ‘yan
boko da aka koyar da su karatun boko a cikin Hausa, tun boko na sabo-sabonsa.
Haka kuma, na tuntuɓi ayyuka da dama
na masana fannonin daban-daban domin samun kayan aiki. A gaskiya da na ratsa
duniyar Intanet da Google na amfana fiye da yadda na ratsa ayyukan da ke ɗakin karatu. Binciken ya yi fashin baƙin matashiya tare
da hararar manufar hukuma a kan wannan yekuwa. A ɗan kalli duniyar mutane musamman yawan mutanen da ke ciki
masu adadi fiye da biliyan bakwai. Daga nan aka dubi adadin harsunansu (7,500)
a cikin ƙasashen duniya (195) da suka mamaye kowace ƙasa da harshenta
take amfani. A gida Nijeriya muna da yawan mutane (200,000,000) ɗauke da harsuna (525) cikin jihohinmu (36). Jihar da ta
fi kowace yawan harsuna Bauchi mai harsuna fiye da (66+) kuma Hausa na daga
cikin manyan harsunanta (5). Bisa ga samun harshen Hausa na (11) a harsunan
duniya, kuma na (1) a duniyar baƙar fata, wanda gida Nijeriya da Nijar akwai jami’o’in
tarayya fiye da (13) da ke koyar da ita a digiri da manyan digirori. Wannan ta
ba ta damar samun fiye da Farfesa (100) a halin yanzu (2023). Sakamakon haka,
binciken ya yanke shawarar yankin Nijeriya ta Arewa, su rungumi Hausa, musamman
duba ga gawurtattun daulolinta (8) da ba irin su a faɗin Nijeriya.
Gabatarwa
Faɗar Hausawa na
lokacin abu a yi shi nashin ƙasa ne babu kure. Kowane irin al’amari na duniya yana da lokuta
uku zaɓaɓɓu: Lokacin yin sa, watau lokacin yin sa zaɓaɓɓe; lokacin jiran
lokacinsa, wato a yi dakon zuwansa; na uku shi ne shuɗaɗɗen lokacinsa, wato
lokacin ya zo ya wuce, ko an yi dakon jiransa, har ya zo ya wuce ba a farga ba.
To, Hausawa sun ce, lokaci ya haifi mahaukata uku: Wanda lokacin abu ya wakana ya
ƙi yarda; na biyu
wanda lokacin abu bai yi ba, ya ce sai ya yi; na uku mai ganin kowannensu daidai
yake ga tuninsa da ƙwazonsa.Waɗannan uku duk
mahaukata ne, amma malaminsu watau na ukun ya fi su hauka. Matsalar lokacin da
ya wuce ba ya waiwayowa bale a kira shi. Don haka, kiran da Gwamnatin Tarayya
ta Nijeriya ta yi na a dawo da rakiyar harshen TURANCI/INGILISHI, a tsarin
karatun makarantunmu na boko, a dawo da harshen “uwa” wata sabuwar gudunmawa ce
ga cigaban iliminmu. Ba mu da wata makawa face mu fito mu bayar da gudunmawarmu
gadan-gadan har sai kowane tsuntsu ya yi kukan gidansu. Haƙiƙa wannan maganar
babba ce, babin da za ta mamaye a karatu, babba ne, ko ma mu ce, littafin kanta
take nema daga gare mu. A ‘yar mahangarmu ɗalibai ga ɗan abin da na
hango:
Tunanin Bincike
Na ɗan yi nazarin hangen irin ra’i daga cikin ra’o’in masana
da ya kamata in ɗora wannan aiki.
Cikin duba nan, duba can, sai na ga ai kamata ya yi karen da ya yi cizo a nemo
gashinsa a yi magani. A kan wannan tunani na ga ya dace in ɗora wannan aiki bisa ga wani fitaccen karin magana ko
zantukan magabatanmu da za su yi canjaras da tunanin Gwamnatin Tarayya a kan
komawa ga harshen uwa ga karatun boko. A ganina, wannan aikin kamata ya yi in ɗora shi a kan wata fitacciyar maganar hikima da ke fita a
bakunan magabata idan sun ga an saɓa wa gaskiya, aka
sake dawowa neman agajinta bayan ‘yan dabaru da wayon masu saɓa mata ya ƙare. Za a ji su suna cewa: “DOLE UWAR NA ƘI” (Naƙi) wato da dole da
na ƙi ba su taɓa zama a inuwar itaciya ɗaya ba.
A tunanin zancen an ce ‘Dole” uwar ‘Naƙi” ke nan “Dole”
mace ce, Kuma ‘yar da ta haifa “Naƙi” mace ce. A nahawu ai za a ce: Ai Naƙi ita ce uwar Dole.
“Dole” kuwa ‘yar “Naƙi” ce. Samun tsigalau “‘yar” ya dangantar da nasaba ga “mace” ba namiji ba,
domin ba a ce “ɗan” ba. A
tunaninmu ɗalibai da gangan
na mayar da su mutane domin in samu damar feɗe biri har wutsiyarsa. A nahawun rubutu, ai kalmar “Naƙi” a rarrabe ake
rubuta su: “na ƙi”, ni na haɗe su domin in sama
wa “Dole” ɗiya mai suna “Naƙi.” Wannan abin
shi ke aukuwa a karatun bokon Nijeriya tun fil azal da harshen uwa ake boko,
mulkin mallaka ya haramtar da shi, yanzu ba su, ba mulkin, jirgin bokon
Ingilishi ya kasa kai mu ganga, ya kasance bungali shigar mai yarda. Da wuya ta
yi wuya, aka ga gara a mayar da na hannu gida, kana a dawo a kama na dawa. Shiga
wannan tunani ya ba ni damar samun ra’in wannan bincike: “DOLE UWAR NA ƘI”. Ga yadda na
fasalta binciken:
Fashin Baƙin Matashiya
Matashiyarmu an ɗora ta a kan jimla ɗaya mai sassa biyu ga tsarin nahawu. Sashe na farko shi ne: “Harshen Uwa”....A
kan haka na ga dole mu lalubo ma’anar harshe domin da shi aka yi turke a
matashiyar. Masana sun ce, harshe shi ne:
Ingilishi:
“The principal method of human
communication consisting of words used in a structured and conventional way and
conveyed by speech, writing or gesture.”
Fassara:
“Wani fitaccen makamin sadarwa mai ƙunshe da kalmomi da aka tsara su bisa jerin gwanon
daidaituwar nahawu aka sadar da su a lafazance, ko a rubuce, ko cikin sigar manuniya.”
A wata fassarar
masanan sun ce, harshe shi ne:
“A
system of communication used by a particular country
or community.”
“Wani tsarin salon sadarwa da wata ƙasa ko wasu al’umma ke amfani da shi.”
Babu wai, cikin waɗannan fassarorin mun fahimci harshe na mutane ne, kuma
mutane ke sadarwa da shi, bugu da ƙari, tsira yake yi cikin al’umma ba wahayinsa ake yi ba.
A ko’ina ya mamaye cikin ƙasa ko al’umma ya zama harshensu kuma da shi ake kiran
su, su karɓa. Ga alama,
kasancewar “uwa” mafi kusa ga yaran da aka haifa shi ya kawo sunanta ‘Uwa” kusa
ga kalmar “Harshe” aka samu “Harshen Uwa”. Uwa a fassarar Ingilishi ita ce:
“Mother” wanda Ƙamus ya fassara da cewa:
“Mother is countable noun, your mother
is the women who gave birth to you. You can also call someone your mother if
she brings you up as if she was this women.”
A wata fassarar
cewa suka yi uwa ita ce:
“A female parent.”
“A women in authority.”
“Uwa suna ne, a nahawu yana cikin suna ƙirgau, uwa ita ce wadda ta haifi mutum (da cikinta). Haka
kuma ana iya cewa wata mata “uwa” idan ita ta reni mutum har ya kai
hayyacinsa.”
Fassara ta biyu
cewa ta yi, uwa ita ce:
“Mace mahaifiya.”
“Mace da ke da cikakken iko.”
Ɓangare na biyu na matashiyarmu shi ne, “Farfajiyar
Karatun Boko.” Farfajiya ita ce iyakoki ko kuma kadadar wani abu da za a duba
iya kallon mai kallo. Duniya gaba ɗaya tana iya zama
farfajiya, ƙasa na iya kasancewa farfajiya, haka ayyuka da ake gudanarwa na ilimi da
fasaha na ɗaukar fassarar
farfajiya. A kan wannan fassarar na ɗauki fagen ilimi
na Boko ko na Addini, a matsayin wata farfajiyar karkara ga mabuƙata ilmi. Karatun Boko,
an yi masa fassarori daban-daban (Newman,2000) da (Adamu, 2000) da
(Bunza,2001). A taƙaice, a tawa fahimta fassarar “boko” a wajen Bahaushe biyu ne: Ƙarya, yaudara da ƙwambo, amma ita
kalmar daga “book” aka samo ta, duba zuwa ga abu na farko da boko ya zo da
shi, shi ne “littafi” sunan abu na farko da za a koya wa yara shi ne “book”.
“What is this? It is a book”. Dubi wannan waƙar yara zuwa ga ‘yan boko:
:’Yan makarantar bokoko,
: Ba karatu ba salla,
: Sai yawan zagin Malam.
Harshen Uwa a Tunanin Ma’ilmanta
Matsalar ilmi a
ko’ina ta tsira ba ta rasa alaƙa da al’adun wurin da ta tsira. Zancen harshen uwa ga harshe
tunani ne na Turawa da ma’ilmanta domin a daidaita su ne. A tunanin masana harshen
uwa shi ne:
Ingilishi:
“The language which a person has growwn up
speaking from early childhood.”
Fassara:
“Harshen uwa shi ne harshen da mutum ya
tashi ciki ya tarar da ana yin sa, ya tashi da shi tun a yaranta.”
A faffaɗar ma’anar harshen uwa a mahangar masanin ilmin koyarwa
ita ce:
Ingilishi:
“Mother tongue education refers to any
form of schooling which uses the languages that children are most familiar
with, in order to help them learn. This usually the language that children
speak at home with their family. The “mother tongue” does not have to be the
language spoken by the mother.”
Fassara:
“Harshen
uwa shi ne harshen ilmi da ake koyo a makaranta, wanda ake amfani da harshen da
yara suka fi sani, domin ya taimaka musu ga koyo wannan harshe a al’ada shi ne
harshen da yara ke magana da shi a gida cikin iyayensu da danginsu. “Harshen
Uwa” a nan ba dole sai harshen da mamar yaro ke magana da shi ba.”
A shekarar 25
July, 2019 an fassara kalmar da:
“The term mother tongue refers to
person’s native language that is a language learned from birth. Also called a
first language.”
A mahangar Encyclopedia.com
8 June, 2018 Mother Tongue.
“A general term for the language of
childhood home, learned “at one’s mother knee.”
“Harshen uwa na nufin harshen gado
harshen da aka koya daga haihuwa. A wata fassara ana ce da shi: Harshen Farko.”
“Harshen Uwa shi ne harshen da aka
tashi da shi tun haihuwa a gida, an koye shi a tun ana dafe da guiwowin uwa.”
Harshen Uwa a Tunanin Bahaushe
Bahaushe bai saɓa wa ma’ilmanta a fassararsa ba, sai dai idan an ce “Harshen Uwa” zai ji
bin bambarakwai ka ce:
a.
Uwa ke da harshen ba uba ba.
b.
Uwa ta fi uba daraja ga ɗa.
c.
Uwa ke da ɗan ba uba ba.
d.
Ɗan uwa yake bi ga gado ba uba ba.
e.
Uwa ta fi uba ƙarfi ga yaron.
f.
Uba ba ya da wata rawa ga koyon harshen ɗansa.
Waɗannan abubuwa da makamantansu, su ke sa Bahaushe zai ji ɗan ƙaiƙayi idan aka ce “harshen uwa” ga yaron da ke da
uwa da uba, ko a raye ko a mace. A wajen Bahaushe gado ga uba ake yin sa ba ga
uwa ba. Idan uba na Bagobiri uwa Bakaba, yaron da aka haifa Bagobiri ne, don
haka karin harshen Gobirci ne karin harshensa. Ai shi ne dalilin da ya sa, idan
an je yi wa irin waɗannan yara tsagar
fuskar gado, ta Gobirci ake yi musu. Sai dai idan gefen uwar na da ƙarfi da nacewa,
sai a yi tsagar uban ga haɓar dama, ta uwar
ga haɓar hagu. Haka nan
ke aukuwa ga Hausawan Jamhuriyar Nijar yanzu haka.
Tunanin waɗannan abubuwa da ka iya tasowa ya sa Bahaushe ya fi natsuwa
a ce, “harshen gado.” Da jin haka Bahaushe ya san harshen mahaifiya ake nufi,
amma ba harshen da aka tashi ciki ba. Harshen da aka tashi a ciki sunansa
harshen gari ko harshen ƙasa ko harshen al’umma, ba dole ya kasance harshen
mahaifiyar yaro ba. Wannan tunani ga fassarar harshen uwa yana da kyau a
fayyace shi sosai Bahaushe ya lura da shi, wanda ba Bahaushe ba ya san dalilin
da Bahaushe yake da su a kan fassara kalmar “harshen uwa”.
Harshen Uwa a Karatun Bokon Nijeriya
A tsarin karatun
bokon Nijeriya da an ambaci cewa a dawo da koyar da karatun boko da Hausa
rigingimu za su tashi na, wane harshe za a sa ya limanci harsunan da ke cikin ƙasa? Babban abin
da ya kyautu ga ɗaliban ilmi a gane
shi ne:
i.
A duniyar mutane muna da mutane sama ga malaliyar
(biliyon) bakwai (7).
ii.
Waɗannan mutane
biliyon bakwai sun amfani da harsuna fiye da dubu bakwai da ɗari biyar (7,500).
iii.
Waɗannan harsuna
(7,500) suna warwatse cikin ƙasashe ɗari da tis’in da
biyar (195) na duniya.
iv.
Kowace ƙasa daga cikin ƙasashe (195) na duniya tana da harshenta na gado.
v.
Gabanin ilmin boko kowace ƙasa da harshenta
take gudanar da kowwane irin al’amari na ci gaban al’umarta, kuma ba ta
kasa ba, fasaharta ba ta daƙile ba, sai cigaba take har zuwa lokacin da aka samu
cigaban zamani.
vi.
Ilmin boko ya barbazu a kowane lungu na cikin ƙasashen duniya
(195) amma har yanzu babu ƙasar da ta dakatar da amfani da harshenta na gado ko ta
haramtar da shi, har ya mutu. Don haka ke nan harshen gado mutu ka raba ne ga
kowace al’umma ga kowace ƙasa. Ba shi gurbi ya taka rawa ga ilmi dole ne.
Duba zuwa ga waɗannan hasashe-hasashe da muka lissafa, za mu ga cewa,
tunanin a mayar da gami a koma ga harshen gado ba wata matsala ba ce, domin ba
kashe harsuna aka yi ba, suna nan yaudararsu aka yi. Haka kuma, matsalar komawa
ga harshen gado matsalar duniya ce gaba ɗaya ba Nijeriya kawai ba. Bari mu ɗan waiwayi ƙasarmu mu ga halin da da harsunanmu suke ciki da yadda za su ji, in an ce,
a sake reshe a kama uwa.
Harsunan Nijeriya
A gida harsunanmu suna da yawa. Duk da haka,
yawansu ba zai hana a koma ga zaɓaɓɓu daga ciki a bayar da ilmi a cikinsu ba. A ƙiyasin da ma’ilmanta suka yi a
Nijeriyarmu ta wannan ƙarni (2023) harsunan da ke cikin Nijeriya sun kai ɗari biyar da ashirin da biyar ko fiye (525) harsunan a yi
musu zubi zuwa gida tara (9) kamar haka:
1.
Hausa tana da mutane masu magana da ita fiye da miliyan
(80).
2.
Yoruba suna da masu magana da shi fiye da mutum miliyan
(50).
3.
Igbo suna da masu magana da su fiye da miliyan (30).
4.
Efik-Ibibiyo suna da masu magana da su fiye da miliyan
(15).
5.
Fulfulde suna da masu magana da su fiye da miliyan (13).
6.
Kanuri na da masu magana da shi fiye da miliyan (8).
7.
Tiv na da masu magana da shi fiye da miliyan (5).
8.
Nupe na da masu magana da shi fiye da miliyan (3).
9.
kare-kare, Kupa, Kakanda, Edo, Igala, Idoma, da Izon
(miliyan 2-3).
10.
Jimilla za a ga sun kai miliyan ɗari biyu da shida (206)masu magana da rayayyun harsunan
Nijeriya.
Nazarin Harsunan a Fagen Karatun Boko
Ko kusa ban ga wata matsala ga cewa a koma wa
harsunan gado ba idan muka dubi yanayin ƙasar nan mai yawan mutane fiye da miliyan ɗari biyu (200,000 000) a samu miliyan ɗari biyu da shida (206) masu magana da rayayyun harsunan
gado. Mu yi lissafi mu gani, muna da rayayyun harsuna ɗari biyar da ashirin da biyar (525) muna da yawan mutane
fiye da miliyan ɗari biyu (200,000
000). Idan muka raba yawan mutanen da muke da su da harsunan da muke da su, za
a samu a ƙalla ko da kowane harshe sai an yi amfani da shi za a samu dubu ɗari biyu da tamanin da ɗari tara da hamsin da biyu (280,952). A duniyar da muke
ciki ta yau (2023) babu ƙasa daga cikin ƙasashen duniya (195) da ɗauki irin wannan salon. Don haka mafi adalcin salon da za
a zaɓa shi ne:
1.
A dubi yawan masu magana da harshe a ɓangaren da mazauna suke a sa harshen a matsayin harshen
karatu. Abin nufi a nan shi ne, misali a Arewa a ce a sa harsuna uku:
i.
Hausa mai mutane miliyan tamanin (80).
ii.
Fulfulde mai muatne miliyan (13).
iii.
Kanuri mai muatane miliyan (08).
2.
Babu laifi idan an kasa Nijeriya Lardi-lardi a ce, duk ƙasar da ke da
babban lardi wato (Kingdom) ta zauni harshenta na gado, ke nan abin ya kasu
kamar haka:
i.
Hausa.
ii.
Borno.
iii.
Nupe.
iv.
Yoruba.
v.
Igbo.
vi.
Efik-Ibibio
Ga su nan dai.
Ke nan a nan duk
al’ummar da ba ta da ƙasa ta kanta sai ta hanzarta gyara nata harshe, amma dole ta bi ƙasar da take ƙarƙashinta ta yi
amfani da harshenta. Wannan tun fil azal haka ake ba zai kawo wata ƙaramar magana ko
doguwa ba. Turawa sun so su yi haka, tsoron mu haɗe kai mu yaƙe su, su ka ƙi tabbatar da wannan hasashe.
3.
Hasashe na uku shi ne, ko a duba cikin harsunanmu duk
wanda yake da salon rubutu da karatu nasa na gado a ba shi damar gudanar da
ilminsa kai tsaye. Haka ake yi tun gabanin tahowar “boko” domin karatun
Musulunci ya riga shi. A karatun baƙaƙen Larabci akwai na Hausa akwai na Fulani akwai na Kanuri akwai na Yoruba
akwai na Adarawa akwai na Kyangyanci akwai na Zarma (Zabarmawa) ga su nan dai.
Muhallin Hausa a Tsare-tsaren Harshen Karatun Boko
Harshen Hausa ba
ya da wata matsala a fuskantar kiran da Gwamnatin Tarayya ta yi na mayar da
boko cikin harshen uwa.Abubuwan da za mu duba a nan su ne:
1.
Tun fil azal da Hausa ake karatun addini a ƙasar Hausa.
2.
Addinin Musulunci da Larabci ya zo aka Hausantar da shi.
3.
An gina rubutun Ajami ya riga ya bunƙasa cikin harshen
Hausa.
4.
An fassara littattafai masu tsarki Injila da Alƙur’ani cikin Hausa
fiye da ƙarni ɗaya (shekara ɗari).
5.
Fitattun littattafan addinin Musulunci an fassara su
cikin Ajamin Hausa.
6.
An yi ayyukan addinin Mishon da yawa cikin Ajamin Hausa.
7.
A wannan ƙarni babu harshen da ya kai Hausa ayyukan fassara na
fannoni daban-daban cikin harsunan Afirka ɗari bakwai (700).
Kafin zuwan Larabci Hausa ta yi nisa wajen
goyon wasu ƙananan harsuna da yin tasiri cikinsu, da yin maraba da ita, ba tare da faɗa ba. Wannan wata dama ce ta nuna za su fi yarda da miƙa wuya ga Hausa
fiye ga sauran harsunan da ba ita ba. Idan aka ba wa Hausa dama a Arewa ba ƙaramin ci gaba za
a yi ba, domin ta riga ta fara hanya an rage zango sosai.
Karatun Boko
A cikin karatun Boko Hausa ta fi sauƙin a je da ita a
dawo da ita ba tare da matsala ba. Abin da ya kyautu mu ɗan ce a nan shi ne:
1.
Tun bayyanar boko a Arewa fiye da ƙarni ɗaya ta samar da harufan Karatun Boko.
2.
Da aka kafa makarantun boko da Hausa ake koyar da
magabatanmu tun a aji 1-4 sai a aji 5-7 ake saka ƙaƙale (Ingilishi).
3.
Maakarantunmu na gaba da firamare suna Hausa, suna da
malaman Hausa, masu ilmin Hausa da koyara da ita.
4.
A makarantun gaba da sakandare ana yin karatun Hausa a
Diploma da NCE.
5.
A jami’o’inmu ana karatun Hausa a B.A, B.A (ed), M.A, M.A
(ed), PGD, da Ph.D. Sin wau ra takurin boko ke nan.
6.
Yau a shekarar (2023) muna da fiye da Farfesa ɗari (100) a fannin Hausa a duniya, wanda babu harshen da
ke da rabinsu daga cikin harsunan Nijeriya (525). Tirƙashi! Ashe girma
ya kawo tsoro ya ɗebe.
7.
A fagen fassara tuni Jami’ar Bayero, Kano ta fara fassara
littattafan kimiyya zuwa Hausa a matsayin somin taɓi. To! Daɗa ga fili ga mai
doki.
Yawan Ƙasa da Jama’a a Arewa
Masu kirdado sun
tabbatar da akwai kimanin mutane miliyan (80) masu magana da harshen Hausa a
matsayin harshen gado ko harshe na biyu. a ɗan nawa bincike in an ce da “harshe na biyu (L2) to,
Hausa za ta haura miliyan ɗari (100) domin ko
a daulolin Borno, Nupe, Yoruba, da Fulani za a taras kamar daulolin ƙasar Hausa ne,
saboda hatta da sarakunasu da Hausa suke amfani, wasu da Hausa ake yi musu waƙoƙi; kuma akwai
kafafen yaɗa labaran Hausa a
daulolin. Idan za mu fasalta Hausa bisa ga daulolin da ta kafa da waɗanda take sarauta, za mu ga dauloli kamar haka:
|
Daula |
Karin Harshe |
Cibiya |
1. |
Kano |
Kananci |
Kano |
2. |
Katsina |
Katsinanci |
Katsina |
3. |
Gobir |
Gobiranci/Sakkwatanci |
Sabon Birni |
4. |
Zamfara |
Zamfarci |
Anka/Gusau |
5. |
Kabi |
Kabanci |
BirninKabi/Argungu |
6. |
Zazzau |
Zazzaganci |
Zariya |
7. |
Maraɗi |
Maraɗanci/Arabci |
Maraɗi |
8. |
Damagaran |
Damagaranci/Arabci/Maraɗanci |
Zindar |
Babu wata ƙabila ko al’umma daga cikin al’umman Nijeriya da
ke da yawan tsofaffin dauloli da suka kafa ƙarfafan gwamnati
irin daulolin ƙasar Huasa. Abin ban sha’awa duk harshe ɗaya ake amfani da shi, sai dai karin harshe ya ɗan bambanta ko shi kuwa kowa na fahimtar abin da kowa ke
faɗa. Bisa ga ƙiyasi kusan kashi
80% na Arewacin Nijeriya da kashi 50% na Jamhuriyar Nijar, Hausa ce babban
harshe. Ashe ba ta wuri a tsarin koyar da karatun boko a Nijeriya ta Arewa da ɓangaren Nijar bisa ƙa’ida yake.
Tasirin Hausa ga Sauran Harsunan Nijeriya
An ce a ko’ina Bahaushe ya je da harshensa
yake yawo. Idan ya yi kaka gida a wuri sai dai a koyi harshensa ba dai ya koyi
na wasu ba. A wata riwayar ‘yan kasuwar Legas da Ibadan da Aba, sun ce, Hausawa
ba koyon harshen suke yi ba, daga sarɓa-sarɓa har su ƙware. Su kuwa ‘yan
ƙasa sai dai su zo
su koya a wajensu. Akwai ɓurɓushin son kai ga wannan hasashe, na kawo shi domin a
tattauna. Ɗan abin duba a nan shi ne, za a ga harshen Hausa ya yi naso sosai cikin
harsunan Nijeriya da yawa.
i.
Duba cikin Yarbanci hatta da mawaƙinsu Olushola sai
da ya sa Hausa cikin waƙar ta’aziyyar Janar Murtala Ramat Muhammad.
ii.
Dubi Fulani masu wasan shaɗi. Shaɗi gadonsu ne, amma
babu mawaƙan shaɗi Bafulatani dole
da Hausa ake yi musu kiɗa da Hausa suke
kirari.
iii.
Dakarkari da Farfesa Mahdi Adamu ke ganin asalinsu
Hausawa ne suka rikiɗa saboda nisa da ƙasar Hausa suka
tsiri nasu harshe. A waƙe-waƙensu har na jana’iza za a ga suna Hausa: “Zai shiga rami, babu gardama”
rugudum! Rugudum! A cashe da kiɗa.
iv.
Lokacin da Bukar Suka Dimka suka shirya wa Janar
Babangida juyin mulki, sun fi goma ‘yan kudancin Zariya, kowannnensu da
harshensa daban. Dole da Hausa suka dinga maganganunsu har sai Dimka ya ce: “Kai
amma dai Hausawa sun cuce mu, hatta da harshenmu sun cinye.” Don haka ya fitar
da tushen Hausa daga Nijeriya, Sakkwato ya ce: “Su koma Nijar”.
Raba Gardama
Ga ɗan binciken da ya
gabata masu ɗari-ɗarin ganin wai, ‘yan bambance-bambancen karuruwan karin
harshenmu da cunkoson harsunanmu za su zama mana tarnaƙi ga saka
harshenmu na gado ga karatun bokonmu su sake lale. Idan za mu waiwayi tsarin
harsunanmu na duniya (7,500) za mu ga:
1.
Harshen Mandarin (Patonghua) shi ne na ɗaya a duniya da yawan muatne biliyan ɗaya da miliyan ɗari huɗu (1.4 billion)
masu magana da shi. A cikin “Sin” China akwai harsuna ɗari uku da biyu (302) Mandira ke da kashi 70% ya rinjayi
harsunan Vue, Xiang, Min, Gan, Wu Kajia da Hakka. Don cigaban ƙasa kowa ya bai wa
Mandari goyon baya, yau (2023) sun kasance harshe na ɗaya a duniyar mutane.
2.
Idan za mu koma ga Ingilishi da ya mamaye mu, ya mayar da
mu ƙauyawa tushensa ya
karkasu zuwa kashi huɗu:
i.
Kentish in the South East.
ii.
West saxon in the South West.
iii.
Mercian Midland territories of Mercia.
iv.
Northumbrain North.
Ingilishi yana da
kare-karen harshe (160) a cikin UK kawai akwai karin harshe (40) wanda ke da
bambancin furuci, da rubutu, da ginin kalmomi. Turancin Amerika kaɗai yana da mutane miliyan ɗari biyu da ashirin da biyar (225 million), tattare da
bambancin Ingilishi na Canada, Australia, Newzeland, South Africa, da India. Waɗannan abubuwa sun isa su kasance misalai ga masu ganin
wai akwai matsalar karin harshe ko wani bambancin harshe a cikinmu. Yaya aka yi
tattare da waɗannan
bambance-bambance suka manta da su, suka zo suka mamaye mu, suka tilasta
harshensu a kanmu?
Gurbin Harshen Uwa ga Karɓar Karatu da Bayar
da Karatu
Babbar manufar bai wa harshen uwa damar maye
gurbin harsunan ‘yan mulkin mallaka da suka mamaye mu ba girma da arziki shi ne
farko mu tabbatar da ‘yanci1n kawunanmu. Wanda duk ba a damu da amfani da
harshensa na gado ba, yana na a matsayin bauta komai talalar da aka yi masa da
sunan ‘yanci. Tilasta wa mai koyo ko mai koyarwa amfani da wani harshe wanda ba
na mai bayar da karatu ba, ba na mai koyon karatun ba, wani tarnaƙi ne babba cikin
ilmin koyarwa. Masana sun ce:
Ingilishi:
Mother tongue is a language which a
child starts learning after being born and thus it also helps in providing a
definate shape by our emotions and thoughts. Learning in the mother tongue also
in crutial is enhencing other skills such as critical thinking, skills to learn
a second language and literacy skills.
Fassara:
Harshen gado shi ne harshen da yaro ya
faro koyon wasu abubuwa da haihuwarsa. Babu wai, shi zai taimaka wajen daidaita
tunaninmu da ƙudurce-ƙudurcen da muke ɗokin aiwatarwa. Tabbas! Koyo da koyarwa
cikin harsunanmu na gado zai taimaka wajen agaza wa ƙoƙarinmu da wasa tunaninmu, da kuma
himmar koyon harshen da ba na gado ba, da iya sarrafa shi wajen yaƙi da jahilci.
Idan ba da harshen
gado ake koyar da yaro ba, harsunan biyu yake koyo, amma cikin tunanin harshe ɗaya (na gado). Dole tunani da basira su ragu domin
bincike ya tabbatar da cewa:
Ingilishi:
Education in the mother tongue is a key
factor for inclusion and quality learning, and it also improves learning outcomes
and academic performance.This is crutial especially in primary school to avoid
knowledge gap and comprehension. www.Unesco.org>article>
Fassara:
Koyarwar ilmi
cikin harshen gado, wani babban makami ne na, inganta ilmi ga zukatan masu
koyo. Haka kuma za a samu sakamakon koyarwa ta kasance mai kyau har masu koyo
su kasance haziƙai ga darussan da suke koyo karatunsu ya kasance nagartacce. Amfani da
harshen gado muhimmi ne ƙwarai musamman a makarantun Firamare domin a kasance
koyaushe ana tare da yara cikin darusan da ake koyar da su, sai tazarar rashin
fahimta ta taƙaita.
Wannan tunanin UNESCO ta fitar da shi bayan da ta yi
bincike mai zurfi a ƙasashen da ake koyarwa da harshen gado da waɗanda ake koyarwa cikin harshen da ba na gadonsu ba. Ashe
tuni ma’ilmantan duniya sun hango matsayin harsunan gado a farfajiyar karatun
boko. Me ya rage ga Nijeriya ta Arewa, in ba aiwatarwa ba?
Ƙololuwar Tunanin
Boko
A ko’ina karatun
boko ya yanke cibi musamman ƙasashen da ke ƙarƙashin mulkin mallakar Ingila abubuwa uku ne duwatsun
murhun ɗagwaro tukunyar tuƙa tuwon boko da
miyarsa. Abu na farko shi ne, a tabbatar da “Harshen Ingilishi” ne limami. Duk
wani harshe haramun ne a zurfafa ilmin da za a biya albashi da shi in ba nasu
ba. Duk mai hankali ya san ba da ba ilmi ne kan gaban tsarinsu ba, illa
tabbatar da al’adu da addinan Birtaniya cikin zukatan ƙasashen da ta yi wa
ƙwacen mulki da su
tabbata Turawa so da ƙi. Ba don matsalar bayar da ilmi da karɓarsa da “Ingilishi” ba, da ba a san iyakacin cigaban da ƙasashen mallakar
Birtaniya suka kai ba.
Sauran duwatsun girka dahuwar boko su ne,
lissafi (mathematics) , Physics (Fisika), Chemistry (Maganaɗiso), da Biology (Ilmin Halittu). Ɗan abin da za a
lura, a duniyar mutane waɗanda suka ƙago waɗannan fannoni da waɗanda suka yi zara a ciki a duniyar wannan ƙarni (2023) ba da
baƙon harshe suka yi
nasarar fice ba da harshensu na gado ne. Fitaccen masanin lissafi a ƙarni na 21st
Grigori Perelman (Haihuwa, 13 June,1966) Rasanci ne harshen gadonsa, da shi ya
yi karatu. A ilmin Physics (Fisika) a duniya fitaccen masani shi ne, Albert
Einstein, Bajamushe ne, da Jamusanci ya yi karatu. A fannin ilmin Chemistry
(Maganaɗiso) ƙasashe biyar da
suke jagorantar duniyar (2023) su ne: Germany, Ireland, Uk, USA, Australia, da
China. Kowannensu da harshensa na gado ake bayar da ilmin boko a dukkanin
makarantunsu.
Matakan Cigaba
Ba mu da wani mataki da ya zarce faɗar Bahaushe cewa wuyar aiki ba a fara ba. Tun tuni mun
fara aka zo aka daina, yau mun ga dole uwar na ƙi babu makawa sai
mun sake bitar karatunmu. Daga cikin ayyukan da ke kanmu su ne:
1.
Kafa ƙaƙƙarfan kwamitin amintattu masu kishi su ba da shawarorin yadda za a tunkari
aikin da ke gabanmu.
2.
Na biyu, dole tunanin kafa wani gawutaccen kwamitin
masana na fannoni daban-daban kan yadda za a tunkari fassara ba dare ba rana.
3.
Na uku, dole tunanin yadda za a samar da da ƙwararru daga
cikinmu waɗanda masana na
fannoni daban-daban da za su bayar da gudunmuwa.
4.
Na huɗu, haɗa kan masana Hausa wuri ɗaya a ba gabaci haƙƙinsa mu yarda gaba da gabanta mu sa magabatanmu gaba a yi
aiki tare domin a gudu tare a tsira tare. Mu daidaitu a kan ƙa’idojin rubutu, da
wallafe-wallafenmu, da sauran ayyuka mu kasance tsintsiya maɗaurinki ɗaya.
Sakamakon Bincike
Haƙiƙa tunanin Gwamnatin Tarayya ya kasance a kira shi, faɗuwa ta yi daidai da zama. Wannan bincike ya hango daga
cikin yawan mutane biliyan (7) da ke cikin duniya, masu magana da harsuna
(7,500) a cikin ƙasashen duniya 195, Nijeriya ke da mutane fiye da miliyan ɗari biyu (200,000 000) tana da jihohi (36) masu harsuna
(525). Daga cikin adadin harsunan duniya Hausa ita ce ta (11) don haka a Afirka
ko duniyar baƙar fata ita ce ta ɗaya. A Nijeriya
ita kaɗai ne al’umma mai
dauloli (6) babu kwatankwacinta. Ita ke da tsayayyen rubutu da karɓuwa a farfajiyar boko, mai Farfesoshi fiye da ɗari (100) a fannonin karatu daban-daban. A kan wannan,
bincikena na ganin ya kamata a ce, dukkanin daulolin ƙasar Hausa da
jihohin da ke ƙarƙashinsu su mayar
da Hausa harshen karatun bokon yaransu gaba ɗaya. A halin yanzu akwai jami’o’in tarayya goma sha biyu
(12) da ke ba da digiri a fannin karatun Hausa. Na yarda da Makaɗa Sani Sabulu na Kanoma a faɗarsa da ke cewa:
: Ko ba magana a zura ido,
: Ta ishi mai hankali.
Kammalawa
Babu ƙasar da ta cigaba da harshen wasu ba nata ba. Mu sa lura
mu ga ƙasashen (G.7) masu
arzikin man fetur a duniya babu ƙasar da ba da harshenta take amfani ba. Ƙasashen da ke da
saukakkin addinai daga Allah, babu ƙasar da ba da harshenta take amfani ba. Ƙasashen da ke da
makamai masu linzami duk da harsunansu suke amfani. Ƙasashen da suka fi
kowace ƙasa kuɗaɗe masu ƙarfi da duniya ke ji da su, duk harsunansu na gado suke s
amfani da su. Ashe dai, ƙasashen da aka mamaye harsunansu aka hana musu amfani da
su, ba su da komai sai tsiya da maguɗi da
tashintashina. Allah Ya tsare mu, Ya tsare wuyan raƙuminmu in ji Buzu
da ya ga mai maƙoƙo.
MANAZARTA
Abbas, S. (2000) “Ethnomathematics of Hausa Socio-cultural
Environment. Towards a New Pedagogy
of Teaching Mathematics in Primary Schools”, PhD thesis, Zaria: Ahmadu Bello University.
Adamu, M. (1975) “Hausa Factor in West African History,
Zaria: Ahmadu Bello University Press.
Alexender, F. (1968) “Some Linguistics Problems of Nation
Building in Negro Africa.” In Language Problems of Developing Nations,
New York: Willey Pp.119-127.
Baldi, S. (1975) “A systematic Hausa Bibliography”, MA
thesis, USA:Duquesre University.
Birnin Tudu, S. Y. (1990) “Nazarin
Rubutun Ajami a Ƙasar Hausa” kundin MA, Sakkwato:Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.
Bunza, A. M.(2022) “Harshen Hausa
Madugun Jaddada Addininin Mususlunci: Waiwaye Ciki
da Wajen Daular Mususlunci ta Sakkwato”, takardar da aka gabatar a Makon Ɗanfodiyo, Sokoto:
Sultan Macciɗo Institute, 27/10/2022.
Bunza, A. M. (2022) “Gurbin Harsunan Gado ga Neman Ilimi da Ilmantarwa”, takardar
da aka gabatar a makon Shehu Ɗanfodiyo, da Majalisar
Haɗin kan Ƙungiyoyin Matasa Musulmi ta shirya, Sokoto:Sultan
Macciɗo Institute, 28 Oktoba, 2022.
Chambarlin, A. (1975) “The Development
of Islamic Education in Kano City Nigeria, with Emphasis on Legal Education in the 19th-20th Centuries”, PhD thesis, Colombia: Colombia University.
Crystal, D. (1993) A Dictionary of Linguistics and Phonetics, 3rd Edition. London:
Blackwell Publishers.
Dry, D. P. L. (1953) “The Place of
Islam in Hausa Society”, PhD thesis, Oxford: University
of Oxford.
Emenanjo, E. N. (1991) “The Study of Nigerian
Languages in Nigerian Universities: The Past,
the Present and the Future.” in Rufa’i, A. (ed) Nigerian Languages: Yesterday, Tomorrow
and Future.” Proceeding of the 20th Year
Commorative Symposium of CNL, Bayero University, Kano.
Fischar, S. R. (2023) A History of Writing, London: Breaktion
Books, 79 Farringdon Land.
Furniss, G. L. (1991) “Hausa Language
Studies: The Present. In Rufa’i, A. (ed) Nigerian
Langages” Yesteday, Tomorrow and Future.
Proceeding of the 20th Commemorative
Symposium of the CSNL, Bayero University, Kano.
Garba, A. M. (2002) “Islamic Scholarship
in Hausaland from 16th-18th Centuries a Study in
Katsina, Zamfara, and Kebbi”, Phd thesis Sokoto: Usmanu Danfodiyo University.
Hair, P. E. (1967) The Early Study of Nigerian Languages Essays and Bibliographics, London: Cambridge University Press.
Hiskete, M. (1975) “Materials Relating
to the State of Learning Among the Fulani Before the Jihad”, in BSUASXIX.
Ikara, B. (Ed) (1982) Nigerian Languages and Cultural Development.
Lagos: National Language
Centre.
Ikara, B. (1991) “Hausa Language
Studies: A Projection for the Future”, in Rufa’i, A. (ed) Nigerian Languages: Yesterday, Tomorrow and
Future.” Proceeding of the 20th Year
Commemorative Symposium of CSNL, Bayero University, Kano.
Jagger, P. A. (2000) Hausa. Amsterdam:John Benjami.
Kani, A. M. (1992) “Arithmetic in the
Pre-colonial Central Sudan”, in Thomas Emegwali,
G. (ed) Science and Technology in Africa 20th Case Studies From Nigeria, Sierraleone, Zimbabwe and Zambia, The
Edwin Mella Press.
Kirk-Greene, A. H. M. (1964) “The Hausa
Language Board”, Afrika and Ubarsee. Band XL. VII, No. 14, Pp:187-203.
Mani, M. (1978) Zuwan Turawa a Nijeriya ta Arewa, Zariya: NNPC.
Newman, P. (1991) “Century and a Half
of Hausa Language Studies”, in Rufa’i, A.(ed)
Nigerian Languages: Yesterday, Tomorrow and Future.” Proceeding of
the 20th Year Commemorative
Symposium of CSNL, Bayero University, Kano.
Newman, P. (2000). Encyclopedic Reference Grammer of Hausa, London and New Haven:
Yale University Press.
Olagoke, D. O. (1979) The Mother Tongue and ESL in Nigerian
Education. In Ubarakwe et.al The
Teaching of English Studies. Ibadan: University Press.
Olaoye, R. A. (ed) (2009). History of Indegenous Science and Technology
in Nigeria, Ibadan: CreseHill Publishers.
Yahaya, I. Y. (1988) Hausa a Rubuce, Tarihin Rubuce-rubuce Cikin
Hausa. Zaria: NNPC.
Yalwa, L. D. (2018) “Position of Hausa
as a National Language and Lingua Franca in Nigeria and West Africa”, in Bayero Journal
of Linguistics, Kano: Bayero
University Press P. 1-26.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.