Ticker

6/recent/ticker-posts

Fried Rice

Fried Rice 😋

Fitattun Kayan Haɗi

* Shinkafa

* Peas

* Man gyaɗa

* Nama

* Albasa

* Kayan Ɗanɗano

* Kayan Ƙamshi

* Karas

* Dankali

* Curry

Fried Rice

Fried Rice

Lura: Waɗannan fitattu ne kawai daga cikin kayan haɗin. Ana iya samun sauye-sauye (daɗi ko ragi), wanda hakan ya danganta ga salo da ra'ayin mai girki.

Mataki na farko:- Za ki gyara namanki, ki tafasa shi da albasa da tafarnuwa da kayan kamshi da magi daya da gishiri kadan (Ya danganta da yawan naman).

Mataki na biyu:- Bayan kin sulala, sai ki tsame naman a wani kwano daban.

(Za ki soya naman, ki yanka su kanana ki ajiye a gefe).

Mataki na Uku:- Sai ki qara ruwa a kan ruwan da kika tafasa naman, daidai yadda za ki tafasa shinkafarki.

Mataki na hudu:- Sai ki saka tumeric da su curry (Sabida ya yi color) ki saka kayan dandano da kayan kamshi daidai yadda kike so shinkafar ta bayar da dandanon.

Mataki na biyar:- Sai ki rufe ki bari ya tafasa.

Mataki na shida:- Bayan ya tafasa sai ki wanke shinkafarki ki zuba. Ki juya ki rufe da foil paper.

Mataki na bakwai:- Ki ba shi lokaci kadan ya dahu ruwan ya tsote.

A kula📌

(Kar a bari ya yi laushi sosai, za a dafa shi ne wara-wara).

Mataki na takwas:- Bayan ya dahu sai ki sauke a gefe.

Mataki na tara:- Ki dora tukunya a kan wuta, ki saka mangayada daidai yadda kike so, ki saka albasa da aka yanka.

Mataki na goma:- Ki juya ya fara soyuwa, sai ki saka jajjagen kayan miya (Attarugu da tattasai da albasa) Ki rufe ya tsotse ruwan jikinsa.

Mataki na sha daya:- Bayan ya fara soyuwa ki bude ki saka karas da kika yanka da green beans da peas.

Mataki na sha biyu:- Sai ki zuba gishiri kadan, ki saka ruwa kadan ki rufe su yi laushi.

Mataki na sha uku:- Bayan sun yi laushi daidai yadda kike so, sai ki kawo shinkafarki da kika dafa ki zuba. ki juya ya hade sosai.

Mataki na sha hudu:- Ki kawo namanki da kika soya kika yanka kanana ki zuba a kai.

Mataki na sha biyar:- Ki zuba albasa da kika yanka duk yankan da kike so ki zuba, da tattasai ja da kore da kika yanka ki zuba. Ki juya sosai ya hade.

Mataki na sha shida:- Ki kawo ganyen albasa da kika yanka ki zuba ki juya ya hade.

Mataki na sha bakwai:- Ki rufe ki ba shi kamar minti biyar su kama jikinsa, wuta kasa-kasa.

Mataki na sha takwas:- Shikenan in kika bude za ki ji yana kamshi komai ya yi daidai. Shikenan an kammala.

**

Ana ci da coslow, ko a haka ma. Yana da dadi sosai.

A ci daɗi lafiya.

Daga:

Ummu Amatulqahhar Kitchen 
(Humaira'u)

Post a Comment

0 Comments