𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, Malam Ina Maka fatan alkhairi
duniya da lahira. Malam na kasance muna soyayya da wata yarinya, mun jima muna
tare bamuyi aure ba sai yanzu muke shirin auren. Malam kwananan Shaiɗan ya fara shiga tsakanin mu har mun fara
taɓa juna amma yanzu Inshã
Allah na daina. na rage zuwaa wajenta sabida hatsarin dake cikin hakan. Dan
Malam Ina neman addu'arka da shawaranka kafin ace an saka mana ranan aure.
Nagode Allah ya haɗa Mu
cikin rahamar sa ya kuma gafarta Mana.ameeen.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Allah Maɗaukakin Sarki da ya haliccemu ya ajiye wasu
amanoninsa ajikinmu. Daga cikin waɗannan
amanonin akwai hannayenmu, Qafafunmu,
Jinmu, ganinmu, Tunaninmu, Har al'aurorinmu.
Daga lokacin da ka ɗauki wani abu cikin waɗannan abubuwan ka saɓa ma Allah dashi, to hakika kaci amanar
Allah kenan. Shi yasa aranar Alqiyamah Allah zai tsayar dakai agaban Zatinsa,
sannan ya sanya gaɓoɓin jikin naka su rika bada shaida bisa
dukkan ayyukanka.
Kaji tsoron Allah ka tuna cewa yana nan tare dakai
aduk inda kake. Kuma zai iya ɗaukar
ranka aduk sanda yaso. Idan kana gadarar cewa zaka tuba, Ai Allah zai iya ɗaukar ranka kafin ka tuba ɗin. Don haka kaji tsoron Allah ka dena
Kokarin aikata Zina.
Manzon Allah ﷺ ya ce : "A SOKA MAKA KIBIYAR BAQIN
QARFE ACIKIN KANKA, SHI YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA KA SHAFI JIKIN MATAR DA
BATA HALATTA GAREKA BA".
Kamar yadda ba zaka so a aikata hakan da 'Yarka ko
Qanwarka ko yayarka, Ko Mahaifiyarka ba, to itama wannan yarinyar ai 'Yar wani
ce, Qanwar wani ce, Kuma watarana zata zama Uwar wani.
Idan har kuka ci gaba da aikata wannan abin, to
lallai kun zubar da dukkan albarkar auren. Don haka itama kaja kunnenta ku dena
wannan abun.
Koda ka biya sadakinta, Koda an sanya muku rana,
bata halatta gareka ba, har sai bayan an daura muku aure.
Allah ya shiryeku ya shiryemu baki ɗaya, ya gafarta mana, ya gyara dukkan
ayyukanmu.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.