Ticker

6/recent/ticker-posts

Baban Luba Uban Nana, Baban Aminu Alhaji Shehun Malami

"Baban Luba Uban Nana,
Baban Aminu Alhaji Shehun Malami" 

Inji Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun a faifan sa na Marigayi Mai Girma Sarkin Sudan Na Wurno, Alhaji Shehu Malami Murabus mai amshi 'Ba dakai aka wargi ba.. A wannan hoto Marigayi Mai Girma Sarkin Sudan Na Wurno Alhaji Shehu Malami Murabus ne zaune a gefen hagu tare da Uwargidan sa Hajiya Asma'u Yar Marafan Sakkwato, Alhaji Ahmadu Usman Ɗanbaba kuma Jikanyar Marigayi Mai Girma Sardaunan Sakkwato, Sir Ahmadu Bello GCON KBE, Firimiyan Jihar Arewa na farko. Allah ya kyauta makwanci, amin.

Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments