Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Annabi Isah Zai Dawo Duniya A Matsayin Annabi Ne?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

munyi imani da Annabi isah zai dawo duniya, shin zai dawo a matsayin annabi ne? kuma Annabinmu ya ce ba wani Annabi bayana. kokuma awani matsayi zai dawo?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Dafarko: Dalilai na Ayoyi da hadisai da haɗuwan malamai, sun yawaita akowani zamani da kowani gari a kan cewa, shugabanmu Annabi muhammad (Sallallahu Alaihi wasallam) shi ne cikamakin Annabawa da manzanni.

Duk wanda Yayi da'awar Annabci bayansa to lallai shi makaryacine, kuma Dajjaline.

Allah ya ce:

مَا كَانَ مُحَمَّدٌ أَبَا أَحَدٍ مِنْ رِجَالِكُمْ وَلَٰكِنْ رَسُولَ اللَّهِ وَخَاتَمَ النَّبِيِّينَ ۗ وَكَانَ اللَّهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمًا ٠٤۝

Muhammadu bai kasance uban kõwa ba daga mazanku, kuma amma shĩ yã kasance Manzon Allah kuma cikon Annabãwa. Kuma Allah Ya kasance Masani ga kõme. (Suratul Ahzaab:40)

Ibnu kaseer ya ce:

Allah ya faɗa acikin alqur'ani, sannan kuma Annabi ya faɗa acikin hadisai ingantattu daga gareshi cewa:

Babu wani Annabi a bayana, duk wanda zai yi da'awar Annabci abayana yasan cewa shi makaryacine ɓataccene mai ɓatarwa. Koda yayi wani abinda mutane bazasu iyayiba. Wato yazo da wani bakon abu da ya fita daga al'adan ɗan adam. Yayi rufa idonsa. Koda yazo da sihiri da bokanci. Dukansu korarrun abune kuma shi ɓataccene awajen masu hankali. Kamar yanda ya gudana  da Aswadul Ansiy a kasar yaman. da musailamatul  kazzab agarin yamama.

 Na karya da barna da magan-ganun masu muni. Wanda duk mai hankali da tunani yasan cewa su makaryatane, ɓatattune Allah ya la'ancesu.

Hakanan duk wani mai irin wannan da'awar har zuwa ranar alkiyama har lokacinda ogansu dujal zai fito.

Tafsiru Ibnu kaseer ( 6/ 430 -431)

Bukhari (3455) da muslim (1842) sun ruwaito hadisi daga Abu huraira Allah ya kara masa yarda. ya ce manzon Allah (sallallhu Alaihi wasllam) yace.:

Banuu israa'ila sun kasance Annabawane ke jagorantarsu, duk lokacinda wani Annabi ya mutu sai Allah ya basu wani Annabi a madadinsa sai Annabi ya ce Amma babu wani Annabi a bayana.

Sannan muslim (523) ya ruwaito hadisi daga Abu huraira yace.:  Annabi (sallallahu alaihi wasallam) yace.:

An fifitani a kan sauran Annabawa da abubuwa shida.

1. An bani matattarin kalmomi acikin zance.

2. An sanyamin kasa duka tazama mai tsarki kuma masallaci (duk inda sallah ta kamaka kayita anan.)

3. An halastamin cin ganima.

 4. Anbani nasara (kan abokan gaba) Tahanyar jefa musu tsoro azukatansu tsakanina dasu Nisan tafiyar wata guda.

5. An aikoni zuwaga mutane baki ɗaya.

6. Anrufe Annabta daga kaina.

Abu isah attirmiziy (2272) ya ruwaito hadisi daga Anas ɗan malik Allah ya kara masa yarda ya ce manzon Allah (sallallahu alaihi wasallam) yace.:

Lallai  manzanci da kuma Annabta ya Kare daga kaina. Babu Wani Annabi abayana kuma babu Wani manzo Bayana.

Albani ya ingantashi acikin "Sahihu Turmuzi" Malaman hadisi sukace: Isanadin hadisin ingantaccene abisa sharaɗin ruwayar Muslim"

Dan haka babu wani Annabi bayan manzon Allah (sallallahu alaihi wasallam)

Dalilai da suka tabbatar da saukowar Annabi isah (Alaihissalam) akarshen zamanai, zai saukone yayi amfani da hukuncin shari'ar manzon Allah (sallallahu alaihi wasallam) Bawai zaizo da sabon sako bane.

Al'imamul bukhari (2222) da Muslim (155) ya ruwaito hadisi daga Abu huraira Allah ya kara masa yarda yace. Manzon Allah (sallallahu alaihi wasallam) ya ce:

ina rantsuwa da wanda raina yake hannunsa Annabi isa ya kusa ya sauko yana mai hukunci da adalci zai karaya gumaka, ya kashe aladu, ya sanya jiziya ga kafirai, sannan ya kwarara dukiya hassai kowa ya wadata yazama babu mai karɓa.

 *Al' iraqy rahimahullahu ya ce:*Abin nufi shi ne Annabi isa zai sauko yayi amfani da shari'ar manzon Allah ba amatsayin wani manzoba. Domin shari'arsa an shafeta. Shi kuma shari'ar manzon Allah (sallallahu alaihi wasallam) tananan baza'a  shafetaba har Zuwa ranar alkiyama.

"Darhul tasreeb (8/117)

Muslim (156) ya fidda hadisi daga jabir dan Abdullahi Allah ya kara masa yarda ya ce:  manzon Allah (sallallahu alaihi wasallam) ya ce:

wasu daga cikin al'umata bazasu gusheba suna yaki harsai Annabi isa ya bayyana acikinssu. Sai jagoransu ya ce masa kazo ka mana sallah sai Annabi isa yace, Lallai sashinku shuwagabannine ga sashi. Wanda Allah ya girmama wannan al'uma dashi. 

Akwai hadisai masu yawa da wasu ayoyi da suka nuna dawowar Annabi Isa duniyar nan tamu, Amma

Da wannan takaitattun Nassoshi nake cewa Lallai Allah ya tabbatar mana da dawowar Annabi isa amatsayin bawa kuma mai bin shari'ar manzon Allah (sallallahu alaihi wasallam) bawai zaizo da sabon sako bane.

Saboda haka dawowar Annabi Isah (Alaihissalamu) baya cin karo da faɗin Annabi (Sallallahu Alaihi wasallam) cewa: ( Babu Wani Annabi Abayana) da faɗinsa ( Duk wanda yai da'awar Annabta Abayana makaryacine) dasauran Nassoshi Ingantattu.

Annabi Isah zaidawo Amma ba'a matsayinsa Na Annabi ba, A'a zaidawo Amatsayinsa na Mabiyin Shari'ar da aka Aiko Annabin rahma fiyayayyen Halitta Muhammad Ɗan Abdullahi (Sallallahu Alaihi wasallam)

Shiyasa Wasu malamai suke sanya Annabi Isah daka cikin Sahabban Manzan Allah (Sallallahu Alaihu wasallam).

Dan haka Annabi isa zaibi bayan limamin da ya samu yana jagoranci.

Haka malaman lajnatul da'imah suka bayyana acikin fatawa lajnatul da'imah amsar tambayata ( 3/328- 329)

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments