Ticker

6/recent/ticker-posts

Lum’a A Bayan Sallame Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mace ce ta yi sallar Azahar, sai bayan wani ɗan lokaci kafin fitar lokacin sallar aka ce mata akwai lum’a sakamakon liƙewar selotep a tafin ƙafarta. Shin za ta sake sallar ne, ko kuwa yaya za ta yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

Idan dai a haka abin ya faru, to kenan ta yi sallah ba da cikakkiyar alwala ba, don haka sallar ba ta yi ba. Tun da dai alwala sharaɗi ne ga sallah, kamar yadda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗa:

« لاَ تُقْبَلُ صَلاَةُ أَحَدِكُمْ إِذَا أَحْدَثَ حَتَّى يَتَوَضَّأَ »

Ba a karɓar sallar ɗayanku idan ya yi hadasi har sai ya sake alwala. (Sahih Al-Bukhaariy: 6954, Sahih Muslim: 559).

Yana nufin cikakkiyar alwala irin yadda ya siffanta a cikin Alqur’ani da kuma yadda Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya koya wa sahabbansa, kamar a cikin hadisin Uthman Bn Affaan da waninsa daga cikin sahabbai (Radiyal Laahu Anhum).

Don haka wajibi ne wannan matar ta sake wannan sallar har abada, saboda wannan hadisin sahihi:

Daga Umar Bn Al-Khattaab (Radiyal Laahu Anhu) ya ce: Wani mutum ne ya yi alwala sai kuma ya bar wurin ƙumba a kan ƙafarsa bai wanke ba, sai kuwa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya gan shi, shi ne ya ce:

« ارْجِعْ فَأَحْسِنْ وُضُوءَكَ »

Koma ka gyara alwalarka.

Ya ce: Sai kuma ya koma ya yi sallar. (Sahih Muslim: 599).

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/K7RkQRMf2b57l3UENoJ1Or

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments