Ticker

6/recent/ticker-posts

KANONMU (Don tuna Ranar Zaman Lafiya ta Duniya a Yau)

Ita dai Dimukuraɗiyarmu,

A Kano ribarta gunmu,

Shi ne raba kawunanmu.


Baƙar gaba da sharri,

Ta kawo nan jiharmu,,

Ta dasa a cikin gidanmu.


Ta raba mu da 'yan uwanmu,

Majiɓunta rayuwarmu,

Masu amfani gare mu.


Malamanmu sarakunanmu,

Tajirai da dukkan matasa

Ta rarraba kawunanmu.


'Yan siyasa masu mulki,

Ke amfana gare ta,

Da yawanmu muna ta gaba.


A Kano tuni na fahimta,

Wannan tsari na mulki,

Tarko ne mu gare mu.


Tarbiyya al'adunmu,

Ke rusawa da sannu,

Gobara sai mu gane.


Ya Allah ga Kanonmu,

Wutar gaba ƙiyayya,

Ta siyasa don Habibu.


Ka kashe mana ya Tabara,

Kasa jama'ar Kanonmu,

Su dawo hayyacinsu.


Mu daina biyewa gaibu,

Muna sara da sukar,

Cikinmu muna kirari.


' Yan uwa ne mu dukkanmu,

Addini ya haɗe mu,

Jiha duka ta haɗa mu.


Khalid Imam naku,

Ke jawo hankulanmu,

Mu mai da wuƙa kubenta.


Shi ci gaba babu shakka,

Bai da taki sai haɗin kai,

Na sa aya a nan gun.

Malam Khalid Imam
08027796140
khalidimam2002@gmail.com

Post a Comment

0 Comments