TAMABAYA (07)❓
Assalamu alaikum brk d sapia yg y alamura...Allah
y temakA. Nace watace tace n tmbya mata Dan Allah menene sahihin mafarkin mage
kuma tana cizonta?? Ngd
AMSA
Waalaikumussalam, warahmatullahi, wabarakatuhum
Fassarar mafarki ilimi ne mai zaman kansa saboda
indai har mutum yana iya tuno mafarki to yanada cikakkiyar ma'ana tunda da
akwai hadisin da ya tabbata daga Manzon Allah SAW akanmafarkin alkhairi (kamar
na Umra ko Hajji) bushara ce daga Allah SWT, mafarkin sharri kuma (kamar na shaidanun Aljanu ko na shanuwa tana
tunkushin mutum) to daga shaidan ne, saikuma mafarkin da mutum yakeyi silar
faruwar wani abu (kamar mutum yaci abinci mai yaji sai ya kwanta baisha ruwaba,
zai iya mafarkin gashinan a kusada kogi yana shan ruwa)
Allah SWT ya labarta mana mafarkin da Annabi Yusuf
AS yayi na ganin rana, wata da taurari guda 11 wanda mahaifinsa Annabi Yaqub AS
ya fassara masa da cewar Allah zai daukakasa akan yan uwansa. Da kuma labarin
fassarar mafarkin da Annabi Yusuf yayiwa wadanda aka rufesu a kurkuku tare
Sannan kuma Annabi SAW ya kasance idan ya idar da
sallah yakan juyo ya fuskanci sahabbansa RA ya tambayesu shin ko da akwai wanda
jiya yayi mafarki ? (Idan an samu sai Annabi SAW ya fada musu fassarar
mafarkin)
Imam Malik (Rahimahullah) ya kasance yana da dalibi
mai suna Muhammad Ibn Seerin (An haifeshine a garin Basra wato Iraq a shekara
ta 33 bayan hijira wanda yayi daidai da 653AD), haka kuma Imam Ibn Seerin ya
koyi karatu a wajen Alhasan Ibn Abi al-Hasanul Basry, Ibn Aown, Al-fudhayl, Ibn
Iyadh. Allah SWT ya azurta Ibn Seerin da ilimin fassarar mafarki wanda musamman
ya rubuta wani shahararren littafi mai suna "Muntakhab Al-Kalam fi Tafsir
Al-ahlam
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.