Ticker

6/recent/ticker-posts

Zaƙewa Wurin Kwalliya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Allaah gafarta malam, shi wannan irin kwalliya da mata suka fito da shi a wannan zamanin yaya yake ne a cikin addini? Yadda mace take sauyawa daga surarta ta asali kwata-kwata, wani lokaci ko mutum mahaifinta ne, in ba an ce masa wance ce ba, ba zai ma iya ganewa ba!

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Da farko dai musulunci bai hana mata yin kwalliyar da ba ta wuce iyaka, ko wacce ba ta saɓa wa ƙaida ba:

قُلْ مَنْ حَرَّمَ زِينَةَ اللهِ الَّتِي أَخْرَجَ ِعِبَادِهِ

Ka ce: Wanene ya haramta kayan ado da kwalliya na Allaah da ya fitar domin bayinsa?

Don haka, halal ne mace musulma ta riƙa yin wanka, da wanki, tana tsabtace jikinta, da tufafinta. Ta shafa mai a jikinta, da kanta, domin ya ƙara laushi, da taushi, ta riƙa yanke ƙumbunanta, ta riƙa sanya kwalli ko tozali a idanunta, ta sanya zobe, da warwaro da sarka, da ɗan kunne irin yadda suka dace da koyarwar shari’a. Haka kuma ya halatta ta riƙa yin amfani da kyawawan tufafin da aka ɗinka su yadda ya dace, kamar atamfa, da shadda, da leshi, da sauransu. Kuma ya halatta ta bayyana hakan a gaban muharramanta, kamar mijin aurenta, ko mahaifinta, ko kawunta, ko baffanta, ko yayanta, ko ƙaninta, da sauransu yadda dace.

Amma idan kwalliya ta wuce iyakar shari’a, to a nan ne musulunci bai yarda ba, kuma ya hana musulma yinsa. A nan ga waɗansu nau’uka kwalliya da mata suke amfani da su a yau, amma kuma Malamai suka nuna cewa ba su dace da koyarwar musulunci ba:

1. Ƙarin gashin kai.

2. Aske gashin gira.

3. Aske ko saita ko ƙara gashin ido.

4. Feƙe haƙora don yin wushirya.

5. Rina furfura da baƙin launi.

6. Tsawaita ƙumbuna.

7. Sanya wa ƙumbuna fenti.

8. Mayar da gashin-kai ya koma kamar na turawa.

9. Sanya a-cuci-maza a kai.

10. Amfani da mai ko hoda masu sauya launin fatar jiki.

11. Amfani da ‘eye-shadow’.

12. Amfani da jan-baki.

13. Yin zane a fatar jiki (tattoo).

14. Mace ta sanya tufafin maza.

15. Sanya matsattsun tufafi masu nuna kaurin gaɓoɓin jiki.

16. Sanya tufafi shara-shara masu nuna launin fatar jiki.

17. Amfani da tufafin da ke bayyana sashe ko dukkan al’aura.

18. Amfani da takalma (high-heeled shoes).

19. Sanya tufafi irin na kafirai.

20. Bayyanar da kwalliya ga waɗanda ba muharramai ba.

Hana yin amfani da waɗansu daga waɗannan abubuwa ya zo a cikin nassoshi sahihai sarihai a fili ƙarara, waɗansu kuma an fitar da hukuncinsu ne daga gamammun ƙaidojin sharia masu hana a yi amfani da su, kamar cewa suna jawo lahani ko taadi ga lafiyar jiki, ko kuma kamar cewa su koyi ne da kafirai. Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

مَنْ تَشَبَّهَ بِقَوْمٍ فَهُوَ مِنْهُمْ

Duk wanda ya kamantu da wasu mutane, to yana tare da su.

A nan akwai wasu masu raunin imani da suke cewa: Idan an hana koyi da kafirai a cikin al’amuran rayuwa, me ya sa ba mu ga su kansu malamai sun daina amfani da kayan ƙere- ƙere da kafiran suka yi ba, kamar su motoci da jirage da wayoyi da sauransu?!

Amsa a nan shi ne:

1. Da farko dai ba a yi wa addini irin wannan tambayar ta nuna raini da rashin kunya! Domin tun tuni Allaah Ta’aala ya ce:

لَا يُسْأَلُ عَمَّا يَفْعَلُ

Ba a tambayarsa a kan abin da ya aikata.

Sannan kuma Allaah Maɗaukakin Sarki ya ce:

وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ وَلَا مُؤْمِنَةٍ إَذَا قَضَى اللهُ وَرَسُولُهُ أَمْراً أَن يَّكُونَ لَهُمُ الْخِيَرَةُ مِنْ أَمْرِهِمْ وَمَن يَّعْصِ اللهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالاً مُبِيناً

Bai kamaci wani mumini ko wata mumina ba, idan Allaah da Manzonsa ya yanke wani al’amari, ya zama suna da wani zaɓi na su na-daban a cikin al’amarinsu.

2. Sannan kuma ai wannan ilimin na ƙere-ƙere zamaninin yinsu ne Allaah ya kawo shi, kuma ba wani abu ne da ya keɓanta da kafirai kaɗai ban da musulmi ba. A yau muna ji da ganin yadda ’ya’yan musulmi da yawa suke shiga fagen ƙere-ƙeren, kuma suke yin fice da gwargwadon hali da iko.

3. A ƙarshe kuma, wannan hani da aka yi a kan koyi da su ba a kowane fanni ba ne. Ya dai shafi irin abin da suka saɓa wa dokokin shari’armu da shi ne na ƙirƙira a cikin addini, da saɓa wa kyawawan ɗabi’u da halaye na-gari abin yabo. Shi ya sa babu malamin da ya ƙyamata, balle ya hana tsarin kiliya dama ko hagu a wurin tafiya, ko shan maganin da bai ci karo da koyarwar sharia ba.

Wata kuma ta ce: Tana yin irin wannan ado da kwalliyan ne domin ta burge mijinta, ta ƙara janyo shi gare ta, ta hana shi kallon wasu mata a waje, musamman dayake akwai mata kafirai da fasiƙai da suke amfani da hakan suna ɗauke hankulan maza?

Amsa a nan sai a ce:

1. Wannan ma dai ba dalili ba ne, kuskure ne babba. Wai shi wannan mijin wane irin musulmi ne da ayyukan saɓon Allaah da kafirai da fasiƙai suke tafkawa ne suke burge shi? Wane irin musulmi ne haka da ya zama cewa kyakkyawar kwalliyar da shariar musulunci ta halatta wa matarsa ba ta burge shi ba, sai irin wadda shaiɗan ya ƙawata wa mabiyansa ne yake so?!

2. Kuma ba amfani da irin waɗannan kayayyakin kwalliyan a cikin gidaje domin wai a burge mazaje ne a yau ya haifar da abin da ya zama ruwan-dare ba? Inda ake ganin yaran mata da ’yan mata suna amfani da su a wajen gidajensu, suna bayyanawa ga samarinsu da sauran waɗanda ba muharramansu ba?! Kuma ga shi nan kullum abin sai ƙara haɓaka yake yi, yana janyo munanan ayyuka irin na fyaɗe da sauransu, duk kuwa da wa’azi da gargaɗin da Malaman Sunnah suke ta yi?! Waɗansu ashararan ma nema su ke Malamai su halatta musu amfani da irin waɗannan kayayyakin!!

3. A taƙaice dai, ko da an samu mijin da yake shaawar waɗannan kayayyakin kwalliyan, kuma har yake sayo su domin matarsa ta yi amfani da su, abin da ya fi a fahimtarmu a yanzu shi ne, bai kamata ta yarda ta yi masa biyayya a kan haka ba, saboda maganar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da ya ce:

لَا طَاعَةَ لِمَخْلُوقٍ فِي مَعْصِيَةِ الْخَالِقِ

Babu biyayya ga wani halitacce a cikin saɓon Allaah Mahalicci

Allaah ya ƙara mana ilimi mai amfani.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments