Ticker

6/recent/ticker-posts

Bikina Ya Kusa, Me Zan Sha Dan Ƙara Ni'ima?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Bikina yau sauran wata daya; don Allah Malam ka taimaka ka fada min abin da zan sha yadda ni’imata ta ‘ya mace za ta karu, domin ina son in faranta wa mijina sosai a ranar daren farkonmu

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Ina yi miki addu’ar Allah Ya ba ki ikon cikar burinki na faranta wa mijinki rai a ranar daren farkonku da ma sauran dararen da za su biyo baya, Ameen.🤲

Ga shawarwarin da nake fatan za su amfane ki in Shã Allah:

1. Tun da dai ke budurwace baki taɓa aure ba, to ki guji duk wasu kayan da’a ko hakkin maye da za a ba ki don ki sha, domin tun asali irin waɗannan magunguna an yi su ne don matan da suka dan jima cikin aure kuma zuumar sha’awarsu ta dan fara sanyi.

Waɗanda ba su taɓa aure ba kuwa zuumarsu na nan da zafinta, don haka babu wani dalili na zukakata da irin sinadaran zukakawa; wannan ke sa nan gaba a samu rikirkicewar sha’awa domin yamutsa ta din da aka yi da waɗannan sinadarai maimakon a barta ta tafiyar da kanta a kan irin tsarin da Allah Ya tsara mata.

2. Amma kina iya shan ‘ya’yan itatuwa da yawa gab da bikin naki, inda hali ma, kina iya daina cin duk wani abinci illa ‘ya’yan itatuwa da ganyayyaki kaɗai kamar ana sauran sati ɗaya bikin naki.

3. Haka ma magungunan Musulunci da ka samu ingancin warakarsu daga Manzon Allah , irin su zuma, habbatus sauda, zaitun da sauransu. Waɗannan za su warkar miki da duk wani rauni ko cikas da kila kina da shi a lafiyar jikinki da ta ruhinki gaba ɗaya.

4. Sai kuma ki rika yawan shan ruwa, a kalla ki sha kofi takwas na ruwa kullum.

5. Sannan ki tsabtace zuciyarki da kyawawan shau’uka da tunani da kyautata zato da fatan alheri. Allah Ya ba ku zaman lafiya tare da sauran dukkan ma’aurata Musulmi, Ameen 🤲

Allah ta'ala yasa mudace.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fb6ƙgYPXfEeHb8CD1SWAkK

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments