Ticker

6/recent/ticker-posts

Waye Fasiƙi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Don Allaah Malam, ina son a yi mini cikakken bayani a kan: Wanene fasiƙi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Cikakken bayani sai manyan Malamai, amma ni ɗan abin da na sani ne kawai zan faɗa:

FASIƘANCI shi ne: Kangarewa ko taurarewa ko ficewa daga dokokin Ubangiji a fili ƙarara, maana: Duk wanda wata doka ta Allaah a cikin Alƙurani ko Sahihiyar Sunnar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ta je masa, wadda kuma take ƙunshe da wani umurni ko hani, amma kuma sai ta taurare, ya yi ƙememe, ya ƙi aikata wannan umurnin, ko kuma ya ƙi nisantar wannan hanin, to ya zama fasiƙi kenan, mai fita daga yi wa Allaah Taaala ɗa’a da biyayya.

Malamai sun yarda cewa Fasiƙanci iri biyu ne, kamar yadda Kafirci da Mushirikanci da Munafunci da Zalunci da Bidi’anci kowannensu iri biyu ne, akwai babba akwai kuma ƙarami.

Babban fasiƙanci shi ke fitar da mai aikata shi daga cikin musulunci gaba-ɗaya, ya shigar da shi cikin tawagar kafirai.

A cikin ƙissar Annabi Adam (Alaihis Salaam) game da umurnin a yi sujada ga Annabi Adam (Alaihis Salaam) Allaah Maɗaukakin Sarki ya ce:

فَسَجَدُوا إِلَّآ إِبْلِيسَ كَانَ مِنَ الْجِنِّ ، فَفَسَقَ عَنْ أَمْرِ رَبِّهِ

Sai dukkansu suka yi sujada, sai dai Iblis kaɗai, shi ya kasance daga aljani ne, don haka sai ya yi fasiƙanci game da umurnin Ubangijinsa

Watau: Sai Iblis (La’anahul Laah) ya kangare, ya fice daga bin wannan umurnin na Ubangijinsa, kangarewa irin na kafirci, kamar yadda ya zo a wata ayar:

فَسَجَدُوا إِلَّا إِبْلِيسَ أَبَى وَاسْتَكْبَرَ ، وَكَانَ مِنَ الْكَافِرِينَ

Sai duk suka yi sujada in ban da Iblis, ya ƙi kuma ya yi girman-kai, kuma ya kasance daga kafirai ne.

Amma ƙaramin fasiƙanci wanda bai kai girman babban fasiƙanci ba, shi kam ba ya fitar da mutum daga musulunci, kamar inda Allaah Taaala ya ke magana a kan waɗanda suka yi harama da aikin Hajji sai ya ce:

فَلَا رَفَثَ وَلَا فُسُوقَ وَلَا جِدَالَ فِي الْحَجِّ

To, babu batsa kuma babu fasiƙanci kuma babu jayayya a cikin Hajji

Haɗa kalmar fasiƙanci da batsa da jayayya da aka yi a nan ya nuna maanarta ita ce: Saɓo kawai, amma ba babban kafirci mai fitar da mutum daga musulunci ba.

Don haka, abin da ya ke wajibi a kan kowannenmu dai shi ne: Ya nisanci dukkan nau’ukan fasiƙanci babba da ƙarami domin neman samun tsira a Gobe Ƙiyama.

Allaah ya taimake mu.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi 

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments