𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum, dan Allah tambaya nake da ita
game da hadisin da ya ce Allah ya tsine ma namiji mai sa kayan mata da mace mai
sa kayan maza. To wai ko kaya ne unisex kika siya kika fara sa wa ‘ya mace, to
a gaba ko kin sake haihuwa sai ya kasance namiji ne ba za a sa masa ba, shin in
an yi haka tsinuwa na kan uwa? Sannan ita ma mace ba za ta sa kayan mijinta ba,
shin duk hukuncin haka yake?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa’alaikumus salam, wancan hadisi da Annabi ﷺ ya ke cewa: Allah ya tsine wa namiji mai
sa kayan mata, da kuma matar da take sa kayan maza, tabbas haka abin yake. Sai
dai abin yana buƙatar
tafseeli, wato rarrabewa:
1. Akwai kayan da suka keɓanci mata kaɗai, to waɗannan idan na miji ya yi amfani da su, shi
ne wanda wannan tsinuwa take kansa, misali abin wuya, awarwaro, takalmin mata
mai ƙwas-ƙwas, wando da riga da aka yi su don mata
kaɗai, hijabi da sauransu.
Duk namijin da ya sa waɗannan
ya shiga cikin wannan tsinuwa.
2. Akwai kayan da aka yi su don maza kaɗai, misali wando da riga na maza, kamar
kaftani ko babbar riga, ko hula, takalmi mai rufi na maza (cover shoe) da
sauransu. Duk macen da ta sa waɗannan ita
ma ta shiga tsinuwar Allah.
3. Akwai kayan da aka yi tarayya a tsakanin maza
da mata, kamar takalmi silifas, ko zobe na azurfa, yadin ƙyalle da za a siya a yanka a ɗinka, da sauransu, duka waɗannan maza da mata sun yi tarayya a ciki,
don haka idan mace ko namiji suka sa waɗannan ba wata tsinuwa a kan ko ɗaya, saboda kaya ne na tarayya.
Amma game da kayan miji kuwa, matuƙar kaya ne da suka keɓanta ga maza kawai, ba shi halasta matarsa
ta sa, saboda wancan hadisin da Annabi ﷺ ya ce Allah ya tsine wa namiji mai sanya kayan
mata, da mace mai sanya kayan maza.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.