Ticker

6/recent/ticker-posts

Ta Yi Allurar Zubar Da Ciki

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Ɗalibar makarantar koyon aikin asibiti ce ta yi wa wata matar aure allura wadda daga baya ta gano yana zubar da cikin da bai fi makonni uku ba, to shin wannan ɗalibar za ta yi kaffarar kisan kai kenan? Sannan kuma ga shi tana fama da ciwon ‘ulcer’, ba za ta iya yin azumi ba? A taimaka min da amsar wannan tambaya, menene mafita?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Wajibin da yake kan wannan ɗalibar da sauran ɗalibai irinta shi ne: Tun kafin ta yi wa mara-lafiya allura ta san wace irin larura ce, adadi nawa ya dace ta yi, kuma wace matsala ko ta’adi allurar ke haifarwa ga jiki? In da wannan ɗalibar ta ɗauki wannan matakin da farko to da wataƙila ba ta shiga wata damuwa ba, kuma da ba ta buƙatu ga yin wannan tambayar ba, in Shã Allahu.

Sannan sahihiyar magana a wurin Malamai ita ce: Ba a cewa mai zubar da ciki ta yi kisan-kai sai in ya kai lokacin da aka hura masa rai, watau idan cikin ya kai watanni huɗu. Amma abin da bai fi makonni uku ba wannan ba za a ce an yi kisan-kai ba, kodayake dai hakan ba abu ne da ya halatta ba a shari’a, sai in akwai wata larura mai ƙarfi.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments