Ticker

6/recent/ticker-posts

Idan Miji Yayi Amfani Da Matarsa Bai Shiga Gabanta Ba, Zasuyi Wankan Janaba?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Mlm tambayata ita ce: Idan miji ya yi amfani da matarsa ta cinyoyinta da matse-matsinta amma bai shiga cikin gabanta ba. Shi ya gamsu ta hakan amma ita babu abin da ta ji, kuma ba ta fitar da maniyyi ba, to wanka ya wajaba a kanta?

Allaah ya saka wa malam da alhairi.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Al-Imaam Muslim ya fitar da Hadisi cewa: Lokacin da aka saukar da wannan ayar:

وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْمَحِيضِ قُلْ هُوَ أَذًى ، فَاعْتَزِلُوا النِّسَاءَ فِي الْمَحِيضِ

Kuma suna tambayarka game da haila, ka ce: Shi ƙazanta ne! Sai ku nisanci mata a wurin haila (Surah Al-Baƙarah: 222).

Sai Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

اصْنَعُوا كُلَّ شَىْءٍ إِلاَّ النِّكَاح

Ku aikata dukkan komai, sai dai aure (saduwar jima’i) kawai.

Kuma Al-Bukhaariy da Muslim sun fitar da Hadisi daga Maimunah Bint Al-Haarith (Radiyal Laahu Anhaa) ta ce: 'Duk lokacin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yake buƙatar wani abu daga matarsa a halin tana haila, sai ya umurce ta ta ɗaura gyautonta (kamar sikel ko wandonta), sannan ya aikata duk abin da yake buƙata.

Malamai sun yarda cewa: Janaba tana samuwa ce ta hanyoyi uku, kamar haka:

1. Fitowar maniyyi ta hanyar saduwa a tsakanin namiji da mace.

2. Fitowar maniyyi a cikin barci ko a farke, kamar ta hanyar yin wasa da al’aura (istimnaa’i), ko amfani da ‘budurwar roba’.

3. Nutsewar kan al’aurar namiji a cikin na-mace a wurin saduwa, ko da kuwa maniyyi bai fita ba.

Don haka, idan miji ya yi amfani da wani sashen jikin matarsa, ba cikin farjinta ko duburarta ba, kuma idan har ya yi maniyyi da hakan, to ya yi janaba kuma sai ya yi wanka saboda haka.

Amma ita matar babu abin da ya same ta, matuƙar dai ba ta fitar da maniyyi ba.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GUƙ2GCCzlcdL6nknƙLYYox

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments