RANAR HAUSA TA DUNIYA, SHAWARI NA GAREMU HAUSAWA,

    Babu shakka wannan harshe na Hausa harshe ne mai ban shawara da sauki wajen koya,

    Harshe ne me daddadden tarihi musamman ta fiskacin kasuwanci da noma da kiwo, 

    Harshen Hausa ya mamayi harshina da daman gaske, ta yadda za kaga bayan ya mamayi harshinan arewa za ka iya samun Igbo ko Bayarbe sun zama hausawa, sun rikida,

    To dama ita Hausa ba kabila bace, Hausa kasa ce, yanzu de duk kabilan da ya iya magana da Hausa ya zama bahaushe,

    Abin takaici shine duk wannan martaba da daukaka na Hausa a duniya Hausa ba hashe ne na Ilimi wanda za kayi Degree ko Doctor ko professor bane, kuma duk manyan da Allah yayi mata masu mugun kirji dajin su Hausawa ne hankalinsu bai daidaita wajen yiwa Hausa gata ba, mumbar masanan da suka damu da hakan suna ta ihu tamkar a dajin da ake kira ihunka banza,

    Adabi yana neman bace mana, hakan ya jawo mana rashin wayewa da rashin kishin kasashemmu da y'an uwammu,

    Professor Bunza Allah ya kara masa lafiya da nisan kwana yana cewa da sanya karatun Hausa a Boko ya kai shekaru'120, yace a a kaf Africa babu harshe sama da Hausa, ya kara da cewa a harshinanan da muke dasu a duniya 7600 Hausa ce ta 11, 

    Gaskiya wannan babban koma baya ne ganin yadda Hausa bata iya sarrafa komai ko kera wani abu, alhali harshe ne da yayi hadaka da harshina masu fasahar gaske,

    Tarihin Hausa ya tabbatar mana da cewa ko bature bai iy mana da fasaha ko wayewa ba illa da yaudara,

    Sakin hakikanin al'adummu da harshe me ya jawo yanzu bamu iya kera komai saidai a kera mu saya, bamu da ingataccen magani sai mun fita waje, akwai harshina da yawa da basu kaimu ba amma yanzu harshinansu na Ilimi ne, akwai kasashen da suka zamanantar da abincinsu na hakuri da magungunansu na gargajiya daidai da zamaninsu kuma sun zauna lafiya,

    Mu kuwa mun saki abin cimmu da shammu da magungummu muna sayo masu chemical, daga ka haura shekaru 40 idonka ya fara rauni kaine ciwon suga kaine hawan cjini kadanne hanta Kaine koda,

    Iyayemmu sun fi mu karfi sun fi mu shekaru sun fimu karfin gani sunyi mana fintinkau,

    Wannan ita ce shawarata


    Kafar Intanet ÆŠin Da Za Ku Samu Dubbannin Rubuce-Rubuce Game Harshe Da Al'ada Da Adabin Hausawa

    Daga

    Yunusa Saminaka

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.