Ticker

6/recent/ticker-posts

Ranar Hausa ta Duniya - Sadaukarwa ga Abdulbaki Jari.

1.

 Ranar da muke tsumin ta,

 Ga ta nan a watan Ogusta,

Ashirin da shida ga wata,

 Ne bikin harshe na Hausa.

 

2.

Gun mu rana ce ta Sallah,

Ga Bahaushe duka zallah,

 Ya kamata mu roƙi Allah,

 Ya tsare harshe na Hausa.

 

3.

 Na sako Shakwara da Janfa,

 Hauwa ko ta sako Atamfa,

 Kwaliya sai ɗanmu Baffa,

Duk cikin shagali na Hausa.

 

4.

 Hausa harshe Hausa yare,

Hausa ta fi gaban mu ware,

 Hausa ta ci Gabas da zaure,

Yamma na ta biki na Hausa.

 

5.

 Ɓangaren Adabi akwai mu,

 Duk da al’adun garinmu,

 Har na gargajiya da ran mu,

 Mun riƙe harshen mu Hausa.

 

6.

 Waƙe-waƙe akwai na yara,

 Har da Tashe gun su yara,

Ga na 'yar tsana mun yi zarra,

 Duk muna yi mu a Hausa.

 

7.

Dariya a kiɗa akwai mu,

Dana Kowa har Mazan mu,

Makaɗan Fada ku ji mu,

Wanga su ne dai na Hausa.

 

8.

Laƙuban suna a bar mu,

 Talle Marka da Iro namu,

 Shakarau So-dangi ɗan mu,

 Har da Kyauta akwai a Hausa.

 

9.

Ga Ajuji Barau ubanmu,

 Naga Cindo Ayashe namu,

 Sa da Barmini Audi ɗan mu,

Har da Mairiga a Hausa.

 

10.

 Suturu waye ya kai mu?

 Dana mata har mazan mu,

 Adabi namu babu sammu,

Shi ya sa na karanci Hausa.

 

11.

 Rigunanmu akwai kaftani,

 Har da Aska Tara ku ji ni,

 Warki ka haɗa Tambuni,

Sace mai Adda a Hausa.

 

12.

Garke ciki har 'yar Shara,

 Aska Biyu har na yara,

 Sace mai Gafiya mu tara,

 Malum-malun a Hausa.

 

13.

Fanyama a wandunan mu,

Ɗan Itori Bulus cikin mu,

 Ɗantunis Kamufafai namu,

Kwarjalle Tsala a Hausa.

 

14.

Hulula ga Zanna ta mu,

 Ɗankwara da Kube a kan mu,

 Facima Bankwala gun mu,

Da Habar Kaba Zita Hausa.

 

15.

 Sambatsai rawanin ƙasar mu,

Gashin Jimina a kan mu,

Dangafafai Fade namu,

 Ɗan Maroko Huffi Hausa.

 

16.

 Zannuwan mu ciki da Saki,

 Ɗantofi da Gam ba raki,

Fatari da Mukuru ba ƙi,

 Tsamiya da Saro a Hausa.

 

17.

 Sana'o'i zo ka ɗauka,

 Noma Kiwo da Saƙa,

 Jima da Rini a harka,

Wanzaci sai a Hausa.

 

18.

Gun biki waye ya kai mu?

 Ga bikin sallar garin mu,

Haihuwa Aure a gun mu,

Har Kalankuwa duk a Hausa.

 

19.

 Ɓangaren suya akwai mu,

 Dankali Doya a ran mu,

Soya Waina sai garin mu,

 Har da Kifi da Nama Hausa.

 

20.

 Gun dafe-dafe wa ya fi mu,

 Ga Tuwo da Kunu a ba mu,

 Alkubus da Gurasa tamu,

 Alale Shinkafar Hausa.

 

21.

 Har abin sha duk gare mu,

Zoɓo Rodo Kunun Ayar mu,

 Ga Kunun Zaki a ran mu,

 Har da Dija duk a Hausa.

 

22.

 Cinye-cinye akwai gare mu,

 Dibilan Nakiya gun mu,

 Yin Kuli-kuli wa ya kai mu?

 Dakuwa Alkakin Hausa.

 

23.

 Hausa harshe Hausa yare,

Hausa ta fi gaban mu ware,

 Hausa ta ci Gabas da zaure,

Yamma na ta biki na Hausa.

 

24.

 Harshen da ya lashe saura,

Za ga duka ƙasa ka lura,

 Bar batun maganar asara,

Ɗaukaka ce gun mu Hausa.

 

25.

 Hamdulillah za na huta,

 Dole ne nai gaisuwata,

 Gun Rasulu abin biɗata,

 Da Sahabu da masu Hausa.

 

26.

 Ni Muhammadu ɗalibi ne,

 Ɗanbala mai son ku gane,

Can Borno cikin garin ne,

Ɗalibi nake ɗa ga Hausa.

 

27.

Unguwar Hausari can ne,

 'Yan Goro gidan Kaka ne,

 Nan nake da zama ku gane,

 Ni Bahaushe ne ɗan Hausa.

 

28.

 Ni na tsaro wanga waƙa,

 Ƙwar huɗu take babu shakka,

 Duk da kun san ba hazaƙa,

 Na yi don kishi ga Hausa.

 

29.

 Jumma’a ga wata na zauna,

Na rubuta 'yar uwana,

 Na yi ne don taya murna,

 Na zuwan rana ta Hausa.

 

30.

 Ran daren Ashirin da biyar,

 Ga watar Ogos na bayar,

 Ashirin da uku na kayar,

Da haɗin biyu uku Hausa.

Haƙƙin mallaka
Mohammed Bala Garba.
Ranar Hausa ta duniya.

www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments