Kari: Madid 7+5+7( -V- -/-V-/-V- -)
1.
Da sunan samamme Assamadu,
Assalamu wadda ya aiko Ahmadu,
Sa alihi sahabun Muhammadu,
Wanda na rike ba da wasa ba.
2.
Rabbi dafa na wake Hausa harshena,
Wadda nake fatan ka É—aukaka mana,
Shi a duk duniya har da nahiyana,
Afrika domin al’ummarmu mui gaba.
3.
Ba hankali a kin abin da ba sani ba,
Ba ka kushe abin da ba ka sani ba,
Ba ka yi rawar ido kan Hausa ba,
Ba ka san rashin sani da duhu ba?
4.
In ba ka sani ba zo a bayyana ma,
Harshe shi ne farko a halita ma,
Don da shi Adam ya yi magana ma,
Tun a farko ba ma a yau ko jiya ba.
Masani ya san harsuna duk É—aya,
Martaba kimarsu ma duka bai É—aya,
In ba ka sani ba sai kai hatsaniya,
KuÉ—in goro ake musu ba fargaba.
6.
Yanzu zan fara gabatar maka,
Da abin alfaharin uwa da kaka,
Mother tongue a turancin Amurka,
Hausa gatan maraya har mai uba.
7.
Na cikin harsunan Chadi ina ka ji,
Lalle da shi Afrika ke bugan kirji,
Na da duk ci gaba da duk ka’idoji,
Na rubutu ko balaga ga martaba.
8.
Ya mamaye duk Afrika ta yamma,
Saman kowanne harshen Naija ba gardama,
A Arewa É—aya tak da kowa ya kama,
Limami ne shi ko gun Yoruba.
9.
Ko mulkin mallaka ya yi ya bar sa,
Duk yawan kalmomin Larabci da nasa,
Na cikin gida na kuma asalinsa.
CuÉ—anya bai firgita martabarsa.
10.
Kai Malam! Harshen akwai wadata,
Na kalmominsa da kowa zai furta,
Ya aro, ya arar, ka san ya yalwata,
Ga shi da al’adu kowa ya zaÉ“a.
11.
Gafara mai zuma ya yi talla,
Mai maÉ—i ya koma fanin kalla,
In naka harshen ya mutu akalla,
To ai Hausa ita ba ta mutu ba.
12.
Sannunki Hausa ke kaÉ—ai sarauniya,
Harshen da ke da BBC, VOA, tun jiya,
Kai ga mu har da FM a cikin Nijeriya,
Akwai Hausa ko a fasahar Markzukaba
13.
Balle a google, ka dawo gida,
Akwai NTA har da AM ba raÉ—a,
Ga Freedom rediyo wurin faÉ—a,
Ba a raba Hausa da Hausawa ba.
14.
Hausa da Hausawa kusan abu É—aya ne,
Kamar da mutum da asalin sunansa ne,
Hausawa masu magana da Hausa ne,
Ya kuma gado ta tun ba ma bara ba.
15.
Harshe ne mai wadatattun sarakuna,
A Nijar, Mali, Togo, Libiya, Ghana,
Togo, Benin, Abijan, ga Borkina,
Bakar fata ba ai ya Bahaushe ba.
16.
Wajen watsuwa a dukkan yankuna,
Lungu da sako ga su a ko’ina,
Akwaisu a ko’ina har a Madina,
Balle a irin kano uwa-uba.
17.
Lalle akwai bambance-bambance,
Tsakanin Bahaushe da ma yai fice,
Ya kuma nazarci Hausa a karance,
To lalle in ba ka karanci Hausa ba.
18.
Kai É—an kallo ko rakiya ka zo ne?
To na rasa wane suna zan kira ka ne,
Mai zaman banza ko karan karofi ne?
In ba ka karanta ba ba ka samu ilmu ba.
19.
Ba ka san mene ne karin sauti ba,
Ba ka ma san ko da rausayar murya ba,
Ba ka ma san ko da rarrabewa zaɓi ba,
Ba ka ma san rukunonin aikatau ba.
20.
Ba ka ma san mene jigo a wakar ba,
Ba ka ma san fanonin adabinka ba,
Ba ka ma san asalin farkonka ba,
Ba ka san tarbiyar tatsuniya ba.
21.
Ba ka san 6+6 ba 12 ba ne ba,
Ba ka san zahafai da iloli ba,
Ba ka san walkiyar tauraro ba,
Ba ka ma san me nake bayani ba.
22.
Ba ka ma san ko al’adunka ba,
Ba ka ma san yin kasuwanci al’ada ba,
Ba ka ma san mene ne maita tsafi ba,
Ba ka ma san ko da surkulle ba.
23.
In dai ba ka gane mene ne Hausa ba,
Ba za ka san amfanin karanta ta ba,
Ba za ka san komai a cikinta ba,
Lalle mafurtanka suna shan azaba.
24.
Kamata ya yi ango ya san amaryarsa,
Malami ya fi kowa gane dalibansa,
Falke ya fi kowa sanin hanyarsa,
Kasance ba a fi Bahaushe Hausa ba.
25.
Karatun Hausa daban ne ga kowa,
Ya zama daban ga dalilai da yawa,
Linguistics, Adabi, al’adun Hausawa,
Kaso 3 nan babu in ba Hausa ba.
26.
Bature na yin Turanci a ko’ina,
Balarabe na yin Larabci a larduna,
Chinese na yin Chainanci a China,
Mu kowa sai kin Hausa me ya sababa?
27.
Ba bunkasa in ba aiki da shi ba,
Ba a technology in ba da shi ba,
Ba a development in ba da shi ba,
Ko an ki an so dole sai an sa shi gaba.
28.
Rashi na sanin asali da ciwo,
Rashi na sanin asali ya kawo,
Harshenmu ya kasa ya dawo,
Harshen kasa wadda zai mana jagaba.
29.
A duka hidimomi na rayuwa,
Mun yi sake harshenmu na cutuwa,
Mun sallamar da shi a ajamawa,
Su kuwa sun rike ba su gajiya ba.
30
Aliyu U. Yaro ne ya wallafa,
Baituka talatin daidai lissafa,
Mukalar Farfesa Bunza ta tallafa,
Tamat hamdi, Ubanjin Ka’aba.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.