Ticker

6/recent/ticker-posts

Prof. Khalid Abdullahi Zaria a Ranar Hausa ta Duniya, 2023

1. Duk Wanda Zai Rubuta Littafin Hausa, Ko Da Tarihin
ANNABI MUHAMMADU Ne, Ya Tanaji Kuɗin Bugawa, Don Duk Arewa Ba Mai Tallafa Masa!

2. Duk Wanda Ya Rungumi Aikin Wallafa Littafan Hausa A Matsayin Sana'ar Da Zai Ɗauki Ɗawainiyar Iyalinsa, Sai Gidansa Ya Fi Ƙarfinsa!

3. Ba Gwamna, Sanata Ko Minista Daga Arewa Da Ya San Wai Yau Ana Wani Bikin Ranar Hausa, Talakawa Ne Ke Barankadamarsu!

4. 50-Page-English-Book Maras Ma'ana Wajen Sarakuna Da 'Yan Boko Da Matasan Arewa Ya Fi Littafin Hausa Mai Shafi 500 Komai Ma'anarsa!

5. Sarakunan Arewa Da Na Haɗu Da Su, Ba Wanda Ya Taɓa Mutunta Littafan Hausa Da Nake Rubutawa, Sai Dai Su Tambaye Ni, Ina Na Turanci?

6. Ban Taɓa Ganin Bahaushe Ya Ƙaddamar Da Littafin Hausa ₦10,000,000 Ba. Na Ga Hausawa 5 Sun Ƙaddamar Da Na Turanci ₦500,000,000.

7. Yawaita Rubutu A Harshen Hausa Ne Laifin Da Mutum Zai Yi 'Yan Arewa Su Raina Shi Musamman Matasan Da Ke Bibiyar Social Media!

8. Musulmin Arewa Ne Suka Fi Raina Hausa, Domin Ko Da ƘUR'ANI Aka Fassara Da Hausa A Rubuce, Ba Zai Sa Su Mutunta Marubucin Ba!
Prof. Khalid Abdullahi Zaria a Ranar Hausa ta Duniya, 2023

Post a Comment

0 Comments