Ticker

6/recent/ticker-posts

Matsayin Karatun Sura A Cikin Sallah!

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum.  Allah ya kara wa malam lafiya da Nisan kwana, tambayata a kan sallar duha in za ka yi raka a huɗu huɗu kowanne sai ka karanta mata Fatiha da sura, ko biyu za ka yi wa Fatiha da sura biyun kuma fatiha kaɗai? Bissalam.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salámu. Sallar nafila takan bambanta da sallar farillah, duka raka'o'in sallar nafila ana iya karanta sura a cikin su, saboda dukkan sallolin nafila da aka kiyaye daga Manzon Allah an tabbatar yana karanta sura a cikin dukkan raka'o'in. Hatta ma a sallar Farillah ya tabbata cewa Manzon Allah a wasu lokutan yakan karanta sura a cikin raka'o'i biyun ƙarshe na a sallar Azuhur da La'asar a wasu lokutan, kamar yadda Muslim ya ruwaito a hadisi mai lamba ta: (452).

Abu Hurairata Allah ya ƙara masa yarda ya ce: "A cikin kowace sallah akwai ƙira'a, duk abin da Annabi ya jiyar da mu (na karatu) za mu jiyar da ku, abin da ya ɓoye mana kuma za mu ɓoye maku, duk wanda ya karanta Ummul Kitábi ta isar masa, amma wanda ya ƙara a kan haka shi ya fi". Muslim (396).

Imam Annawawiy ya ce: "Faɗin Abu Hurairata cewa wanda ya karanta Fatiha ta isar masa, wanda kuma ya ƙara a kan haka ya fi, to wannan dalili ne da ke nuna wajabcin karanta Fatiha, lallai abin da ba Fatiha ba ba ya isarwa a madadinta...".

Alminháj (4/105).

Asshaikh Ibn Uthaimeen ya ce: "Karatun Sura a bayan Fatiha Sunnah ne ba wajibi ba ne a bisa fahimtar mafi yawan malamai, saboda ba abin da ke wajaba sai karatun Fatiha".

Duba Assharhul Mumti'u (3/73).

Saboda lura da bayanan da suka gabata, idan mai sallar nafila ya karanta surori a bayan raka'o'inta, to hakan shi ne ya fi, idan kuma bai karanta surori ba, to sallarsa ta yi, amma ya bar abin da yake shi ne aula.

Allah Ta'ala ne mafi sanin daidai.

Jamilu Ibrahim, Zaria.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments