Abinda Ya Halatta Ga Namiji Yayin Da Matarsa Take Jinin Haila

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum, Mallam musulunci ya haramta asadu da mace tana cikin al'ada. tambaya anan shin ya halatta mace tayi wasa da mijinta har maniyyi ya futa? Cikin al'ada Ko kuma shi zaice mata tayi wasa da gabansa har maniyyi yafuta, meye hukuncin yin Hakan?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wabarakatuhu.

    Dukkan Maluman Musulunci suna ganin halaccin Mutum ya kwanta shimfida guda da Matarsa alokacin da take cikin jinin haila, har ma ya halatta su aikata komai irin nasu na Ma'aurata amma banda Jima'i.

    Suna kafa hujjah ne da hadisin Sayyiduna Anas bn Malik (ra) wanda yake cewa : "Yahudawa sun kasance idan Mace tana haila basu cin abinci tare da ita, kuma basu zaunawa waje guda da ita. Da Sahabban Manzon Allah suka tambayeshi game da haka sai Allah Mai girma da daukaka ya saukar da ayar nan ta cikin Suratul Baƙarah :

    وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْمَحِيضِ ۖ قُلْ هُوَ أَذًى فَاعْتَزِلُوا النِّسَاءَ فِي الْمَحِيضِ ۖ وَلَا تَقْرَبُوهُنَّ حَتَّىٰ يَطْهُرْنَ ۖ فَإِذَا تَطَهَّرْنَ فَأْتُوهُنَّ مِنْ حَيْثُ أَمَرَكُمُ اللَّهُ ۚ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ التَّوَّابِينَ وَيُحِبُّ الْمُتَطَهِّرِينَ

    Kuma suna tambayar ka game da haila Ka ce: Shi cũta ne. Sabõda haka ku nĩsanci mãta a cikin wurin haila kuma kada ku kusance su (wato kar kuyi jima'i dasu) sai sun yi tsarki (wato bayan daukewar jininsu kenan). To, idan sun yi wanka sai ku je musu daga inda Allah Ya umurce ku. Lalle ne Allah Yana son mãsu tũba kuma Yana son mãsu tsarkakewa. (Suratul Bakara 222)

    Sai Manzon Allah yace ma Sahabbansa "KU AIKATA KOMAI DASU IN BANDA JIMA'I". (Imamu Ahmad da Muslim ne suka ruwaitoshi).

    Masrouƙ bn Al-Ajda' yace "Na tambayi Nana A'ishah menene ya halatta ga Namiji alokacin da Matarsa take cikin haila? Sai tace "KOMAI DA KOMAI, IN BANDA FARJI". (Wato zai ita Mu'amala da dukkan Jikinta amma banda al'aurarta). (Imamul Bukhariy ne ya ruwaitoshi acikin Tareekh).

    Wato zata sanya Wani zani tayi Ƙunzugu dashi, ko kuma ta sanya Gajeren wando wanda zai rufe tun daga Ƙasan cibiyarta har zuwa gwiwarta, Sannan ta kwanta Shimfida guda da Mijinta.

    Akwai Hadithi daga Nana Maimunatu bintul Harith (ra) tace "Manzon Allah ya kasance idan yana nufin yin Mubashara da wata Mata daga cikin Matansa wacce take cikin Haila, yakan umurceta da tayi Ƙunzugu" (Bukhariy da Muslim ne suka ruwaitoshi).

    Don Ƙarin bayani aduba wadannan hadithan :

    Sahihul Bukhariy hadisi na 300-303.

    Sahihu Muslim hadisi na 293-294.

    Abu Dawud hadisi na 211, 269.

    Sannan aduba RISALATUL ƘAIRAWANIY babin dake magana akan haila. Sai kuma AL-FIƘHUL WADHIHU juzu'i na 1, shafi na 104-105.

    Sannan dangane da hukuncin fidda maniyyi ba tare da Jima'i ba, Malamai sun ce ya halatta Mace ta shafi al'aurar Mijinta har ya fitar da Maniyyi, ko kuma shi ya shafi al'aurarta har ta biya bukatarta. Amma idan mutum ya shafi tasa al'aurar da kansa har Maniyyi ya fita, to Wannan shi ne Istimna'i wanda mafiya yawan Maluman Musulunci suka ce Haramun ne.

    Amma idan mace tana cikin haila bai halatta mijinta ya shafi Farjinta ba, sai dai sauran sassan jikinta. (Kamar yadda aka faɗa cikin hadisan dake sama).

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/K7RkƘRMf2b57l3UENoJ1Or

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.