"Nijeriya da Nijar Daidai Suke" (Mamman Gawo Filinge)

    Jagora: 

    Bismillahi Rabbi Jallah ka kama muna, 

    Allah taimakam mu don

    girman Annabi, 

    Don WaÆ™ag ga tau da zan yi da wuya take, 

    Domin naga yan tawaye 

    ni ka zanzama , 

    Kun san kau zaman tawaye wada dush shike

    Komi kawwa Husaini dus sai kawa Hassan. 

     

    Y/Amshi:

    Tai da batun ka mai yabo

    Baban Bubakar, 

    Komi yayyi ma wuya a cikin duniya, 

    Kai ba duniya kaÉ—ai ba hamma lahira, 

    Komi zaka yi da sunan Allah kakai, 

    Allah kow kirayi suna nai ya jiya, 

    Komi yats tsananta, 

    Komi da wuya duka

    Kar roki Ubangijin mu Allah sauÆ™i shi kai. 

     

    Jagora:

    Ku dai dubi batun ga nau

    da kyau yara da nai maku, 

     

    Y/Amshi:

    Mun san gaskiya ta haƙiƙan ta kah hwaɗi

    Lalle na zaman tawaye da wuya shike, 

    Komi kaw wa Husaini dus sai kawa Hassan, 

    Ko mu mata garemu kishi haka nan shike,

    komi zaka bamu dus sai in ka raba shi daidai batu yayyi kyau, 

    Nijeriya, Nijeriya, Nijeriya da Nijar daidai suke. 

     

    Jagora:

    Amma ku bari ina hwaÉ—a maku komig gama, 

    Nijeriya da Nijar daidai duka, 

     

    Y/Amshi:

    WaÉ—an su waliyyai da Jallah yayyi cikin duniya, 

    Mamman Jabbu su da Usumanu Na Hodiyo

    sun sakko suna cikin yawon duniya, 

    Mamman Jabbu yats tsaye Sayi da martaba, 

    Shi kau Usumanu Shehu har Sakkwato can shike, 

    Amma duk cikin dare É—ai haÉ—uwa sukai suna hirad duniya, 

    RoÆ™on Allah sukai shi taimaki dud duniya musulmunci shi yawa, 

    Nijeriya, Nijeriya, Nijeriya da Nijar daidai suke. 

     

    Jagora:

    Mamman Jabbu su da Usumanu bin Fodiyooo

     

    Jagora/Y/Amshi:

    ÆŠiyan uba da uwa É—ai suke, 

    Y/Amshi:

    Allah ya haÉ—a mu tun hwarkon duniya, 

    Kowac ce zai raba mu mun san Æ™arya shi kai, 

    Nijeriya, Nijeriya, Nijeriya da Nijar daidai suke. 

     

    Jagora:

    Lalle yara dud da Ƙur'ani ya faÉ—i, 

    Innamal Muminina ihwantun, 

     

    Y/Amshi:

    Kulluhin musulmin dud duniya dangi na É—ai muke. 

     

    Jagora:

    Dan nan nij ji yan karin magana na faÉ—in abin da yat taÉ“a hanci duka idanu ta ruwa sukai, 

     

    Y/Amshi:

    Abin da yat taÉ“a Æ™woyar ido, 

    Lalle na ku tabbata hanci ji shi kai, 

    Abin da yat taÉ“a Nijeriya, 

    Lalle na kusan da ya taÉ“a Nijar duka. 

     

    Jagora:

    Don manyan Ƙasa sunan su biyu sun game, 

    Diori Hammani su da Janaral Yakubu Gawan. 

     

    Y/Amshi:

    Sun zamna wuri guda sun kayi shawara,

    Abin da ka duk Æ™ara arziki da zaman lahiya, 

    Nuhin Diori Hammani an nuhin Janaral Yakubu, 

    Su taimaki dud duniya a samu zaman lahiya, 

    Don haka ko da yaushe shirya mutane su kai. 

     

    Jagora:

    Ga zaman Diori Hammani ga zaman Janaral Yakubu. 

     

    Y/Amshi:

    Zaman Arsha da Diori yayi kyau da Mistoriya, 

    Mistoriya hwara matay Yakubu, 

    Zaman shi yi kyau kamaz zaman Diori da Aishatu, 

    Nijeriya, Nijeriya, Nijeriya da Nijar daidai suke. 

     

    Jagora:

    Nicce zarumin maza Janaral Yakubu, 

     

    Jagora/Y/Amshi:

    Mai birnatti mai libarbar mai bindiga, 

    ... wuta soji.. 

    Ga bambu ga igwala gun Yakubu, 

    ... wuta.. 

    Mai bistare da sisi sai Yakubu, 

     

    Jagora:

    Kai yan yara akwai wuta cikin hannun Yakubu, 

     

    Jagora /Y/Amshi:

    Ya hana tawaye har da É“allewa ya hana, 

    ... wane mutun! 

    Kuma ya bada ran shi don haÉ—a Nijeriya, 

    Allah ya taimakai Ƙasa dut ta game, 

    Nijeriya, Nijeriya, Nijeriya da Nijar daidai suke. 

     

    Jagora:

    Sannu da aikin shirin zaman jima'a Yakubu, 

    Sannu da aikin shirin Ƙasa Janaral Yakubu, 

    YaÆ™in nan da kayyi domin Nijeriya, 

    Ba don Nijeriyal É—ai ba kai wannan faÉ—a, 

     

    Y/Amshi: 

    Saboda Ƙasashen Afirka duk kai wannan hwaÉ—an, 

    Kowac ce za shi tawaye ko wata hwanÉ—ara, 

    Wada kaw wa Ojukku haka nan za ai mishi, 

    Ƙi gudu sa maza gudu Janaral Yakubu, 

    Ba mata ba ko maza na tsoron bone, 

    ... lalle.. 

    Nijeriya, Nijeriya, Nijeriya da Nijar daidai suke. 

     

    Jagora:

    Nicce zarumi maza Diori na Ai'shatu, 

     

    Jagora/Y/Amshi:

    Mai Kirno da Istalo Diori na Ai'shatu, 

    ... da alÆ™alami yab bi duniya.. 

     

    Y/Amshi:

    Mai fensiri da big Diori na Ai'shatu, 

    Akwai alÆ™alami ga Diori had da ruwan taddawa, 

    Dan ilmi da hankali da biyayya tasa, 

    Nijar mun yi zamne ba wani mai gardama, 

    Nijeriya, Nijeriya, Nijeriya da Nijar daidai suke. 

     

    Jagora:

    Bismillahi dum musulmi roƙo nikai,

    Don Rahamani nayi roÆ™o gun gwamnati, 

    Kuka na a sani jirgi in yo Haji, 

     

    Y/Amshi:

    Ka zo Makka ka zo Madina kai da abu yayi kyau, 

    Da mun ci bagaruwa da zam zam sai mun raga,

    Ka sai muna yan warwaro da yan sarkokin gabas, 

    Mu sa su muna takama muna ce maka Alhaji,

    Ka roÆ™am muna gahwara  mu bar Æ™una lahira, 

    Duz zunubammu Allah ka gahwarta muna, 

    Diori Hammani ar ruwa Yakubu Sabuni, 

    Kowa yag gama su daud'a tai ta zube,

    Nijeriya, Nijeriya, Nijeriya da Nijar daidai suke. 

     

    Jagora:

    Allahu ka taimaka dum manyan duniya, 

    Masu nufin lafiya ta sabka cikin duniya, 

    Masu nufin arjiki ya Æ™aru cikin duniya, 

     

    Jagora:

    Allahu shi taimaka ma Diori mijin Ai'shatu,

    Allahu shi taimaka ma Janaral Yakubu Gawan, 

    Allahu shi taimaka ma Soji mazan duniya, 

    Masu tsaron Ƙasa a samu zaman lahiya, 

    Kowacce zai raba mu soji ku duba muna, 

    Allahu shi taimake su don girman Annabi. 

     

    ... amin, amin, amin, amin...

     Daga Taskar

    Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
    ÆŠanmadamin Birnin Magaji
    Imel: birninbagaji4040@gmail.com
    Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.