Maganin Yaɗuwar Zina

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    As Salaam Alaikum. Malam, wai yaya za a yi maganin abin da ya zama ruwan-dare ne a yau na yaɗuwar zina a cikin al’ummarmu? Mu da muke aikin acaɓa ko ‘express’ da daddare mu ke ganin abubuwa. Malam, ban da ’yan mata da samari da aka saba ɗaukarsu, yanzu abin ya kai ga har manyan matan aure ma akwai wuraren da suke zuwa a cikin manyan motoci, a cikin duhun dare suna ɗaukar samari domin zuwa aikata ma sha’a!

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

    Allaah ya sauƙaƙe.

    Hanyar da za a iya bi domin maganin wannan matsalar da sauran matsaloli irinta ita ce:

    1. A yi ƙoƙarin kakkafa dokokin Shariar Musulunci da ɗabbaƙa su, watau da zartar da hukuncinsu a tsakanin jama’ar musulmi. Ma’ana: Duk waɗanda aka kama su da laifin zina daga cikin jama’ar musulmi sai kawai a zartar musu da hukuncin da Allaah Ta’aala ya yanke tun daga sama da saman bakwai:

    Idan ba su taɓa yin aure ba sai a yi ma kowanensu buloli guda ɗari, a gaban jama’ar musulmi, kuma ba tare da nuna tausayi gare su a cikin addinin Allaah ba.

    Idan kuwa sun taɓa yin aure sai a ƙara musu da jefewa da duwatsu har sai sun mutu.

    Wannan hanyar ita ta fi kyau kuma ta fi ƙarfi don maganin wannan matsalar.

    2. A lokacin da aka rasa, ko aka kasa zartar da wannan hukuncin, ba abin da ya rage sai a cigaba da jan kunne da gargaɗi ga masu aikata wa ta hanyoyi guda biyu:

    (i) A jawo ayoyi da hadisai sahihai masu razanarwa da tsoratarwa a kan wannan mummunan aikin.

    (ii) A jawo ayoyi da hadisai sahihai masu zaburarwa ga ɗaukar matakai don kare kai daga wannan aikin.

    3. Jawo hankalin wanda ko waɗanda suka faɗa cikin irin wannan aikin da hikima da kyakkyawan wa’azi, kamar yadda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi da saurayin da ya zo wurinsa da fatawar neman ya yi masa izini don ya je ya yi zina! Sai ya tambaye shi: Kana son a yi haka da mahaifiyarka ko ’yar uwarka ko ’yarka? Ya ce: A’a! Sai ya ce masa: To, haka sauran mutane ma ba su son hakan ga uwayensu ko ’yan uwansu ko ’ya’yansu. Daga nan sai ya yi masa addu’a.

    Ko kuma kamar yadda na ga wani ya feso a cikin WhatsApp wurin bayar da shawara ga matashi ko matashiyar da sha’awa ta yi musu ƙarfi cewa:

    Su riƙa ɗaukar abin da suke ji a jikkunansu kamar yadda suke ji ne a lokacin da suka gani ko suka ji ƙanshin wani kyakkyawan abincin da suke sha’awa alhali kuma suna ciki azumi. Me ke hana su yarda har su ɗanɗana wannan abincin? Dokokin da Allaah Ta’aala ya kafa ne ke zama musu kariya, ya hana su saɓawa. Kamar haka, wanda ya ji sha’awar zina sai ya tuna cewa dokar da Ubangiji ya kafa ce ta hana shi. Allaah Ta’aala ya ce:

     وَلْيَسْتَعْفِفِ الَّذِينَ لَا يَجْدُونَ نِكَاحاً حَتَّى يُغْنِيَهُمُ اللهُ مِنْ فَضْلِهِ

     Kuma waɗanda ba su samu damar yin aure ba sai su kame har sai Allaah ya yalwata musu daga falalarsa.

    Kuma Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

    يَا مَعْشَرَ الشَّبَابِ! مَنِ اسْتَطَاعَ مِنْكُمُ الْبَاءَةَ فَلْيَتَزَوَّجْ، فَإِنَّهُ أَغَضُّ لِلْبَصَرِ وَأَحْصَنُ لِلْفَرْجِ، وَمَنْ لَمْ يَسْتَطِعِ فَعَلَيْهِ بَالصَّومِ، فِإِنَّهُ لَهُ وِجَاءٌ

    Ya ku samari! Daga cikinku duk wanda yake da damar ɗaukar nauyin ɗawainiyar aure to ya yi auren, domin shi ne zai tsare idanunsa kuma ya kange al’aurarsa; wanda kuma ba zai iya ba sai ya kama azumi, domin shi kamar dandaƙa ce gare shi.

    Allaah ya kiyaye, Allaah ya ƙara tsare mu daga dukkan hanyoyin hallaka.

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfƙds

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.