Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Matar Da Tayi Ma Mijinta Tsafi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Malam da fatan ka sauka lfy. wata cousin dina ce wallahi suka samu matsala da mijinta. sai taje gurin wani malami, sai yace suje a zuƙo jinin jikinta ya haɗa musu magani dashi. ta dinga zuba mai a abinci ko tayi abincin dashi. malam ba wanda ya faɗa min, sai ji nayi. shin yaya abin yake? JAZAKALLAH BIKAIR.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Hakika waɗannan sun aikata kuskure babba. Daga cikin manyan kusakuren nasu akwai

1. Zuwa wajen boka da sukayi :

Hadithi daga Sayyiduna Imrana bn Husayn (rta) yace Manzon Allah yace : "BA YA TARE DAMU DUK WANDA YAYI CHAMPI KO AKAYI MASA CHAMPI DOMINSA. KO KUMA YAYI BOKANCI KO AKAYI BOKANCI DOMINSA, KO YAYI SIHIRI KO AKAYI SIHIRIN DOMINSA. WANDA YAJE WAJEN BOKA KUMA YA GASKATASHI CIKIN ABINDA YAKE FAƊA, TO HAKIKA YA KAFIRCE MA ABINDA ANNABI MUHAMMADU YAZO DASHI". (Imamul Bazzar ne ya ruwaitoshi).

To kinga su sun gaskatashi har sunje sun kawo masa jinin da aka haɗa tsafin dashi.

2. Ciyar da Musulmi najasa da gangan : Wannan ba Ƙaramin Kaba'irah bane. Duk wanda ya Ciyar da musulmi najasa to hakika ya zalunceshi. Kuma Allah zai saka masa.

3. Tsafi domin mallakar Miji : Hakika shi bokan da yayi tsafin nan ya kafirta. Haka kuma duk wacce tasa akayi tsafin itama zata kafirta. Haka itama 'Yar uwar taki da ta zuba ma Mijinta wannan abun don neman mallakar zuciyarsa.

Ki gaya musu cewa lallai sun aikata babban laifi na shirka da kafirci. Su gaggauta tuba su dawo hanyar Musulunci.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments