Duk Wanda Zaiyi Rantsuwa To Ya Rantse Da Allah Ko Kuma Yayi Shiru

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh Malam don Allah wani al'amari ne ya shige min duhu, menene hukuncin yin rantsuwa da wani malami kamar yanda naji wani abokina yana cewa wai ya rantse da shehu?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumussalam warahmatullah wabarakatuh, to ɗan uwa magana ta gaskiya yin rantsuwa da wani mutum ko waye shi wanda ba Allah ba haramunne kuma ketare iyaka ne bai halatta ba.

    Hadisin Abu-Ubaidah daga Jabir ɗan Zaydin daga Ibn Abbas Allah ya kara masu yarda daga Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi ya ce: "DUK WANDA YA KASANCE DAGA CIKIN KU ZAIYI RANTSUWA TO YA RANTSE DA ALLAH, KO KUMA YAYI SHIRU"   duba JAMI'US-SAHIH NA ABU-UBAIDAH 654

    Akwai hadisi daga Abu-Sa'eed Alkhudriy Allah ya kara masa yarda yace, Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi ya riski Umar Bin Khaddab yana rantsuwa da iyayensa sai Annabi ya ce: "ALLAH YA HARAMTA MAKU RANTSUWA DA IYAYEN KU HAR ZUWA RANAR TASHIN ALƘIYAMAH, DUK WANDA ZAIYI RANTSUWA TO YA RANTSE DA ALLAH KO YAYI SHIRU"  duba acikin JAMI'US-SAHIH na ABU-UBAIDAH 655

    Don haka dai bai halatta ba ka rantse da wani malami ko wanene shi, idan kuma kayi girman kai wajen rashin bin Umurnin Ubangijin ka to kasani zaka wayi gari cikin fasikai, daga karshe sai Allah yayi maka hukunci, kuma lallai mai gafarta zunubbai ne kuma mai karban tuba, kuma mai tsananin azaba, Allah ya tsare mu, Allah yasa mudac.🤲

    WALLAHU A'ALAM.

    ✍️Hussaini Haruna Ibn Taimiyyah Kuriga

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.