Ticker

6/recent/ticker-posts

Kalmomin Da Ba Su Da Bambanci A Rubutun Yau Da Kullum Amma Ma'anoninsu Sun Bambanta

BABA - Mahaifi

BABA - Mahaifiya

BABA - Gaye 

BABA - Wajen Rini


KARA - Na Itace 🌱

KARA - Ta Ganin Girma 

KARA - Na Waƙa


GADO - Na Magada 💰 

GADO - Na Kwanciya 

GADO - Tsuntsu 🐦


FARI - Na Launi 

FARI - Na Ƙwari 

FARI- Na Farawa 1st 

FARI - Na Ƙiƙƙifta Ido 👀 

FARI - Na Rashin Ruwan Sama. 


WUYA - Na Jikin Mutum 

WUYA - Ta wahala 


KUKA - Na Hawaye 😢 

KUKA - Ta Miya 


KAI - Na kai Da ake magana dakai 

KAI - Na Jikin Mutum 


KYAUTA - Na Sunan Mutum 

KYAUTA - Na Girmama Mutum 


BAYA - Na Bayan Mutum 

BAYA - Na Ƙarshe 🔚


DOKI - Na Dabba 🐴 

DOKI - Na Ƙofar Ɗaki


YAJI - Na Abinci 

YAJI - Na Ƙauracewa Gidan Miji

YA JI - Na Sauraro 


SHAYI - Na Kaciya

SHAYI - Na Abinci 🍵 

SHAYI - Na Tsoro


KALA - Na Launi 

KALA - Na Nema (Roqo) 


KASHI - Na Turoso (Ba Haya) 

KASHI - Kaso (Rabo, Adadi) 

KASHI - Na Duka 💪👊


TIRMI - Na Atamfa 

TIRMI - Na Daka 


HAUSHI - Na Fushi 

HAUSHI - Na Kukan Kare 🐶 


ADO - Sunan Mutum 

ADO - Kwalliya 


GWANDA - Ta Itace 

GWAN DA - Ta Zaɓi 


BAIWA- Ta Basira/Karama

BAIWA - Ta Bayi


Gora - ta itace/dukan mai laifi.

Gora - ta masunta


Yaya - Babban dan uwa Namiji

Yaya - Babbar 'yar uwa mace.

Yaya - Tambayar yanayi


Riga - Ta tufafi

Riga - Na tserewa 


Kaza - Tsuntsun gida

Kaza - Na abinda ba'a ambata sunansa ba


Kora - Farin abu da yake fitowa akan kazami

Kora - Firtima


Gada - Ta tsallake ruwa/Rami

Gada - Dabbar daji mai kama da Akuya


Gari - Na abinci

Gari - Birni/kauye


Lami - Sunan mace

Lami - Yanayin d'and'ano


Fata - Buri

Fata - Shimfid'ar da ta lullube jikin mutum/dabba


Wuri - Na kud'i a da

Wuri - Waje


Bori - Harkar matsafa

Bori - Birgima/Bijirewa

Bori -  Boring gyaɗa


Tafi - Had'a hannaye wuri d'aya su bada sauti

Tafi - Mari

Tafi - Umurni na tafiya


Kafa - K'ofa/hanya

Kafa - Dasa (Kafa itacen nan)


Jingina - Ajiye wani abu dan karbar bashi

Jingina - Jinginu da jikin wani abu


Bashi - Wari

Bashi - Karbar kudi ko madadinsa aro

Bashi - Umurnin bayarwa ga jinsin Namij. 


Kafar Intanet Ɗin Da Za Ku Samu Dubbannin Rubuce-Rubuce Game Harshe Da Al'ada Da Adabin Hausawa

Post a Comment

0 Comments