Ticker

6/recent/ticker-posts

Ai Ba Yau Aka Fara Rarara Ba A Ƙasar Hausa!

Allah gafarta Malam, na sha yi wa wasu ɗaidaikun mutane bayani dangane da samuwa da bunƙasar waƙoƙin siyasar jam'iyya a Nijeriya musamman dangane da abin da ya shafi zambo/zagi.

Mutane da dama sun ɗauka cewa Rarara ne ya fara yin zambo ko kuma abin da suka kira shi da zagi ko cin mutuncin abokan hamayya, inda nake nuna masu cewa ko kusa ba haka abin yake ba. Kusan ma idan an kira Rarara da tattaɓa-kunne ba ma jika ba a wannan fagen to ba a yi kuskure ba.

An yi mawaƙa da dama na siyasa waɗanda a zamaninsu ba su bar 'yan adawa sun sha ruwa ba. Kodayake, yawanci a wancan zamanin mawaƙan 'yan adawa ne suka fi kausasa harshe a cikin waƙoƙin nasu, watakila ko don su huce haushinsu ne kan abin da suke ganin cewa zalunci ne da danne haƙƙi wanda masu mulki ke yi masu.

Misali, an samu mawaƙa irin su Malam Sa'adu Zungur da suka zamo tamkar garkuwa ga talakawa, inda suka riƙa kai hari da harshe da kuma alƙalaminsu wajen faɗa da danniya da zaluncin masu mulki. Kamar yadda ya ce:

 

"A yau mun ɗauki makamanmu,

Na kisan zaluluncin masu gari.

 

Harshe shi ne kansakali,

Mashi kuwa alƙalami nagari."

 

Haka kuma a wani wurin ya yi zambo ga wasu shugabannin siyasar lokacin, inda ya ce:

 

"Wani ya yi tsawonsa, tsawon banza,

Sai gulma da dogon azzakari.

 

Wani ya yi gajarta yai tumbi,

Yai taiɓa, yai gurun kuturi.

 

Ɗan Dada Ajuji maras kunya,

Da bazarta take yawo a gari.

Duk idan aka dubi waɗannan baitocin za a ga cewa kalmomi ne masu zafi ga 'yan adawar wancan lokacin. Domin kuwa an kai ga duk wanda aka kama shi da kwafin wannan waƙar kai tsaye za a wuce da shi gidan kurkuku.

Wasu daga cikin waɗanda suka yi ire-iren waɗannan waƙoƙin a wancan lokaci akwai Malam Gambo Hawaja da waƙarsa ta "'Yan Sawaba". Inda ya yi wa masu mulkin wancan lokacin biji-biji da alƙalaminsa. Da kuma irin su Malam Auwal Isa Bungudu daga baya dai sauran su.

Abin da ya kamata a fahimta shi ne, ba yau aka fara samun 'Rarara' a fagen waƙoƙin siyasar Nijeriya ba. Kuma abubuwan da ake ji a cikin waƙoƙin na 'Rarara' ba yau aka fara faɗar su ga 'yan adawa ba. Kawai abin za a a iya cewa shi ne, kowane zamani da irin salon da yake zuwa da shi. Kuma ko ma dai mene ne, inda saniyar gaba ta sha ruwa, nan ta baya take tsoma bakinta.


Kafar Intanet Ɗin Da Za Ku Samu Dubbannin Rubuce-Rubuce Game Harshe Da Al'ada Da Adabin Hausawa

Daga Jibril Yusuf Dokan Lere 

Post a Comment

0 Comments