Ticker

6/recent/ticker-posts

Al’adar Mai Tsarin Iyali

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Na yi tsarin iyali ne. Sai a watan farko na ga al’adata, a wata na biyu kuma ban yi ba. Daga baya kuma sai ga jini har kwanaki huɗu, to yaya matsayin sallah da azumi?

Ni matar aure ce, ina yin haila kwana shida. Amma da na haihu kuma na je aka yi mini tsarin iyali, sai jinin ya koma kwanaki ashirin! To zan iya cigaba da ibada da mu’amalar aure ko sai bayan jinin ya ɗauke?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Gudun aukuwar irin waɗannan matsalolin ya sa malamai suka ƙyamaci bin irin waɗannan hanyoyin na zamani don tsarin iyali in dai ba da wata larura mai ƙarfi ba, kamar yadda muka yi bayani a cikin amsar tambayar da ta gabata akan kayyade haihuwa.

Amma a kan wannan matsalar sai a ce: Jinin da ke fitowa ga mata nau’i uku ne: Haila da Nifasi da Istihaala.

(1) Haila jinin da ya zo ne haka nan kawai ba da wani dalili na rashin lafiya ba, sannan kuma da kansa yake fitowa a lokacinsa, ba janyo shi ake yi ba.

(2) Nifasi kuwa shi ne wanda ya zo saboda dalilin haihuwa.

(3) Istihaala kuwa shi ne wanda ya auku saboda rashin lafiya, ko jin ciwo a cikin wata jijiyar mahaifa, da sani ko ba da sanin macen ba.

Don haka, duk jinin da aka tabbatar ba haila ba ne kuma ba nifasi ba ne, to babu abin da ya rage sai dai a ba shi matsayin istihaala kawai.

Istihaala dai ba ya hana abubuwan da haila da Nifasi suke hanawa na sallah da azumi da mu’amalar tarayya a tsakanin ma’aurata.

Allaah ya ƙara mana fahimta.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Cnf26Ƙ8MPƙz9yUYU1nxƙRƙ

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments