Jarrabawa wata hanya ce ta gwada fahimtar dalibi ko aunata; domin fitar da sakamakon karshe da yanke hukumci a kai.
Yawancin dalibai basu da wata damuwa da ta wuce jarrabawa,
musamman ma a matakan karatu na gaba da sakandire. Tsananin tsoron jarrabawa da
rashin sanin dabarun rubutata yana jefa dalibai cikin zulumi da razani. A kasa,
za a baiyana kadan daga cikin dabarun cin jarrabawa kamar haka:
1- NAZARI TUN FARKON ZANGON KARATU: dalibi ya tsarawa kansa
lokutan nazari tun farkon zangon karatu, wannan zai taimaka masa wajen fahimtar
darasi da lakantarsa.
2- SAMUN ISASSHEN (CA): CA ya kunshi: (attendance,
assignments and tests). Samun isasshen (continues assessment) yana taimaka wa
dalibi wajen cin jarrabawa cikin sauki, rashinsa kuma (kai tsaye) yana haifar
da faduwa a jarrabawa. Saboda haka, ya kamata dalibi ya tabbatar da ya rubuta
aiyukan da aka ba shi, ya kuma rubuta (test), tare da samu isasshen
(attendance) .
3- KIRKIRAR TAMBAYOYI: dalibi ya dauki kansa a matsayin shi
ne malami, sai ya kirkiri tambayoyi, ya kuma amsa su da kansa, hakan yana
taimakawa matuka, a wasu lokutan akan dace da tambayoyi masu kama da juna,
tsakanin malami da dalibi.
4- BIBIYAR TAMBAYOYIN BAYA: wannan wata dabara ce da dalibai
suke bi, domin gano salon malami a jarrabawa, kuma yau da gobe sun tabbatar da
ingancin wannan dabara, tare da tasirinta a cin jarrabawa.
5- SHIGA DAKIN JARRABAWA A KAN LOKACI: ana so dalibi ya
shiga dakin jarrabawa kafin lokaci ya yi da minti talatin, wannan zai ba shi
damar samun nutsuwa da daidaituwar tunani kafin fara rubutu. Shiga dakin
jarrabawa a makare dalili ne mai girma da yake haddasa rudewa da jinkirin zuwan
tunani mai kyau a lokacin bukata.
6- CIKE BAYANAI KAFIN KOMAI: wannan shine abu mafi
muhimmanci a lokacin jarrabawa. Ana so ka tabbatar da ka cike bayanaka dai-dai,
kamar lambarka, ajinka, zangon karatu, kod din kwas, sunan kwas, da lokacin
jarraba. Rashin cike wadannan bayanai zai iya zama sila ko dalilin faduwa a
jarraba.
7- KARANTA INSTRUCTIONS: wannan zai baka damar fahimtar
adadin tambayoyin da ake bukatar ka amsa, sannan yana nuna kwarewa da
tsantsenin dalibi.
8- KYAKKYAWAN RUBUTU:
yana taimakawa wajen fito da fahimtar dalibi ga malami. Da akwai malaman
da basu wahalar da kansu wajen karanta jagwalgwalo, wani rubutun zaka ganshi
kamar rubutun-sha.
9-NUTSUWA: a lokacin da dalibi ya shiga dakin jarraba, ya
kamata ya tattara hankalinsa waje guda, ya nutsu. Akwai daliban da suke shiga
halin firgici da zarar sun shiga dakin jarrabawa, daga karshe sai wannan
matsalar ta sa su kasa fahimtar tambaya.
10- FAHIMTAR TAMBAYA KAFIN RUBUTA AMSA: dalibi ya tabbatar
ya karanta dukkanin tambayoyin da a ka yi masa, kafin ya fara rubuta amsa.
Misali, da akwai tambayoyin da a ke bukatar dogon bayani, da akwai kuma wadanda
ake bukatar gajeren bayani. Wasu tambayoyin ana bukatar ambaton wani abu wasu
kuma ana bukatar sharhi da tahlili. Idan aka nemi dalibi ya kwatanta abu biyu
ko sama da biyu, toh ana nufin ya ambaci fuskokin kamanceceniya da hannun riga
a tsakaninsu.
11- FARA AMSA TAMBAYAR DA KA FAHIMTA: ba dole sai ka amsa
tambayoyi a jere ba, aa, ka fara amsa tambayar da ka fi fahimta, wannan zai
baka damar saita lokaci, da kuma hararo tunani da wuri.
12- DOGARO DA KAI A LOKACIN BAYANI: yawancin malamai sun fi
bukatar dalibi ya yi amfani da kwarewa da fahimtarsa a lokutan bayani, wannan
yana karawa dalibi daraja da kima, fiye da dalibin da ya ke dogaro da hadda
kawai.
13- BITAR AMSOSHI: dalibi ya tabbatar ya yi bitar dukkanin
amsoshin da ya rubuta, domin tabbatar da ingancinsu. A wasu lokutan ana samun
gyaran tunani, karin bayani, goge wani abu ko kuma soke tunani baki daya.
Rashin bitar amsoshi yana wanzar da kuskuren dalibi, daga karshe ya samu ragin
maki ko kuma faduwa a jarrabawa.
14- JINKIRI KAFIN FITA: akwai dalibai masu gaggawar fita
daga dakin jarrabawa, watakila domin burga ko kuma nuna iyawa, daga karshe ana
iya samunsu da sakamako mai rauni. Wannan yana tabbatar da muhimmancin bitar
amsoshi da tabbatar da su.
15- RUBUTA ATTENDANCE: kafin ka fita daga dakin jarrabawa,
ka tabbatar ka rubuta (attendance) guda biyu (in and out); rashin rubuta shi ya
na janyo wa dalibi matsala a lokacin da bai yi zato ba.
16- ADDU'A: makami ce mai girma a cikin dukkanin lamuranka
na rayuwa. Ana yin addu'ah ne bayan an zuba kokari da himma.
Kowa da irin kwakwalwarsa, kuma kowace kwakwalwa akwai makin
da za ta iya É—auka duk
dagewarta.
Allah Ya ba mu sa a amin.
Daga
Comrade
Abubakar Sarki ASUK
03-08-2023.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.