Ticker

6/recent/ticker-posts

Dawa Da Shinkafa/Shinkahwa a Gonar Fadama

Dawa Da Shinkafa/Shinkahwa a Gonar Fadama

Dawa Da Shinkafa/Shinkahwa a Gonar Fadama
Wannan gona ce ta fadama a anda aka shuka dawa da shinkahwa/shinkafa, tsarin wannan shukan dawa shi ake kira da suna Santa, akan tsallake kuyya kaman biyar ko shidda sai asaka shinkahwa a tsakiya, domin tasamu cikaken iska, awajen wannan kalan shukan Dawa akan shukata ne da Wani salo da muke kira da sunan sanbiya, shi wannan tsarin na shukan sanbiya duk wanda ya jure ya yi irinsa idan ma a ce duka gonar babu shinkahwa ba wake ba komai sai abin da ya zaɓi ya shuka kaman Dawa ko Gero, to zai saka ka ga sun tashi da kauri da kyau sosai. Ba kowace kalan Dawa ke iya rayuwa a inda shinkahwa ke rayuwa ba. Dawar da ake kira Takambo ta fi kowace kalan Dawa juriyar sanyi da ruwa ko da akan samu gonar mai ajiye ruwa ce da yake an fi shuka shinkahwa a inda wadatar ruwa suke ko wadataccen sanyi.

Dawar da muke kira da suna Takambo, amman taƙorumbo na iya jurewa, da hwara/fara Dawa da ƙyarma, amman Takambo ita ce mafi dacewa,  Dawa Takambo ita ce dawa mai al'adar ƙosawa a lokaci guda da  maiwa, ita ma wata nau'in gero ne mai nuna daga baya.

Daga Taskar

Mai Girma Sarkin Rafin Gobir
Mai Girma Isma'il Muhammad Yusuf


Post a Comment

0 Comments