Cigaba da Tattaunawa a Zauren Hikima Game da Asalin Hausawa

    ...

    Malam Adamu I.A.

    Maganar kawo tsarin mulki a Kasashen Hausa kam da gyara. Ai da yake duk an aminta da cewa ya sami daɗaɗɗen gidan Sarauta a Daura kuma Sarauniyar Ƙasar ce ya aura har ta haifa masa ƴaƴa ba za a ce duk Sarakunan da suka gabace shi ba su da tsarin mulki ba. Haka ma yana da wuya a ce ya aika da ɗiyan sa su je Gobir, Katsina, Kano da sauran Daulolin Hausa su zama Sarakuna da yake waɗannan Dauloli ba a ƙarƙashin mulkin Daura suke ba. Farkon Daular Katsina a Kusheyi (Maƙabartu/Maƙabarta) a ka fara ta tun kafin zuwan Muhammadu Korau. Ka gani ko ba cikin zuriyar sa ne suka fara mulki a Durɓi ta Maƙabartu/Kusheyi ba

    Malam Musa Ibrahim Daura

    Salam, to muna kallon duk rubuce-rubucen da akeyi akan wannan tarihi daya shafe mu kai, tsaye, masu karyatawa da masu goyon baya .

    Da farko dai shi farfesa hambali yana da damar ya karyata ko wane irin tarihi matukar ba al-kur'ani ko sahihan hadisai ya karya ba, bare ace yayi ridda.

    Haka nima, ko wani muna iya karyata duk wata magana da farfesa hambali zai fada matukar ba ayar Allah bace ko hadisi manzon tsira ya fadi ba.

    Abu na biyu tun kafin farfesa hambali ya shiga makaranta ko yazo duniya aka rubuta tarihin bayajidda zuwan sa da abubuwan da suka wakana, kuma an samu manazarta da suka zarta farfesa hambali Amma basu karyata labarin ba, domin akwai abubuwan da ake lura dasu kafin karyatawa ko gaskata tarihi, Wanda na tabbata manazartan da suka gabaci Farfesa hambali sun kalli wadannan abubuwa 

    Abu na uku kamar yadda na fada cewa kowa na iya karyata labari to nima ban yarda cewa farfesa hambali ya fadawa sarki Bashar wannan magana ta cewa su daina danganta kansu da bayajidda ba, idan kuma har anyi haka to a kawo Mana hujja ta hoto mai magana.

    Abu na hudu, farfaesa hambali da masu karyata labarin bayajidda suna iyayi don neman suna da daukaka kamar yadda yanzu gaya ana fadin su.

    Abu na biyar shin wai don tarihin nan ya biyo ta kan Daura ne ake inkarin sa ko kuma mi?

    Abu na karshe tunda ba fagen bayani ne na shiga ba, shi tarihi dole ana samun inda ya mike da Kuma inda ya lankwashe, don haka ba'a karyata shi saidai mutum ya fadi abin daya fahimta a cikin sa.

    Dr. Adamu Rabi'u Bakura

    Shi lamarin ilimi da ƙoƙarin bincike abu ne da yake buƙatar kayan binciken shi kansa da kuma samun sukunin gudanarwa. Zuwan Turawan 'yan leƙen asiri da na Mulkin Mallaka, sun gurɓata tarihin Hausawa da ƙasar Hausa. Misali, Turawa 'yan mulkin mallaka sun nuna cewa Hausawa ba su da adabin zamani kafin mulkin mallaka, in aka cire rubutattun waƙoƙin Hausa duk da cewar akwai hanyoyin rubutu da suka danganci larabci da ajamin Hausa. Masana ilimin na farko sun tafi akan haka. Har ma suka kafa hujja da cewa, ba a rubutattun ƙagaggen labari cikin sigar ajami. Saboda shi ɗan halas ne na Larabci. A daidai wancan zamani, duniya ba ta zama kusa ba. Sai lamurran suka sauya, aka tabbatar da wanzuwar adabin zamani a ƙasar Hausa tun kafin cuɗanyar Hausawa da dangogin Turawa. Irin wannan ne ke gudana. Idan aka duba rubuce-rubucen masu jahadi dangane da ƙasar Hausa, shi ma akwai masu hangen akwai tsambare a ciki. Ka duba "Sabon Tarihin Asalin Hausawa". da"Tarihin Wanzuwa Da Asalin Hausawa", da "Hausa Bakwai: Kunne Ya Girmi Kaka", da "Taƙaitaccen Tarihin Daulolin Ƙasar Hausa Da Maƙwabtansu Kashi Na Ɗaya", da kuma "Asalin Hausawa". In ka ratsa waɗannan za ka sha mamaki. Shi lamarin tarihin ƙasar Hausa sai an koma ga bayanan da magabata suka zayyana a cikin harshen Larabci tun zamanin su Abdullahi Sika, don tantance sahihanvci yadda abun ya kasance. Don haka maganar ƙaryata bayanin da wani ya kawo ko rashin ƙaryatawa bai taso ba. Domin kowane masani da abin da Allah ya fahimtar da shi ya ke amfani, a kuma cikin zamanin da ya sami kansa. Allah ya sa mu dace. Ya kuma arzuta mu da cikawa da imani. Amin.


    Kafar Intanet ÆŠin Da Za Ku Samu Dubbannin Rubuce-Rubuce Game Harshe Da Al'ada Da Adabin Hausawa

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.