Ticker

6/recent/ticker-posts

Ciki da Hanyoyin Tanadinsa a Tsakanin Hausawa a Yau

This article is published in Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies, No. 5 Vol. 1 September, 2008, Department of Nigerian Languages, Bayero University, Kano, Page 163 – 181

Ciki da Hanyoyin Tanadinsa a Tsakanin Hausawa a Yau
English Rendition as “Pregnancy and Prenatal Care among Hausa People Today”

Bashir Aliyu Sallau
Department of Nigerian Languages
Katsina State University
Katsina - Nigeria

Abstract

Birth or child bearing is an important aspect of life which almost all communities of this world give special preference.This is the reason that made such communities to plan for it right from the time a woman is conceived. Different communities have different ways of taking care of their mothers-to-be or in other words prenatal care. Prenatal care is given to pregnant women in order to look after their health and that of the unborn child in their womb so that they will come to this world as healthy individuals. This article focuses attention on the traditional as well as the modern health care delivery administered to pregnant women in Hausaland. There is an introductory aspect in which prenatal care  has been defined and a short history of whom are regarded as the Hausa people was also given.The article contains two important sections.The first part deals with the traditional ways and manner a pregnant woman is identified and the traditional prenatal care given to her by the Hausa people. The second segment discusses on the modern ways of identifying a pregnant woman through urine test and preganancy ultrasound scanning. Further more modern prenatal care as administered in clinics and hospitals and the impact they made on the traditional prenatal care has also been analaysed. 

1. 0 Gabatarwa

Ciki ko juna-biyu ko ɓatan-wata kalmomi ne waɗanda Hausawa suke amfani da su don bayyana wani hali da mata kan shiga a sakamakon saduwarsu da namiji. A al’adar Hausawa da kuma a kimiyance an bayyana cewa daga shigar ciki ana ɗaukar tsawon wata tara kafin a haife shi, amma kuma a wasu lokuta saboda wasu dalilai akan haihu ƙasa da wata tara ko sama da haka.

Haihuwa hanya ce wadda ake samun ƙaruwar al’umma, wannan dalili ne ya sa kowace al’umma a wannan duniya take alfahari da ita. A saboda haka ne Hausawa suke son yawan haihuwa, kuma ba sa gajiya da ita kome yawan ‘ya’yan da mutum ya samu. A al’adar Hausawa duk irin arziki ko sarauta ko muƙamin da Allah Ya ba mutum, matuƙar ba shi da ‘ya’ya ko bai taɓa haihuwa ba banza ne. Wannan dalili ne yakan tilasta wa ire-iren mutanen da ba su taɓa haihuwa ba yin ƙoƙarin da duk za su iya don su sami haihuwa domin samun magada.

Kowace al’umma tana da ire-iren hanyoyin da take bi don tanadin ciki tun daga shigarsa har zuwa lokacin da za a haife shi. Wannan ne ya sa ake samun bambance-bambance a tsakanin al’ummomi daban-daban dangane da yadda kowace take tafiyar da hanyoyinta da al’adunta wajen tanadin ciki. A sakamakon cuɗanya da halin zamantakewa a tsakanin al’ummomi akan sami nason al’adu ta kowace hanya. A saboda haka a wannan takarda za a kawo ingantattun bayanai akan hanyoyin gargajiya da al’ummar Hausawa suke bi don tanadin ciki tun daga shigarsa har zuwa haihuwarsa. Daga nan kuma aka kawo bayanai akan ire-iren hanyoyin kiwon lafiya na zamani waɗanda ake bi don tanadin ciki da yadda ake yin su da wuraren da ake yin su. Sannan an kawo bayani kan irin tasirin da hanyoyin tanadin ciki na zamani suka yi a kan na gargajiya ga al’ummar Hausawa.

Idan muka juya kan su wane ne Hausawa, za a ga cewa masana da manazarta daban-dabam sun kawo ra’ayoyinsu kan waɗanda suke ganin cewa su ne Hausawa. A ra’ayin wani masani ya bayyana cewa Hausawa su ne mutanen da ke zaune a ƙasar Hausa tun tuni, kuma suna magana da harshen Hausa a matsayin harshen uwa ( Ibrahim, 1982:1)

Wani masanin kuma na ganin cewa, Hausawa sun haɗa da mutanen nan waɗanda saboda ƙaura da magabatansu suka yi daga ƙasar Hausa zuwa wasu sassa da ke maƙwabtaka ta kusa ko ta nesa da ƙasar Hausa, ko da kuwa ba sa magana da harshen Hausa ko yin al’adun Hausawa sun ɗauka su Hausawa ne. Misali, Abakwariga waɗanda a yanzu suke zaune a Jihar Taraba ta Nijeriya da kuma wasu da ke ikirarin cewa su Hausawa ne waɗanda ke zaune a ƙasashen Cote de Ɓoire da Burkina Faso da Mali (Adamu, 1983:3).

Akwai kuma waɗanda saboda da ƙaura da magabatansu suka yi zuwa ƙasar Hausa sun manta da harshensu da adabinsu da al’adunsu na asali sun ɗauki na Hausawa. A taƙaice sun koma Hausawa a harshe da adabi da al’ada. Misalin ire-iren waɗannan mutane sun haɗa da Barebari da Kanbarin Barebari da Barebarin Katsina da Buzaye da wasu Fulani (Sallau, 2000:71).

Wani masanin kuma ya bayyana cewa Hausawa dai su ne mutane waɗanda harshensu shi ne Hausa sannan dukkan al’adunsu da ta’addunsu na Hausa. Haka kuma addinin Musulunci ya yi cikakken tasiri a kansu (Magaji, 1986:3).

 

2. 0 Shigar Ciki

Idan aka sadu a tsakanin namiji da mace kuma ciki ya shiga, ana gane haka bayan ‘yan kwanaki ta hanyar wasu alamomi da za a gani a wurin wannan mata. Waɗannan alamomi ne suke bayyana cewa wannan mata ta sami ƙaruwa ko juna-biyu ko ɓatan-wata ko ta sami shigar ciki. Ire-iren waɗannan alamomi ana iya gane su a gargajiyance ko a kimiyance watau ta hanyar nazarin Kimiyya ko amfani da na’urori na zamani. Dangane da wannan nazari an duba alamomin shigar ciki a al’adar Hausawa watau kafin zuwan Turawa da kuma yadda ake gane ta a kimiyance bayan zuwan Turawa ƙasar Hausa.

 

2. 1. 1 Alamomin Shigar Ciki a Al’adar Hausawa

A al’adar Hausawa akwai alamomi da dama waɗanda suke bayyana cewa mace ta sami shigar ciki. A mafi yawancin lokaci tsofaffin mata ne suka fi sanin waɗannan alamomi. Wannan kuwa ya faru ne a saboda sun taɓa shiga cikin irin wannan hali a lokuta daban-daban da kuma hulɗatayya a tsakaninsu. A al’adar Hausawa an fahimci cewa, sheƙi a fuska da yawan zubar da yawu da yawan barci da ƙyamar wani nau’i na abinci da yawan amai da dai sauransu suna daga cikin alamomin da ke bayyana mace ta sami shigar ciki. Alamar fitowar waɗannan alamomi ya danganta ga yanayin kowace mace. Alamar da za ta fara bayyana a wurin wata mace ba irin ta ce za a gani a wurin wata ba. Bayan waɗannan na zahiri akwai camfin Hausawa wanda ke nuna cewa yin mafarki da maciji na daga cikin alamomin da suke bayyana mace ta sami shigar ciki (Mairukubta, 1999:13).

 

a)      Sheƙin Fuska

Idan wasu mata suka sami shigar ciki za a ga fuskarsu na yin sheƙi su ƙara kyau kuma za a ga goshinsu na wani irin sheƙi da haske. Ga wasu matan ana ganin irin wannan alama tun ciki na a makon farko da shiga, wasu kuwa sai bayan wata ɗaya ko fiye da haka ne irin wannan alama take bayyana a wurinsu (Ibrahim, 1982:129-130).

b)     Yawan Zubar da Yawu

Wata alama wadda Hausawa suka ɗauka matuƙar an ga mace na yin ta akwai yiwuwar ta sami shigar ciki, ita ce yawan zubar da yawu. A mafi yawancin lokaci za a tarar irin wannan yawan zubar da yawu ya saɓa al’ada. An fahimci yawan zubar da yawu da mace mai ciki kan yi, ba tana yi ne a son ranta ba. Wannan kuwa ya faru ne saboda yawun da yake taruwa a cikin bakinta ba ta jin daɗinsa bare ta haɗiye shi, kuma za ta ji zuciyarta na tashi kamar yawun ba daga bakinta suke ba dole sai ta zubar da su. Har ma idan ta yi ƙoƙarin tilasta wa kanta haɗiye shi, sai ya yi mata sanadiyyar yin amai. Lokaci bayan lokaci irin wannan yawu kan riƙa taruwa a cikin bakin wannan mata tana zubar da shi. Ta irin wannan hanya ce idan aka ga mace na yin haka, sai a yi tsamnanin ta sami shigar ciki.

 

c)      Ƙyama ko Sha’awar Wani Nau’in Abinci

A lokacin da wasu mata suka sami shigar ciki za a tarar suna ƙyamar wani nau’in abinci kuma suna sha’awar wani abinci. Misali, idan a yau suka ce ga irin abincin da suke so, gobe sai su ce ba sa sha’awarsa ga kuma irin wanda suke bukata. Wasu matan kan fara fuskantar wannan matsala da zarar sun sami shigar ciki, kuma ba za su rabu da ita ba sai sun haihu. Ga wasu matan kuwa a lokacin da cikinsu ya fara girma ya kai wata huɗu ko biyar, sai su rabu da wannan matsala. Ba kowace macen da ta sami ciki ce take fuskantar wannan matsala ba. Ga waɗanda suke da ita sukan nuna ba sa ko son jin ƙamshin abincin da ba sa so, idan kuwa har suka ji ƙamshin irin wannan abinci a wani lokaci yakan sanya su yin amai. Akwai nau’o’in abinci iri daban-daban waɗanda a lokacin da wasu mata suka sami shigar ciki suka fi ƙyama, ire-iren su sun haɗa da miyar kuɓewa da ta karkashi da sauransu. A mafi yawancin lokaci sun fi son miyar taushe da kayan lambu.

 

d)     Yawan Barci

Yawan barci na daga cikin alamomin da suke nuna mace ta sami shigar ciki. A mafi yawancin lokaci za a tarar da ire-iren waɗannan mata da sun sami shigar ciki za su yi ta yawan yin barci kuma mai nauyi. Idan wani dalili ya sa suka tashi, da sun gama abin da ya sa suka tashi daga barcin, sai su koma su ci gaba da yin barcinsu. Wannan matsala ta yawan yin barci ba sai da dare kawai ba, don kuwa ko da rana za a riƙa tarar da ire-iren su na yawan yin barci. Mafi yawancin mata masu irin wannan lalura ba sa rabuwa da ita sai bayan sun haihu.

 

e)      Yawan Kasala da Raggwanci

Akwai kuma wasu matan idan suka sami shigar ciki sai su zama raggwaye waɗanda ba sa iya hasala kome. A mafi yawancin lokaci za a tarar ko sharar ɗakunansu ko yin wanke-wanken kayan abinci da sutura ba sa iya yi. Wannan kuwa ya faru ne saboda halinsu ko yanayin da suka shiga kan sanya musu kasala da lalaci da raggwanci. Irin wannan matsala kan kama mace a watan farko da ta sami shigar ciki kuma takan ci gaba har sai ta haihu. Amma akwai wasu mata waɗanda a lokacin da cikinsu ya kai kimanin wata huɗu zuwa biyar, sai wannan matsala ta rabu da su yadda za su ci gaba da gudanar da al’amuransu na yau da kullum a cikin walwala.

Bayan waɗannan alamomi waɗanda aka yi bayani a kansu a sama, fitattar lokacin yin al’adar mace ya yi ba ta ga jinin al’ada ba babbar alama ce wadda take bayyana mata ta sami shigar ciki ko wata ya ɓace mata. Tun daga lokacin da ta fara ganin wannan alama ce za ta fara lissafin watan da cikin ya shiga, kuma daga wannan lokaci ne ake fara lissafin watan da ake tsammanin wannan mata za ta haihu. Wannan alama an yarda da ita a matsayin manuniyar shigar ciki a al’adance da kuma a kimiyance.

 

2. 1. 2 Alamomin Shigar Ciki a Kimiyance

Akwai hanyoyi da dama waɗanda ake bi a kimiyance don gane alamomin shigar ciki ga mata waɗanda suka haɗa da awon fitsari da yin Sikanin da Kwamfyuta da kuma awon jini. Dangane da wannan nazari an duba hanyoyi biyu waɗanda ake gane mace ta sami shigar ciki a kimiyance. Waɗannan hanyoyi su ne, ta hanyar awon fitsarin mace da kuma ta hanyar Sikanin watau hanyar ɗaukar hoto da Kwamfyuta.

 

(i)                Hanyar Awon Fitsari

Idan mace na zargin tana da ciki ko kuma ta san tana da ƙaramin ciki amma a dalilin wata rashin lafiya, sai jini ya sake fito mata ko kuwa ta ga ta ɗauki tsawon watanni biyu ko fiye da haka ba ta ga jininta na al’ada ba kuma ba ta ji wata alama wadda ke nuna mata cewa tana da ciki ba, sai ta je asibiti don a bincika a gano halin da take ciki1. Hanya ta farko wadda ake bi don a gane cewa tana da ciki ko ba ta da shi ita ce ta awon fitsari. Ana yin awon fitsari a Sashen Gwaje-Gwajen Kimiyya a dukkan manyan Asibitoci na Gwamnati da ma na masu zaman kansu. A nan ne za a ba ta kwalba wadda za ta zubo fitsarinta wanda ta yi na farko da safe a ranar da za ta koma Asibiti. Ana amfani da hanyoyi iri daban-daban wajen yin awon fitsari don gane alamomin shigar ciki. Dangane da wannan nazari za a duba hanyoyi iri biyu.

Hanya ta farko ita ce wadda ake amfani da wata ‘yar igiya ta leda. Da Turanci ana kiran wannan hanya da sunan “strip-method” . Ita wannan igiya tana da ‘yan layuka waɗanda da su ne ake amfani a matsayin mizanin da yake nuna akwai ciki ko ba ciki ko kuwa awon da aka yi bai yi daidai ba sai an sake. To, a lokacin da wannan mata ta kawo fitsarin, sai a ɗebe shi a zuba cikin wata ƙaramar kwalba ta yin awo. Daga nan sai a ɗauko wannan igiya a saka ta cikin wannan kwalba har zuwa tsawon minti biyu. A lokacin da aka fito da ita za a ga ɗaya daga cikin waɗannan alamomi. Idan aka ga layi ɗaya ya fito a wurinta alama ce wadda ke nuna cewa wannan mata ba ta da ciki. Idan kuma aka aka ga layuka biyu, ita kuma alama ce wadda take nuna wannan mata tana da ciki. Amma idan aka ga babu layi ko ɗaya a wurin wannan igiya alama ce wadda take nuna awon da aka yi bai yi ba sai an sake yi. 2 An fi yin amfani da wannan hanya saboda ta fi sauƙi kuma an fi samun ingantaccen sakamako (American Pregnancy Association, 2006:1 of 3).

Hanya ta biyu wadda ake bi don gane mace na da ciki ko ba ta da shi ta hanyar awon fitsari ita ce, wadda ake amfani da wani baƙin tangaram na Kimiyya wanda ya yi kamanni da tayil na tangaram wanda ake yin daɓen ɗaki da shi a wannan zamani. A irin wannan hanya ana amfani da wasu ruwan sinadarai iri biyu don yin irin wannan awo. Da farko ana amfani da sirinjin allura a tsotso fitsarin a ɗiga shi saman wannan baƙin tangaram. Daga nan sai a ɗauko kwalbar sinadari na farko wanda ruwansa yake fari tas kamar na famfo, sai a ɗiga shi a wurin da aka ɗiga fitsarin. Bayan an ɗiga sinadarin sai a yi ta jujjuya wannan baƙin tangaram har zuwa tsawon mintuna biyu yadda fitsarin da wannan sinadari za su game sosai. Daga nan kuma sai a ɗauko kwalbar ruwan sinadari na biyu wanda ruwansa yake kamanni da ruwan nono a ɗiga shi a wurin da aka ɗiga na farko, shi ma a yi ta jujjuyawa har tsawon mintuna biyu yadda waɗannan sinadarai da fitsarin za su haɗu sosai. Bayan cikar mintuna biyu sai wannan jami’i mai yin awon ya yi nazarin waɗannan abubuwa waɗanda ya haɗa don ya gano sakamakon da ke cikinsu. Idan ya duba ya ga yanayinsu bai sauya ba, watau kamanninsu ya tsaya kamar nono, alama ce wadda take bayyana cewa wannan mata na ɗauke da ciki. Amma idan sakamakon ya nuna yanayin waɗannan abubuwa da aka harhaɗa sun yi burtsatsa kamar an zuba tsaki cikin ruwa, alama ce wadda take nuna wannan mata ba ta ɗauke da ciki. Da Turanci ana kiran wannan irin awo da sunan “Lateɗ-Reagent monoclonal-method”. Wannan hanya ba ta kai ta farkon inganci ba, don kuwa idan matar da ta zo a yi mata awon ciki na ɗauke da wasu cututtuka a cikin mafitsararta, idan aka yi mata awo yana da matuƙar wuya a sami ingantaccen sakamako. Wannan ne ya sa aka fi yin amfani da hanya ta farko (Wikipedia, 2007:1 of 4).

 

(ii)              Hanyar Yin Awon Sikanin da Kwamfyuta

Wata hanya wadda kuma ake amfani da ita wajen yin awo don a gano mace na da ciki ko ba ta da shi ita ce ta yin Sikanin da Kwamfyuta. A irin wannan hanya ana amfani da Kwamfyuta don gano yanayin da jariri yake a cikin mahaifa. Da farko ana amfani da wata na’ura wadda take haɗe da Kwamfyuta a ɗora ta a saman cikin mace mai ciki, wannan na’ura ce za ta ɗauko hoton dukkan abin da yake cikin mahaifar wannan mata ta haska shi a akwatin talabijin ɗin Kwamfyuta. Daga nan ne za a ga hali da yanayin da jaririn da yake cikin mahaifa yake (Woo, 2006:1 of 13).

Akwai dalilai da dama waɗanda kan sa a yi wa mata Sikanin don a gane hali da yanayin da lafiyarsu take ciki. Waɗannan dalilai sun haɗa da:

Don a tabbata mace na da ciki ko ba ta da shi.

Don a duba a gano yanayin da jariri yake kwance a cikin mahaifa.

A ƙa’ida an fi son ya kwanta a tsaye kansa na duban ƙasa. Idan ya kwanta a gicciye ba za a iya haihuwarsa ba kamar yadda aka saba, dole sai an yi wa mai ɗauke da cikin aikin fiɗa sannan a fitar da shi. Don gudun kar a fuskanci irin wannan matsala ne ya sa ake ziyartar Sashen Sikanin da Kwamfyuta a Asibitoci don a riƙa aunawa yadda za a ga yanayin da jariri yake kwance a cikin mahaifiyarsa. A nan idan aka gano akwai wata matsala, sai a tura wannan mai ciki wurin Likitan da ya dace don ya yi abubuwan da suka kamata ya kuma ba ta shawarwari.

Ana kuma yin awon Sikanin da Kwamfyuta don a gano wurin da uwa take a cikin mahaifa. A ƙa’ida an fi son ta zauna a sama ko a gefen dama ko a gefen hagu, amma idan ta zauna a ƙasa za ta haifar da matsaloli a lokaci da aka zo haihuwa. Irin wannan matsala matuƙar ba a warware ta tun da wuri ba, a lokacin da haihuwa ta zo, sai uwa ta fara yin gaba ta toshe ƙofar mahaifa yadda jaririn da ke ciki ba zai sami hanyar fitowa ba. Wannan dalili ne zai tilasta sai an yi wa wannan mata mai ciki aikin fiɗa don a fitar da jaririn da yake cikinta. Amma idan mai ciki na ziyartar wannan Sashe, za a iya gano wannan matsala tun al’amari bai ɓaci ba. Idan aka fahimci tana da irin wannan matsala, sai a tura ta wurin Likitan da ya dace don a warware wannan matsala tun da wuri, a kuma ba ta muhimman shawarwrin da za su ƙara taimaka mata da jaririn da yake cikinta.

Haka kuma ana yin Sikanin da Kwamfyuta don a gano yanayin lafiyar jaririn da yake cikin mahaifa. Ana dubawa don a gano shin yana da cikakkiyar halittar mutum? Idan aka gano halittarsa ba cikakkiya ce ba, misali ba shi da hannu ko ƙafa ko kuwa wani sashe na jikinsa ya sami wata nakasa, wannan zai tilasta a zubar da wannan ciki don maganin kar a haifi mutum mai nakasa da sauran matsaloli (Owen, 2005:1 and 2 of 3).

Wani dalili wanda kan sa a yi Sikanin shi ne, don a gano yanayin lafiyar jaririn da ke cikin mahaifa. Idan yana lafiya lau za a ga zuciyarsa na harbawa, idan kuwa ya mutu za a ga zuciyarsa ba ta harbawa. Wannan ne zai tilasta a fitar da mataccen jariri daga cikin mahaifa don kar ya kai matakin da zai cuta wa wannan mai ciki (Woo, 2008:1).

Wani dalili da kan sa a yi sikanin shi ne, don a gano yawan jariran da ke ciki, shin ɗaya ne ko biyu ko fiye da haka. Ana yin haka ne don a san ire-iren tanade-tanaden da za a yi wa abubuwan da za a haifa.

Ana kuma yin sikanin don a gano abin da ke ciki namiji ne ko kuwa mace ce.

Cututtukan mahaifa na daga cikin dalilan da kan tilasta a yi Sikanin da Kwamfyuta don a gano yanayin da take ciki. A irin wannan awo ne ake gane mahaifa na da ƙari ko wasu cututtuka. Sakamakon da aka samu ta hanyar wannan awo ne zai sa a ba wannan mata irin taimako da shawarwari da magungunan da za su taimaka mata wajen warware irin matsalar rashin lafiyar da aka gano a cikin mahaifarta (Owen, 2005:2 of 3).

Akwai kuma wasu mata waɗanda bayan sun ɗauki ciki, sai wani laluri ya sa suka yi ɓari. A lokacin da suka yi ɓarin, sai aka sami matsala wadda ta haifar da jaririn da ke ciki bai fito duka ba, wannan zai sa matar da ta yi ɓari yin yawan cuce-cuce a cikinta. A lokacin da ta ziyarci Asibiti don a duba lafiyarta, daga cikin hanyoyin da ake bi don a gano dalilin rashin lafiyarta har da yi mata awon Sikanin. Za a yi mata awo don a gano shin a lokacin da ta yi ɓari dukkan sassan jikin jaririn da ke cikinta ya fito ko kuwa an baro wani sashe? Idan aka gano akwai sauran wasu sassa ko wani sashe wanda bai fito ba a lokacin da ta yi ɓari, sai a yi mata wankin mahaifa don a fitar da su.

3. 0 Hanyoyin Tanadin Ciki

Bayan an tabbatar da mace ta sami shigar ciki, abin da za a sanya a gaba shi ne, bin ingantattun hanyoyi don tanadin wannan ciki, a kuma yi renonsa har zuwa lokacin da za a haihu ba tare da fuskanci wasu manyan matsaloli ba. A wannan zamani a ƙasar Hausa akwai hanyoyi biyu waɗanda ake amfani da su don tanadin ciki. Akwai hanyar gargajiya da kuma ta kiwon lafiya na zamani wadda ake yi a Asibitoci. Dangane da wannan nazari ga yadda ake aiwatar da kowace daga cikin waɗannan hanyoyi.

 

3. 1 Hanyoyin Tanadin Ciki na Gargajiya

A al’adar Hausawa ta gargajiya idan mace ta ga tana da ciki, ba ta ƙara ƙetare rafi. Haka kuma ba ta ƙara zuwa ɗibar ruwa da dare, wai don tsoron kar iskoki su musanya mata ɗan da yake cikinta da nasu. A lokacin da ta ga cikin ya kai wata uku ya fara girma ya fito sosai, ba za ta ƙara zuwa kasuwa ba. Dalilin yin haka shi ne, wai don gudun kar ta gamu da mayu su zubar mata da shi. Waɗannan dai duk camfe-camfe ne kawai. A lokacin da cikin ya kai wata huɗu zuwa biyar, sai wannan mai ciki ta fara zuwa daji don saro itatuwan da za ta ajiye su bushe idan ta haihu da su za ta riƙa dafa ruwan da za ta yi wankan jego (Ibrahim, 1982:130).

A lokacin da cikin ya kai wata bakwai, sai wannan mai ciki ta fara shan magunguna. Dalilin shan waɗannan magunguna shi ne, don a yi maganin dukkan wasu cututtuka manya da ƙanana waɗanda ka iya haifar da doguwar naƙuda a lokacin da za a haihu. Akwai bambanci a tsakanin magungunan da ake ba mace mai cikin fari da kuma wadda dama can ta taɓa haihuwa.

Ga bayanin ire-iren magungunan da ake ba mace mai cikin fari don tanadin abin da ke cikinta da kuma kariya gare ta daga cututtuka waɗanda za su iya yi wa lafiyarta barazana. Na farko shi ne, ana tono sauyoyin loda da na badagareji, sai a haɗa su a yi ƙulli-ƙulli uku daban-dabam. Daga nan sai a ɗauki ƙulli ɗaya a jiƙa cikin ruwa. Ruwan wannan magani ne mai cikin za ta riƙa sha tana kama ruwa da shi har zuwa tsawon kwanaki uku. A cikon kwana na uku ko ruwan ya ƙare ko bai ƙare ba sai ta zubar da shi ta sake jiƙa ƙulli na biyu, wanda shi ma za ta riƙa sha tana kama ruwa da shi har zuwa tsawon kwanaki uku. Haka za ta yi da da cikon ƙulli na uku. A taƙaice ana amfani da waɗannan ƙulle-ƙullen sauyoyin magani kowane za a yi kwana uku wanda zai ba da jimlar kwanaki tara.

Amfani da wannan magani zai taimaka wa mace mai cikin fari ta fitsarar da dukkan zaƙin da ke cikin cikinta. Wannan kuwa ya faru ne saboda a al’adar Hausawa an yarda da cewa yawan zaƙi ga mace mai ciki zai sanya a lokacin da ta zo haihuwa ta fuskanci matsalar yin doguwar naƙuda.

Wani magani da ake ba mace mai cikin fari don tanadinsa yadda za a yi renonsa a kuma haife shi lafiya ba tare da fuskantar wasu matsaloli ba shi ne, sai a ɗebo ganyen riɗin barewa a haɗa da tafin hannu ɗaya na wake a dafa don wannan mai ciki ta ci. Za a riƙa yin haka a kullum har zuwa tsawon kwanaki uku a jere. Amfanin wannan magani ga mace mai cikin fari shi ne, ya taimaka wa mai cikin da abin da ke cikinta samun ƙarin lafiya.

Ana kuma yin amfani da sassaƙen iccen aduwa ko na karaki don maganin zaƙi. Ana jiƙa wanda ya samu daga cikin waɗannan da ruwa a riƙa sha.

Idan kuma muka juya a kan mata waɗanda suka taɓa haihuwa, idan suka samu ciki ga ire-iren magungunan da suke amfani da su don tanadin ciki. Ire-iren waɗannan magunguna sun haɗa da wanda ake tono sauyoyin yazawa da sassaƙen maɗaci a haɗa su a jiƙa da ruwa a riƙa sha don maganin zaƙi. Mai ciki za ta fara amfani da wannan magani a lokacin da ciki ya kai wata takwas. Za ta riƙa sha aƙalla sau biyu a cikin mako har zuwa lokacin da za a haihu.

Wani magani da mace mai ciki take sha shi ne, a sassaƙo bayan iccen ɗakwara a jiƙa da ruwa ana sha a kullum har sai an haihu. Shi ma ana amfani da shi don maganin zaƙi.

A lokacin da haihuwa ta zo don maganin doguwar naƙuda ana amfani da ganyen ceɗiya ko na zurman ko na gwandar gida. Ba dukkansu ake haɗawa ba, ana daka wanda aka samu daga cikinsu a jiƙa da ruwa a ba wadda ke yin naƙudar ta sha. Haka kuma ana amfani da ‘ya’yan hakin sansan a jiƙa su da ruwa a ba wadda ke yin naƙuda ta sha. Bayan waɗannan ma ana amfani ɓawon goro a jiƙa da ruwa a ba wadda ke yin naƙuda ta sha. Dukkan waɗannan magunguna da aka yi bayani a kansu, Hausawa na gargajiya sun yarda da cewa idan aka yi amfani da su a lokacin da mace ke durƙushe tana naƙuda da ta sha za ta haihu.

Wani maganin naƙuda wanda Hausawa ke amfani da shi ana fara yin sa ne tun daga lokacin da aka ga ciki ya kai wata bakwai. A wannan lokaci a duk lokacin da take tuƙin tuwo idan ta yi tuƙin fari, sai ta sanya hannunta na dama ta saɓe tuwon da ya liƙe a wurin muciyar da take tuƙin tuwon ta zuba shi cikin ruwan da za ta yi kwashin tuwon. Ana son ta cinye wannan tuwo kafin ta yi tuƙi na biyu. Za ta ci gaba da yin haka a kullum har zuwa lokacin da ta haihu. Yin haka zai ƙara taimaka mata a lokacin da haihuwa ta zo mata ba za ta fuskanci wata matsalar naƙuda ba.

 

3. 2 Hanyoyin Tanadin Ciki na Zamani

Waɗannan hanyoyi sun samu ne a sakamakon shigowar Turawa ƙasar Hausa. Shigowarsu ta kawo sabuwar rayuwa ta fannin kiwon lafiya ciki har da yadda Hausawa da sauran al’ummomin wannan duniya ke tanadin ciki. A waɗannan sababbin hanyoyi ana ba mata masu ciki shawarwari da magungunan Asibiti a Cibiyoyin kiwon lafiya manya da ƙanana a sassa daban-dabam waɗanda ke cikin ƙasar Hausa.

Da farko idan mace ta fahimci ta samu shigar ciki, watau ta ɗauki kimanin tsawon watanni biyu ba ta ga jininta na al’ada ba, yana da muhimmanci a gare ta da ta ziyarci Asibiti a Sashen da ke kula da mata masu ciki don a yi mata gwaje-gwajen da suka dace don a tabbatar da halin da take ciki. Daga nan idan aka tabbatar da ta samu shigar ciki, sai a yi mata rajistar awon ciki wanda ta wannan hanya ce za a riƙa ba ta kula ta musamman. Abin la’akari a nan shi ne, a irin wannan tsari dukkan mace mai ciki idan ta ziyarci ɗaya daga cikin waɗannan cibiyoyi waɗanda ke kula da mata masu ciki ana karɓar ta cikin yanayi na fara’a da annashuwa da kuma fahimtar juna. Ana yin haka ne don a ƙara mata ƙarfin gwiwa ta kuma samu natsuwa cewa wannan wuri ne wanda za a taimaka mata. Bayan an yi mata rajista, sai Malamar Asibiti wadda ke kula da mata masu ciki ta keɓance da ita a cikin Ofishinta don ta yi mata tambayoyi waɗanda suka danganci wannan ciki da take ɗauke da kuma yanayin lafiyar jikinta. Haka kuma tana tambayar ta ko ta taɓa haihuwa?Idan ta taɓa haihuwa, waɗanne ire-iren matsaloli ne ta fuskanta a lokacin da ta yi waccan haihuwar?Haka kuma Malamar Asibitin na tambayar wannan mai ciki ko daga cikin ‘yan uwanta akwai masu ɗauke da cututtuka irinsu hawan-jini ko ciwon sukari da dai sauransu. Ana kuma tambayar ta ko daga cikin zuri’arsu akwai wadda ta taɓa haihuwar tagwaye? Daga ƙarshe sai a tambaye ta ko daga cikin zuri’arsu akwai wadda ta taɓa haihuwar jariri da wata nakasa? A lokacin da wannan mata mai ciki ke bayar da amsa ita kuma Malamar Asibiti sai ta yi ta rubuta amsoshin da ta ba ta a cikin littafin awon ciki wanda aka buɗe wa wannan mai ciki (Sweet, 1988:126-131).

Duk a wannan rana da wannan mai ciki ta fara zuwa awo ana auna tsawonta, dalilin yin haka ya samo asali a sakamakon binciken da aka yi inda aka fahimci cewa dogayen mata sun fi gajerun mata samun sauƙi a lokacin naƙuda. Yin wannan awo zai taimaka a san ire-iren shawarwari da kuma magunguna waɗanda suka dace a ba wannan mai ciki.

Ana kuma auna nauyin wannan mai ciki a wannan rana kuma a duk lokacin da ta zo domin a yi mata awo ana sake auna nauyinta. Dalilin yin haka shi ne, don a gane ƙaruwa ko raguwar nauyinta. Idan nauyinta ya ƙaru sosai ko ya ragu sai a ba ta shawarwari waɗanda za su taimaka mata da kuma jaririn da ke cikinta.

Bayan awon nauyi ana kuma yin awon fitsari don gano yanayinsa da zaurinsa. Ana kuma auna shi don a gano ko wannan mai ciki tana da ciwon sukari ko alamominsa da dai sauran cututtuka waɗanda ake ganewa ta hanyar awon fitsari. Ana yin wannan awo ne don a yi maganin ire-iren waɗannan cututtuka waɗanda ka iya yin aibi ga lafiyar wannan mai ciki da kuma jaririn da ke cikinta.

Daga ƙarshe ana yi wa wannan mai ciki cikakken awo wanda zai bayar da ingantaccen bayanin yanayin lafiyarta. Wannan irin awo cikakken Likita ne kawai ke yin irinsa tare da taimakon Malamar Asibiti wadda ke kula da mata masu ciki. A nan ne Likita zai ummurci wannan mata mai ciki da ta hau wani gado na musamman wanda aka yi don yin awon ciki ta kwanta a rigingine don Likitan ya duba yanayin cikinta da kuma na farjinta. 3 A wurin yin irin wannan awo Likitan na tambayar wannan mai ciki yadda take jin jikinta. A lokacin da take ba shi amsa shi kuma yana kula da yanayin da take ba shi amsar yadda zai ƙara fahimtar yanayin lafiyarta. Sannan kuma zai duba yanayin lafiyar haƙoranta, idan akwai wata matsala sai ya tura ta wurin Likitan haƙora don a yi mata maganin wannan matsala. Yana kuma duba yanayin mamunanta don ya gano ko wani ruwa-ruwa na fitowa daga cikinsu? Ana kuma auna ƙarfin bugawar jini da zuciyar wannan mai ciki don a gano yadda suke bugawa. Ana yin irin wannan awo a duk lokacin da wannan mai ciki ta ziyarci Asibiti don yin awo. Idan a wani lokaci aka gano cewa ƙarfin bugawar jininta ya hau ko ya sauka, to dole sai an ba ta magunguna da shawarwari waɗanda za su taimaka ƙarfin bugawar jininta ya koma daidai. Rashin kula da auna bugawar jini ke haifar da ciwon hawan-jini mai sa jijjiga a lokacin da aka samu doguwar naƙuda. 4

Bayan zuwanta na farko, sai kuma a shawarce ta da ta riƙa zuwa awon ciki kamar yadda aka ƙayyade kowace mace wadda ake yi wa awon ciki ta riƙa zuwa. Ga yadda aka ƙayyade kwanakin zuwa awo ga dukkan mace mai ciki.

Bayan zuwan ta na farko ana son ta riƙa zuwa awo a duk bayan mako huɗu har sai lokacin da ciki ya kai mako na ashirin da takwas da shiga.

Daga nan kuma ta riƙa zuwa a duk bayan mako biyu sai lokacin da ciki ya kai mako na talatin da shida da shiga.

Daga wannan lokaci ta riƙa zuwa awo a duk mako har sai ta haihu. Abin kula a nan shi ne, idan wata matsala ta taso alhali kuwa lokacin zuwa awo bai yi ba, to ya zama dole ga wannan mata ko iyalanta da suka yi gaggawar kai ta Asibiti domin a duba lafiyarta yadda za a cece ta da kuma jaririn da ke cikinta (Sweet, 1988:134).

A duk lokacin da mace mai ciki ta je wurin yin awo ana bincika abubuwan da aka yi bayani a kan su a baya don a tabbatar da lafiyarta da ta jaririn da ke cikinta. Haka kuma ana ba ta shawarwari a kan abubuwan da suka dace ta yi da kuma waɗanda ba su dace ta yi ba.

 

3. 3 Shawarwarin da ake ba Mata Masu Ciki

A duk lokacin da mata masu ciki suka ziyarci Asibiti domin yin awo, ana ba su wasu muhimman shawarwari a kan abubuwan da suka dace su yi da waɗanda ba su dace mace mai ciki ta riƙa yin su ba. Daga cikin ire-iren waɗannan shawarwari akwai:-

 

a)      Cin Abinci Mai Gina Jiki

Dukkan mace mai ciki tana da buƙatar ta riƙa cin abinci mai gina jiki don ya ƙara mata lafiya da jaririn da ke cikinta. Ire-iren wannan abinci sun haɗa da nama da ƙwai da madara da kifi da wake. Haka kuma mace mai ciki tana da buƙatar nau’o’in abinci masu sanya ƙarfin jiki kamar abinci mai sukari-sukari irinsu fulawa da burodi da fanke da biskit da tumatir da dai sauran ire-irensu. Amma kuma abin la’akari a nan shi ne. bai kamata su riƙa cin irin nau’o’in wannan abinci da yawa ba, su dai riƙa ci kadaran-kadahan. Dalili kuwa shi ne, yawan cin ire-iren nau’o’in wannan abinci zai sa su ƙara wa mace mai ciki nauyi fiye da kima. A dalilin haka mace mai ciki na iya kamuwa da ciwon hawan-jini.

Haka kuma mace mai ciki tana da buƙatar ta riƙa cin ganyaye irinsu zogale da rama da yakuwa da soɓorodo da latas da kabeji da dai sauran ire-irensu. Tana kuma buƙatar ƙoda da hanta waɗanda za su riƙa taimaka wa jikinta kuma su zama riga-kafi gare ta da jaririn da ke cikinta daga kamuwa da sanyin jiki (Werner, 1977:250).

 

b)     Samun Wadataccen Hutu

Yana da matuƙar muhimmanci ga mace mai ciki da ta riƙa samun wadataccen hutu. Ana buƙatar da dare ta riƙa samun barci na kimanin awa takwas zuwa tara. Haka kuma da rana ta samu hutun awo biyu ko a bisa gado ko kuma a saman kujera mai abin jingina yadda za ta ajiye ƙafafunta a ƙasa.

 

c)      Ayyukan Motsa Jiki

Ana buƙatar mace mai ciki ta riƙa yin ayyuka don motsa jikinta, amma ba ayyuka waɗanda ke buƙatar a sa ƙarfi sosai ba. Ayyuka irinsu wanke-wanken kayan abinci da ‘yan suturunta waɗanda ba masu yawa ba da yin shara cikin gida da dai sauran ‘yan ƙananan ayyuka duk za su riƙa taimaka wa jikinta ya ƙara ƙarfi.

 

d)     Zaɓen Sutura

A lokacin da ciki ya kai wata ɗaya da shiga, nonnan mace mai ciki za su ƙara girma, sannu a hankali sai dukkan sassan jikinta ma su ci gaba da ƙara girma. A saboda haka yana da matuƙar muhimmanci ga wannan mai ciki ta riƙa sanya wadatattun kaya waɗanda ba za su matse jikinta ba, kuma su kasance marasa nauyi. Haka kuma bai kamata mace mai ciki ta riƙa sanya takalma masu tantaɗo ba don kauce wa haɗarin faɗuwa wadda tana iya yi wa jaririn da ke cikinta wani mummunan rauni da aibi. Haka kuma idan tana tafiya da ire-iren waɗannan takalma ƙugunta na iya samun wani lahani wanda daga ƙarshe idan ta zo haihuwa tana iya fuskantar munanan matsaloli waɗanda za su tilasta sai an yi mata aikin fiɗa a fitar da jaririn da ke cikinta.

 

e) Kula da Tsabtar Jikinta da Wurin Zamanta

Tsabta aba ce wadda ke da matuƙar muhimmanci ga mace mai ciki da ma sauran al’umma. A saboda haka yana da matuƙar muhimmanci ga mace mai ciki da ta riƙa yin wanka a kullum kuma ta kula da wanke suturunta ta kuma tsabtace wurin zaman ta hanyar share ɗakinta da filin da ke cikin gidan da take zaune. A taƙaice ta kawar da duk wani datti da shara waɗanda ke cikin ɗakinta da cikin gidan da take zaune. Yin wanka a kullum zai ƙara sanyaya jikinta yadda za ta ƙara samun ƙarfi, kuma za ta samu sauƙin kasala da mutuwar jiki waɗanda aka san mata masu ciki na fuskantar matsalarsu.

f)      Kula da Haƙora

 A lokacin da ciki yake ƙarami yana da kyau ga mace mai ciki da ta riƙa ziyartar Likitan haƙora don a bincika a ba ta magunguna da shawarwarin da suka dace. Haka kuma a gida ta riƙa kula da tsabtace su a kullum. Yin haka zai ƙara taimaka wa lafiyarta da ta jaririn da ke cikinta.

 

g)     Shan Taba

Bai kamata mace mai ciki ta riƙa shan taba ba don kuwa shan taba na da aibi gare ta da kuma jaririn da ke cikinta. An fahimci cewa mace mai ciki wadda ke shan taba tana cuta wa jaririn da ke cikinta. A binciken da aka gudanar an gano cewa a dalilin shan taba ga mata masu ciki, jariran da ke cikinsu za su samu ƙarancin iskan da za su riƙa shaƙa da kuma rashin samun wadataccen abinci. Wannan zai sanya jariran su samu matsalar da za ta hana su saurin girma. Su kuma matan masu ciki idan suna da alamomin ciwon hawan-jini shan taba zai ƙara assasa wannan ciwo a wurinsu. Wannan zai sanya a lokacin da suka zo haihuwa su fuskanci matsalar hawan-jini mai sa jijjiga (Sweet, 1988:150).

 

h)     Shan Giya

A binciken da aka gudanar an gano cewa shan giya ga mace mai ciki yana da matuƙar aibi ga lafiyarta da ta jaririn da ke cikinta. Da farko dai an gano cewa shan giya na taimakawa wajen zubar da ciki. Haka kuma jaririn da ke ciki yana iya samun nakasa a wani ɓangare na jikinsa ko a ƙwaƙwalwarsa wanda a lokacin da aka haifi yaro yana iya girma da matsalar wawanci da sauran ire-iren waɗannan matsaloli waɗanda kan shafi ƙwalwa. Don a yi maganin ire-iren waɗannan matsaloli ne ya sanya ake ba mata masu ciki shawarar su daina shan giya a lokacin da suke ɗauke da ciki (Sweet, 1988:150).

 

i)       Tsagaita Tafiye-Tafiye

Mata waɗanda a da can sun taɓa yin ɓari ko kuwa idan sun zo haihuwa sukan fuskanci matsalar doguwar naƙuda, to a lokacin da suka samu wani ciki kuma cikin ya kai tsawon makonni talatin da biyu da shiga, bai kamata su yawaita yin tafiya zuwa unguwa nesa ba. Yin ire-iren waɗannan tafiye-tafiye na da babbar matsala a wurin jikinta da kuma jaririn da ke cikinta. Don kuwa za ta riƙa samun matsalar gajiya da mutuwar jiki. A dalilin haka a lokacin da ta zo haihuwa tana iya fuskantar matsalar doguwar naƙuda wadda idan ba a yi sa’a ba, dole sai Likita ya taimaka mata kafin ta haihu.

 

4. 1 Tasirin Hanyoyin Tanadin Ciki na Zamani a Kan na Gargajiya

 A wannan lokaci hanyoyin kiwon lafiya na zamani dangane da yadda ake tanadin ciki a ƙasar Hausa sun yi babban tasiri a kan yadda Hausawa ke gudanar da nasu na gargajiya. Dalili kuwa a nan shi ne, a yanzu mafi yawancin matan Hausawa musamman waɗanda ke zaune a garuruwa da birane har ma da wasu daga ƙauyuka na ziyartar Manyan Asibitoci da Cibiyoyin Kiwon Lafiya waɗanda ke a garuruwa da ƙauyuka don yin awon ciki. A waɗannan wurare ana ba su magunguna kyauta kuma ana ba su muhimman shawarwari waɗanda za su taimaka wa lafiyarsu da ta jariran da ke cikinsu. Wannan dalili ne ya sa a yanzu mafi yawancin matan Hausawa sun yi watsi da hanyoyin tanadin ciki na gargajiya sun ɗauki na zamani. Amma kuma duk da haka ana samun wasu mata musamman waɗanda ke ƙauyuka da ma wasu a cikin garuruwa da birane waɗanda har yanzu ba su daina yin amfani da hanyoyin tanadin ciki na gargajiya ba.

 

5. 0 Kammalawa

Tanadin ciki wani al’amari wanda ba Hausawa ne kaɗai suka ba shi muhimmanci ba, a iya cewa dukkan al’ummomin wannan duniya sun ba shi kulawa ta sosai. Kamar yadda aka gani a bayanan da suka gabata, an yi bayani ne a kan hanyoyin tanadin ciki a ƙasar Hausa. An kawo bayani kan ma’anar ciki da alamomin shigar ciki da yadda Hausawa suke tanadinsa a gargajiyance da kuma irin tasirin da hanyoyin tanadin ciki na zamani suka yi a kan na gargajiya.

Dangane da hanyoyin tanadin ciki a ƙasar Hausa a wannan lokaci a iya cewa waɗannan hanyoyi biyu da aka yi bayani a kan su, watau na gargajiya da na zamani, kowace daga cikinsu na taka irin tata rawar ga wani rukuni na mutane a ƙasar Hausa. Misali, mutanen karkara sun fi yarda da bin hanyoyin tanadin ciki na gargajiya, kuma kasancewar babu wadatattun Cibiyoyin Kiwon Lafiya na zamani a ƙauyuka ya ƙara taimaka wa mutanen karkara su fi raja’a kan wannan hanya ta gargajiya. Su kuma mazauna garuruwa da birane waɗanda ke da wadatattun Asibitoci da Cibiyoyin Kiwon Lafiya na zamani sun fi bin hanyar tanadin ciki na zamani. Amma a wasu lokuta akwai waɗanda ke amfani da dukkan waɗannan hanyoyin tanadin ciki duk dai don neman a samu nasarar haihuwar abin da ke ciki ba tare da an fuskanci wata matsala ba.

Ƙarin Bayani

1.      Abin da ke kawo wannan matsala shi ne, idan mace na ɗauke da cututtukan da suka kama mafitsara, a wasu lokuta tana iya ɗaukar tsawon wata ɗaya zuwa uku ba ta ga al’adarta ba alhali kuwa ba ta da ciki. Ana gane haka ta hanyar yi mata awon fitsari don a gano irin cutar da ke cikin jikinta.

2.      Ita wannan igiya ta roba “strip” wadda ake amfani da ita don yin awon fitsari don gano idan mace na da ciki ko ba ta da shi, ana amfani da igiya ɗaya ba a raba ta, kuma ba a haɗa biyu a lokacin da za a yi awo. Matuƙar ana son a samu ingantaccen sakamako dole a yi amfani da igiya ɗaya cikakka.

3.      Irin wannan awo ne ke sanyawa matan karkara da waɗanda ke da kunya a lokacin da suka fara zuwa Asibiti don yin awon ciki, idan aka yi masu irinsa daga nan ba sa sake komawa. Wasu ma idan aka buƙace su da su kwanta don a yi masu irin wannan awo, nan take za su ƙi yarda kuma daga wannan rana ba sa sake dawowa Asibitin don yin awon ciki. Dalilinsu a nan shi ne, ba su yarda su bayyanar da tsiraicinsu ga wani mutum ba musamman ma namiji. Wannan yana daga cikin dalilan da kan sa matan karkara a ƙasar Hausa ƙin zuwa Asibiti don yin awon ciki. Amma duk da haka Malaman Asibiti mata na ta yin ƙoƙarin jawo hankalin ire-iren waɗannan mata ta hanyar nuna masu muhimmancin yin awon ciki ga mace mai ciki don su amince su riƙa zuwa Asibiti don a yi masu awon ciki a lokacin da suka samu ciki.

4.      Ciwon hawan-jini mai sa jijjiga yana kama mata masu ciki kafin su haihu ko bayan sun haihu. Idan wannan ciwo ya kama mace za ta fita daga cikin hankalinta ta kuma yi ta yin kakari ta riƙa fitar da yawu a baki da kuma majina ta hanci kamar za ta mutu. Idan kafin ta haihu wannan ciwo ya kama ta ba za ta iya haihuwar jaririn da ke cikinta ba. Wannan kuwa ya faru ne a saboda ba ta da cikakken ƙarfin da za ta yi yunƙurin da za ta haifi jaririn. A al’adar Hausawa an ɗauka cewa aljannu ne suka kama wannan mai ciki, dole sai a nema mata magungunan aljannu don su rabu da ita. A irin haka ne mafi yawanci ire-iren waɗannan mata waɗanda suka fuskanci irin wannan matsala ke mutuwa, ko kuma idan Allah Ya sa suna da rabon sake shan ruwa idan sun haihu hankalinsu kan rabu da su. Amma idan aka kai su Asibiti idan ba su haihu ba za a sanya masu ƙarin ruwa a fitar da jaririn a kuma yi masu allurar barci don su samu wadataccen hutu. A lokacin da suke yin barci ba a son a tayar da su ko kuma a yi wani motsi mai ƙarfi wanda ka iya tayar da su daga barcin. Wannan dalili ne ya sa a Asibitoci ba a barin mutane masu yawa su riƙa ziyartar ire-iren waɗannan mata waɗanda suka fuskanci matsalar hawan-jini mai sa jijjiga.

 

Manazarta

Adamu, M. (1978), The Hausa Factor in West African History, Zaria/Ibadan, Ahmadu Bello University Press/Oɗford University Press of Nigeria.

Alhassan, H. da Wasu; (1982). Zaman Hausawa. Zariya: Longman.

American Pregnancy Association, Pregnancy Tests: www. americanpregnancy. org/gettingpregnant/understandpregnancytests. html-18k-

Ibrahim, M. S. (1982):”Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Hausawa ta Gargajiya”. Kundin Digiri Na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Magaji, A. (1986) ”Gudummuwa a Kan Ƙoƙarin da Ake yi Na Samar da Cikakken Tarihin Hausawa da Harshensu”. Takardar da Aka Gabatar a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Mairukubta, H. (1999):”Jego da Reno a Ƙasar Hausa, Tsokaci Kan Hausawan Kabi”. Kundin Digiri na Biyu. Sakkwato: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usman Ɗanfodiyo.

Owen, P. (2005): Ultrasound Scans during Pregnancy: www. netdoctor. co. uk/health-advice/examinations/ultrasoundpregnancy. htm-64k-

Sallau, B. A. S. (2000): “Wanzanci: Matsayinsa na Al’ada da Sana’a a Ƙasar Hausa”, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

Sweet, B. R; (1988): Mayes’ Midwifery, A Teɗtbook for Midwiɓes, Eleɓenth Edition, London: Bailliere Tindall.

Werner, D; (1977): Where There is no Doctor. London: Macmillan.

Wikipedia, (2007): Pregnancy Test, the free encyclopedia: http://en. wiki/pregnancy-test.

Woo, J. S. K. (2006): “What Are Obstetric Ultrasound Scans?-A Comprehensiɓe Guide to Ultrasound Scans in Pregnancy”: www. ob-ultrasound. net/51k-

Woo, J. S. K. (2008): “Abnormality Screening, Obstetric Ultrasonography”, Wikipedia Free Encyclopedia, Wikipedia Foundation: en. wikipedia. org/wiki/obstetric-ultrasonography-33k-

Post a Comment

0 Comments