𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Cikina watansa
biyar said dai har ruwan nono ya
Fara zuba, shin masalace?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Zubar ruwan nono irin wannan kan iya zamowa normal
physiologic response, duk da leaking ɗin ruwan nono irin wannan anfi ganinsa ko
tsammaninsa a watanni 2 na karshen ciki (wata 8 zuwa 9).
A likitance ma munsan a wata 4 na ciki nono ka iya
fara zuba...
Don haka ana iya gani a wata na 5 wato watanni ukun tsakiya (2nd trimester) duk
da ba kasafai ake ganin hakan ba.
Akwai ruwan nonon da ake kira colostrum wanda ke
ba jariri kariya da kara karfafa garkuwar jikinsa. Zai iya kasancewa mace taga
kalar nonon fari ƙar ko kuma ruwan dorawa-dorawa wato yellow.
Don haka inde nonon da ake gani ba kalar jini-jini
bane, nonuwan ba kuma wani kullutu aciki dake sa suna yin matsanancin ciwo, ko
kuwa ganin alamun fatar nonon tai ja ko kan nonon ya tsage ko ya karkace kurum
de zuba yake toh bawani abun damuwa.
Amma insuna ciwo ko ganin ruwan dake fita alamun
jini jini, ko fari kamar ruwa hade da dan jini toh wannan ne abun damuwa sai
anje anga likita tukun.
Amma kamar yadda nace in kurum ruwan nonon ne ke
zubowa wani lokaci musamman yayin jima'i ko sanda take cikin motsawar sha'awa,
ko in an taɓa
matashi, ko in ana zaune kasan fanka tana kaɗawa hakan babu wani matsala. Kai koda haka
kurum nema in anyi aiki angaji.
Sannan bama a mai ciki ba, hatta a mai shayarwa
musamman wacce ta yaye yaro amma nonon yaki tsayawa yake mata nono toh dukkan
ku Inhar zubar sosai nonon yake, yana kuma ɓata muku kaya, gami da saku kuna karni, za
ku iya amfani da ganyen kabeji
Ku sami kabeji ko ganyensa inda hali asa a freedge
yadda zai dau sanyi. Ko cikin randa inkuma duk ba hali sai ai amfani dashi a
yadda ya samu amma de a wankesa tukun.
Daga nan sai mace ta yagi daidai girman wanda zai
rufe kan nonon gaba ɗaya
sai adau rigar nonon a tare shi da ita, abarsa har zuwa wasu mintuna 40, ko awa
1 koma awa 2 ya zamto de sai kinji ya jike da zufa toh sai acire. Kya iya canza
wani a lokacin ko ki bari sai an jima ki kara sa wani. Kar kuma adinga takure
bra ɗin,
abarta saisa-saisa yadda ba za ta dameki ba.
Adinga yin haka sau 3 yini, safe, rana, yammah
aita yi kurum har zuwa lokaci ko kwanakin da ya tsaya ya dena zubar. Wasu ma
galibi aranar farko suke ganin ya tsaya.
Sannan lokaci lokaci in mai ciki ce ke ki rika cin
ayaba duk sanda aka sami dama koda kwaya 1 ce amma ba dole.
Babu bukatar magani ko tada hankali ba matsala bane.
Allah ta'ala yasa mudace.🤲
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/K7RkƘRMf2b57l3UENoJ1Or
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.