Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Limancin Mace A Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin a shari'ance ko ya halatta ga Mace tayi limanci a Sallar Jam'i??

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Dangane da bayani a kan wannan Mas'ala ta hukunci agame da limancin Mace, dukkan Malamai Ahlul-Ilmi sunyi Ittifāki a kan cewa bai halatta ba Mace ta yi wa Maza limancin Sallah, kokuma ta yi wa Maza da Mata ahaɗe, wannan kam babu wani Saɓani a kansa, shin a Sallar Farillane ko a ta Nafila duk bai halattaba, to Sai dai Malamai sunyi Saɓanine a game da hukuncin limancin Mace idan yakasance 'Yan uwanta Matane kaɗai za ta yiwa limancin, ansamu magangan Malamai kamar guda uku a kan haka,

1. Ƙauli nafarko shi ne wanda Mazhabin Mālikiyya suka tafi a kansa cewa, baya halatta ga Mace ta yi wa Maza kokuma ta yi wa 'yan uwanta Mata limancin Sallah, daga cikin Dalilansu sun kafa Hujja da Faɗin Mαnzon Aʟʟαн() da ya ce:

"لن يفلح قوم ولوا أمرهم إمرأة" (رواه البخاري)

MA'ANA:

Al'umma ba za su taɓa rabautaba matukar sun shugabantar da Mace a kan al'amuransu:

2. Ƙauli nabiyu shi ne wanda Mazhabin Shāfi'iyya da Hanābila da kuma mafi yawa daga cikin Malamai sukatafi a kansa cewa, Mustahabbi ne Mace ta yi wa 'Yan uwanta Mata limanci a Sallar farilla ko ta nafila, daga cikin Dalilansu sun kafa Hujja da wannan Hadisi na Ummu-Waraƙat,

"أن النبي() كان يزورها في بيتها وجعل لها مؤذنا يؤذن لها، وامرها أن تؤم أهل دارها"

MA'ANA:

Haƙiƙa Mαnzon Aʟʟαн() Ya kasance yana ziyartarta (Ummu-Waraƙat) a gidanta, kuma ya sanya mata wanda zai riƙa yimata Ƙiran Sallah sannan ya umarceta da tariƙa yiwa mutanen (matan) dake gidanta limanci:

3. -Ƙauli na uku shi ne wanda Mazhabin Hanafiyya da kuma wani sashe na Hanābila sukatafi a kansa cewa, Makaruhine Mace ta yi wa Yan'uwanta Mata limanci a Sallah, amma suka ce idan anyi to Sallar ta inganta,

To Sai dai magana mafi inganci daga cikin maganganun da Malamai suka yi ita ce, ya halatta Mace ta yi wa 'Yan'uwanta Mata limancin Sallah, Sai dai ba za ta wuce gabansu ba kamar yadda Maza suke yi idan za su yi jam'in Sallah, kawai za su jerune su yi sahu itakuma liman ɗin sai ta tsaya a tsakiyarsu, kamar yadda aka samu wani (asar/أثر) da yake cewa:

"أمت عائشة نساء في الفريضة في المغرب وقامت وسطهن وجهرت بالقراءة"

MA'ANA:

A'isha Aʟʟαн() Yaƙaramata yarda ta yi wa wasu Mata limanci a Sallar farilla ta Magriba, kuma ta tsayane tsakiyarsu (matan) sannan kuma tayi karatun Sallar abayyane (gwargwadon yadda matan za suji)

Danhaka kenan idan ankalli Hujjojin kowanne ɓangare, to ko shakka babu cewa Malaman dasuka tafi a kan cewa ya halatta Mace ta yi wa 'Yan uwanta Mata limancin Sallah Alalhaƙiƙa Dalilansu sunfi Ƙarfi.

шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ

           Mυѕтαρнα Uѕмαи

              08032531505

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments