Ticker

6/recent/ticker-posts

Shekara 1 Da Aure Ban Taɓa Jin Daɗin Jima'i Ba Sabida Istimna'i

𝐓𝐀𝐌BAYA

Assalamu alaikum malam Barka da rana ya ayyuka muna Godiya da tunatarwa da kuma magunguna. Allah ya kare ya albarkaci zuri'a. Malam ni likita ce so wata yarinya tazo min da rashin lafiyarta tace shekararta ɗaya da rabi da aure amma bata haihu tace a shekarun nan tunda take bata taɓa jin daɗin jima'i ba, bata taɓa yin releasing ba se tayi Istimna'i sannan take gamsuwa se na tambayeta nace tana yin istimna’i ne tun kafin tayi auren se tace eh gaskia ta saba dayi to malam ni a ganina ba wata matsala ba ce ba virginal infection ba ne dan har na turata tayi test na tricomoniasis dan shima yana sa haka amma sai naga ba shi ba ne illah wannan istimna’in da takeyi ne shi ne yasa bata jin daɗin sex kuma shi ne zai sa ciki ya kasa zaunawa a jikinta na zaunar da ita na yi mata bayani sosai shi ne take tambayata magungunan da za ta sha ta samu sauki tace abin yana damunta sosai yana sakata ciwon mara, shi ne nake ganin maganin islamic se ya fi warkar da ita sannan kuma maganin ku yana da inganci shi ne nace malam wane magani ne za ku bata daga gareku nagode sosae Allah ya saka da alkhaeri🙏🏻

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Améééen y rabb!! Ok, Allah sarki! Nagode da addu'arki gareni Dr. Allah yayi jagora ya sa  mudace.

Gaskiya Daman Duk Wanda yariga ya Fara ISTIMNA'I zai wahala yasami gamsuwar aure ko mace ko namiji domin shi ne ya san inane yake taɓawa a jikinsa ya samu gamsuwa shi ya sa zai wuya Ace ta gamsu sai dai ta nunawa mijinta irin yanda takeyi ta gamsu shi kuma sai yayi amfani da wannan damar yadinga gamsar da ita, to sirin shi ne daga sanda yafara gamsar da ita toh tunaninta zai canja , Kuma ta koma fidirarta da Allah ya halicce ta a kanta domin yin ISTIMNA'I jan dabi'a ne a kan yadda Allah ya tsaraka , toh wanann ita ce shawara ta farko da Zaki Bata sannan magani Kuma ya biyo baya na matsaltsalolin da ya haifar Mata.

Mastsla ta biyu Kuma Dole ta yaƙi da tunaninta a kan cewa mijinta zai gamsar da ita a lokacin da suka Fara jim'i, kinsan rashin sa Rai da cewa mijinta zai gamsar da ita toh shima ciwone da zai hanata gamsuwa.

Amma matsalar Rashin haihuwa tabbas bazai wuce Infection ba ne ya hanata haihuwa, Dole zatai treating ɗin Infection da magani masu ƙarfin kashe ƙoyoyin cuta na gargajiya.

Sanann ga wani taimakon magani ta Fara kafin ta shirya yin maganin ta nemi...

1. Garin habbatussauda

2. Garin haltit

3. Garin Kusdul hindi

4. Garin Albabunaj

5. Garin Tafarnuwa.

6. Zuma

7.yansun

8.Kirfat

Da farko Zaki haɗa Waɗannan kowanne kamar chokali 2 sai ki haɗe su waje ɗaya ki samu Zuma kamar kofi biyu ki zuba garin duka a ciki ki haɗa ki gauraye su ki cakuɗa sosai sai a Dora Kan garwashi ya dahu zuwa minti 20 ya zama zumar sa garin sun zama ɗaya adinga Shan cokali 1 sau 2 a rana.

Allah ta'ala yasa mudace.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇��𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments