Ticker

6/recent/ticker-posts

Za Mu Iya Fasa Aure, Saboda Gudun Haihuwar Sikila?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, inada saurayin wanda bincike ya nuna mutumin kirki ne, ana yi mishi zaton kyawawan dabiu. To za a fara maganar aure sai muka yi genotype test akace duk mu biyun AS ne saboda haka a cikin yaya huɗu zamu iya samun sickler ɗaya. Shine nake tamabaya a addinance ya halatta mucigaba da batun auren ko haƙuri shine yafi? Tunda musan za a iya samun matsala. Na gode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus Salam. A fahimtata dakatawa daga auran shi ne maslaha, saboda yana daga cikin manufofin sharia tunkude cuta gwargwadon iko, yawanci idan aka haifi sikila yana cutuwa da yawa, kuma ya wahalar da iyayansa, tunkude abu kafin ta faru, ya fi sauki fiye da tunkude shi bayan ya auku, kamar yadda ya tabbata a wajan malaman fiƙhu. Allah ya halicci maza da yawa, za ki iya auran wanda ba za ku shiga damuwa ba cıkın ‘ya’yan da za ku haifa, kauda da kunci da takura ƙa’ida ce daga cıkın ƙa’idojin da aka yi ijma’i akan su.

Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Zarewa

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments