Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Rama Sallah Ga Wanda Sumewa Ta Same Shi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Asssalamu alaikum, Malam tambayata ita ce, mutum ne yake fama da cuta irin ta jinnu, yakan fadi ya fita hankalinsa, idan kuma ya tsaya zai yi sallah sai ya ga wuta a gabansa ya gagara sallah. Shin zai rama abin da ya wuce masa na sallah ne idan ya dawo hankalinsa!?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu, za a lissafa wannan matsala ce daga cikin matsalar wanda sumewa ko ɗan gushewar hankali na qanqanin lokaci ta same shi, wanda malaman Fiqhu suke ce masa: "Almugmá alaihi" (المغمى عليه), a game da rama sallolin da suka kuɓucewa mai wannan lallurar, malamai sun yi maganganu guda uku kamar haka:

1. Zai rama dukkan sallolin da suka kuɓuce masa yayin da ya farfaɗo cikin hayyacinsa. Masu wannan fahimta suna hukunta shi ne da hukuncin mai barcin da har lokaci ya wuce bai yi sallah ba. Masu wannan fahimta su ne Hanabila.

2. Ba zai rama sallar da ta kuɓuce masa ba, sai in ya kasance ya dawo hayyacinsa a cikin wani yanki na lokacin sallar, dalilin masu wannan fahimtar ita ce: Nana A'isha Allah ya qara mata yarda ta tambayi Manzon Allah game da mutumin da ya sume bai farfaɗo ya sami yin sallah ba, sai Manzon Allah ya ce mata: "Babu rama sallah ga wannan, sai dai in da ya sume ya farfaɗo a lokacin (sallar), to ya sallace ta". Masu wannan fahimtar sun haɗa da Imamu Malik da Imamus Shafi'i.

3. Zai rama ne idan sallolin da suka kuɓuce masa ba su wuce guda biyar ba, amma in sun wuce biyar, to ba zai rama su ba dukkansu, saboda yawan maimaici ya shigo ciki, don haka sai hukuncin ramuwa ya faɗi, ya zama kamar hukuncin mahaukaci. Daga cikin masu wannan fahimta akwai Abu Haneefa.

To ƴar uwa duk da kasancewar kowane ɓangare daga cikin waɗannan ɓangarori suna da dalilai da suka dogara da su, waɗanda ba zai yiwu a iya kawo su a nan ba, to kawai bisa shawara wanda ya sami kansa a halin sumewa ya rama sallolin da ake binsa idan ba su yi yawan da rama su za su gagara ba, kamar kwana ɗaya ko biyu ko uku da makamancin haka.

Domin neman qarin bayani sai a duba ALMUGNIY (1/290). Da ALMUHALLÁ BIL'ÁTHÁR (2/8, 9).

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments