Ticker

6/recent/ticker-posts

Wa ya Rubuta Ƙawa'idi? Takaitaccen Bayani

Daya daga cikin litattafan da ya shahara a kasar Hausa  ake taƙaddama akan wa ya rubuta shi, shine littafin ƙawa'idus sallati. Wasu malaman na ganin Ruƙayya Fallatiya ce ta rubuta shi (a jira rubuta na na gaba: Takaitaccen tarihin Ruƙayya Fallatiya). Wasu kuma na ganin Nana Asmau ce ta rubuta shi. (Zan kawo taƙaitaccen tarihinta nan gaba).

Ala aiyi halin dai an rubuta littafin ne, saboda yara da kuma sabbin shiga musulunci ko kuma manya yan ajin yaki da jahilci. Irin wadannan rubutu sunyi shuhura a tsakanin malaman kasar Hausa. Misali, Wali Danmarina: Muhammad al Sabbagh ya rubuta mazjaratul fityan domin ya zaburar da samari akan neman ilmi. Shitu dan AbdurRauf ya rubuta Jiddil Ajizi balarabiya da Baajamiya, Inda tun a farkon wakar ya bayyana cewa, yayi rubutun ne, saboda mata da yara kanana. Ya kira wakar tasa da: Nagozo, domin ya sadaukar da ita ga Sarkin Katsina Gozo, saboda irin gudunmowar da Gozo ya bayar wurin raya addini a kasar Katsina, Wanda hakan ya jawo bayinsa suka yi masa juyin mulki, karkashin jagorancin Kauran Katsina Kuren Gumari.

Kamar Bakandamiya da aka fi Sani da: Gangar Waazu, shima littafin Ƙawa'idi babu sunan Wanda ya rubuta shi, hakan ne ya jawo taƙaddama, a tsakanin masana, akan ko wa ya rubuta littafin. An dai yi ittafaƙi mace ta rubuta shi, saboda yadda akayi amfani da kalmar mace a "wa man lam ya arifuha" hakan ya saka wasu ke tunanin walau dai Nana Asmau ce ta rubuta dan dalibanta Yantaru, ko kuma Ruƙayya Fallatiya ce ta rubuta wacce ta rubuta shaharariyar wakar nan: Ummul Yatim wadda aka fi Sani da : Alkarimun yaƙubal.

Kusan marubuta mata sun fi maifa himma wurin imantar da yara da mata, musamman irinsu Maimunatu bint Ƙadhi Bazarin ta Jibiya. Ko da yake akwai mata da suka fi maida himma ga ilmin manya irinsu: Gwaggwo Zaituna ta Adamawa.

Masu bayani sunyi nuni da cewa: "Ƙalal Shehu al faƙihu al Imamu" da akayi amfani da shi a littafin na nufin Shehu Usman Danfodio. Domin shine Shehu kuma shugaba. Dan haka Nana Asmau ce ta rubuta shi , domin koyar da dalibanta yadda ake sallah.

Sai dai daga daya bangaren, sunyi nuni da cewa: ai babban dalibin Muhammad Fodiyo; Muhammad al Kashnawi, ya kira shi da Sheikh imam! Dan haka matar sa Ruƙayya ita ta cancamci a bata muƙamin wadda ta rubuta littafin.

Koma wa ya rubuta Allah ya bata ladan aikinta

Wa ya Rubuta Ƙawa'idi? Takaitaccen Bayani

Post a Comment

0 Comments