Ticker

6/recent/ticker-posts

Ilmi (Education) Ta Aliyu Idris

Ai dole ne mui nazari,

A batun ilimi ya zarta.

 

Ga karatu yai tsada,

Ilmi fa sai mai gata.

 

Cikin shekara su dad'a,

Muna ƙangin bauta.

 

Dama muna ji kullum,

Kakanu sun mana bita,

 

Suna fad'in wata rana,

'Dan talaka zai nisanta.

 

Ilmi fa zai yo wahala,

Wahala ta sa su gujeta.

 

Ga shi 'ya'yan talaka,

Wasu duk sun gigita.

 

Da akwai marasa kishi,

Ilmin ƙasar suka 6ata.

 

Yau Najeriya ba daraja,

Ku tsaya kui fuskanta.

 

'Ya'yan su na can turai,

Na mu sun bambamta.

 

Kun ga kenan ba adalci,

Tun da sun mana rata.

 

Haka shi ne manufar ku?

Rayuwarmu kun cuceta.

 

Hakkinmu ne kuka tauye,

'Yanci mu kun yi farauta.

 

Yanzu ba nation builders,

Ga leaders suna ƙaisata.

 

(C)Aliyu Idris
(Sarkin Yaƙin Malumma)
21/07/2023


Post a Comment

0 Comments