Ticker

6/recent/ticker-posts

Rufe Boda

Masara tabbas a da can,

Sai ɗaiɗaikunmu ke ci,

Da yawa a cikin birane,

Tumaki ko awakai,

Su ke ci su yi ɓulɓul.

 

Dawa ƙaura a da can,

Ake bai wa dawakai,

Rufe bodar ƙasarmu,

Yasa yau sun fi ƙarfin,

Talakawa don masifa.

 

Shinkafa da kuɗinta,

Kan Mai Malafa ya sauka,

Dubu shida ko bakwai ce,

Rufe bodar Buhari,,

Ta fi karfin mai sukuni.

 

Shi ko talakan ƙasa yau,

A maƙota kan ji ƙamshi,

A gidajen masu farce,

Na susa don takaici,

Allah ka jiƙan ƙasata.

 

Tilas ne yau abinci,

Yai ta tsada ga bayani,

A idonmu ake ficewa,

Da girbaben abinci,

Ƙasashen ƙetare can.

 

Masara wake na suya,

Alkama doya da rogo,

Na ƙasarmu ake fitarwa,

Ƙasashe masu nisa,

A can wai ya fi riba.

 

Na kasa rabe mafarki,

Na makaho ni da kaina,

Sun bar boda a buɗe,

Ana safarar abinci,

Da za mu saya da sauƙi.

 

Sun hana mu sayo abinci,

Mu namu suna sayarwa,

Tilas ne yau farashi,

Taki har ma abinci,

Ya tsefe ƙafarsa sosai.

 

Ɗauki ya Rabbi ba mu,

Sauƙi duka na wajenka,

Tausaya mana Jalla Sarki,

Abinci Ka ba mu kullum,

Ko ba sa so da sauƙi.


Malam Khalid Imam
08027796140
khalidimam2002@gmail.com

Post a Comment

0 Comments