Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ya Hallata Na Sadu Da Matata Tana Da Juna Biyu?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam idan mace tanada juna biyu tsawon wata 6 ya halasta Mijinta yayi kwanciyar sunnah da ita kuma wace illa ce jinjirin zai samu?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

ﻭﻋﻠﻴﻜﻢ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻭﺭﺣﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ .

ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ ،

Ya halasta Miji ya sadu da matarsa mai ɗauke da juna biyu a duk lokacin da yake so, koda cikin ya wuce watanni 7, sai fa idan yin hakan yana cutar da matar, haramun ne Miji yayi kowane irin abu da zai cutar da Matar sa. Idan yin saduwar bazai cutar da matar ba, amma akwai wahala agareta, toh yafi dacewa Mijin ya hakura kar ya sadu da ita, domin kauracewa aikata duk abin da zai wahalar da ita, wani nau'i ne na zamantakewa da ita cikin aminci da kyautatawa. Allah (S.W.T) yana cewa

..... ۚ وَعَاشِرُوهُنَّ بِالْمَعْرُوفِ ۚ ....

......Kuma kuyi zamantakewa da su da alkhairi.......

(Suratun-Nur aya 91)

Sannan babu wata illa da saduwa da mace mai juna biyu yake haifarwa jinjirin dake a ciki.

Amma haramun ne Miji ya sadu da matarsa a lokacin da dayan su (Miji ko Mata) yake cikin ihraam na aikin hajji ko Umrah, ko kuma dayan su yana azumi da rana, amma zasu iya saduwa da dadaddare bayan sun buda baki.

Haka kuma haramun ne saduwa da mace idan tana cikin jinin Nifaas.

Haka kuma haramun ne Miji ya sadu da matarsa a lokacin da take cikin haila har sai ta samu tsarki tayi wanka.

Idan tana haila Mijinta zai iya jindadi da ita amma ba ta farjinta ko duburar ta ba. Saboda Manzon Allah (Sallallahu alaihi wa sallam) yace;

لقول النبي صلى الله عليه وسلم: اصنعوا كل شيء إلا النكاح.

رواه مسلم (الحيض /455)

Ku aikata komai, amma banda shiga (saduwa ta farjinta).

(Muslim, Al-hayd, 455)

فتوى الشيخ ابن عثيمين . فتاوى العلماء في عشرة النساء ص/ 55.

(Fataawa Shaykh Ibn Uthaymeen, Fataawa Al-ulama' fii Ashratin Nisaa', shafi na 55).

 والله أعلم،

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/DIcJIQrWyLP0oBOMSnDi5P

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments