𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin Ya Halatta Musulmi Ya Yi Musafaha Da Kafiri?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله العلي الكبير.
Dalilai Ingantattu sun tabbatar da hani dangane da
fara yiwa kafiri sallama, bayahudene ko kirista, Kamar yanda Muslim yaruwaito a
cikin Sahihin littafinsa (2167) Daka Abu huraira Allah yakara masa yarda Manzan
Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: ( Kada kufara yiwa bayahude ko kirista
sallama) .
Haka dalilai Ingantattu sun nuna za a Amsawa
kafiri Sallama idan yayiwa Musulmi sallama.
Bukhari yaruwaito hadisi (6257) da Muslim (2164)
daka Abdullahi Bin Umar Allah yakara masa yarda Manzan Allah Sallallahu Alaihi
waslam ya ce: ( Idan bayahude ya yi muku sallama, yana cewa( Assalamu Alaikum,
kace dashi: wa'alaika).
Haka wajan yin musafaha kada kafara baiwa kafiri
hannunka dan kuyi musafaha, Idan yamiko maka hannu dankuyi musafaha saika mika
masa.
Ibnul Ƙayyeem ya ce: Idan wannan sababin yakau,
kirista ya ce: Maka Assalamu Alaikum Adalci shi ne kamayar masa irin Abun da ya
yi maka Sallama dashi.
" Ahkamu Ahlul Zimmah".
"Sama" Abun da take nufi shi ne mutuwa.
Da Sallama da Musafaha ba'aso Musulmi yafara yiwa
kafiri, Amma idan kafiri yayima yanada cikin Kyautatawa kamiƙa masa
hannu kugaisa, kakuma Amsa Masa Sallama.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.